✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dabarun Kasuwanci: Ko ka na biyan kanka kuwa? (2)

Na yi alkawari a makon da ya gabata cewa zan yi karin bayani akan yadda dan kasuwa zai rika biyan kansa albashi daga harkarsa, a…

Mista Olusegun Aganga, Ministan kula da harkokin kasuwanciNa yi alkawari a makon da ya gabata cewa zan yi karin bayani akan yadda dan kasuwa zai rika biyan kansa albashi daga harkarsa, a wannan makon, sannan kuma in ci gaba da amfani na biyu gare shi wajen yin hakan, wato yadda zai kaucewa cinye jarinsa a cikin rashin sani. Idan mai karatu na biye da ni zai tuna cewa na fara wannan makala ce a makon da ya gabata, inda na sanar da cewa tattauna dabarun kasuwanci daban-daban da za su taimaka wa dan kasuwa, musamman ma karamin dan kasuwa da matsakaici a wajen tafiyar da harkokinsa yadda ya kamata. Saboda yawan wadannan dabaru na kasuwanci, zan dauki tsawon wasu makonni masu zuwa ina tattauna su daya bayan daya.
A makon da ya gabata na fara da Dabarar Kasuwanci ta dan kasuwa ya rika biya kansa albashi yayin da ya ke tafiyar da harkarsa ta kasuwanci. Na fadakar da basirar yin hakan da cewa dan kasuwa ya biya kansa albashi daga harkar da ya ke yi na daya daga cikin jiga-jigan alkaluman lissafin da za su iya fahimtar da shi ko ya na cin riba a harkar da ya ke yi, ko kuma akasin haka, wato ya na faduwa. Na misalta wannan dabara da yadda dan kasuwa zai kiyasta wahalhalun da shi kansa ya ke yi wa wannan harka tasa da kudi nawa zai biya idan ma’aikaci zai dauka ya rika yi masa wannan dawainiya, ko kuma nawa zai iya karba a matsayin albashi ya yi wa wani wannan hidimar a matsayin ma’aikaci? Saboda haka na shawarci dan kasuwa ya cire wannan kiyasi daga cikin kudin da ya samu daga harkarsa yayin da ya ke lissafin ribarsa, domin gano hakikanin ribar da ya ci a wannan lokaci.
  Basira ta biyu ta dan kasuwa ya biya kansa ita ce ta kawar da shi daga shiga cikin jarinsa yayin da ya ke tsunduma hannunsa cikin alaben harkarsa, domin biyan bukatarsa ta yau da kullum. Mu kaddara cewa, Mallam Audu Mai kayan miya da na yi misali da shi a makon day a gabata ya tsayarwa da kansa albashin Naira dubu daya a wata. To yana iya cewa zai rika daukar Naira 250 a kowanne mako, inda mako hudu zai kasance Naira dubu kenan. A wannan tsarin, ko da bukatar kudi ta taso masa domin tafiyar da wani lamari nasa dab a na kasuwanci ba, dan kasuwa na iya daukar aron kudi daga cinikinsa, da zummar rance ya yi daga cikin albashinsa da zai dauka gaba. Kuma idan lokacin daukar alnashin nasa ya yi zai mayar da kwatankwacin abinda ya dauka rance daga kudin kasuwancinsa.
dan kasuwa zai samu alfanun dake tattare da wannan basira kawai idan ya daure ya tsaya akan iya yawan kudin da ya kiyasta su ne albashinsa. Anan ina nufin kada ya wuce wannan kiyasi, kuma ko da wata lalura ta sa ya yi hakan, to ya hakikance cewa ya rubuta kuma ya tsara yadda zai mayar da wannan kudi da ranta domin cike gibin da bari. Babbar shawara anan ita ce, dan kasuwa ya daure ya tsaya akan adadin kudin da ya yankawa kansa a matsayin albashi, ba tare da zarta hakan ba. Wannan zai hana shi shiga cikin jarinsa, wanda hakan ke haifar da karayar jai ga akasarin kanana da matsakaitan yan kasuwa. Kada kuma dan kasuwa ya manta da cewa wannan albashi day a yankawa kansa ba shi kadai ba ne kudi da zai anfana daga harkarsa ba. Akwai riba da zai ware yayin da ya zo lissafinsa na kudi na karshen shekara, ko na bayan kowane wata shida, ko kowanne watanni uku-uku inda wannan tsari ya danganta da yadda dan kasuwa ya zabarwa kansa.
Zan duba Dabarar Kasuwanci akan kasafin riba idan Allah Ya kaimu mako na gaba.