✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dabarun Kasuwanci: Ko ka na biyan kanka kuwa?

Zan fara makala akan Dabarun Kasuwanci a wannan makon, kuma zan kwana biyu ina yi, wato kwana biyu irin na Bahaushe, idan Allah Ya so.…

Hada-hadar kasuwanci a kasuwar MaiduguriZan fara makala akan Dabarun Kasuwanci a wannan makon, kuma zan kwana biyu ina yi, wato kwana biyu irin na Bahaushe, idan Allah Ya so. dan kasuwa zai lura cewa mafi yawancin wadannan dabaru na kasuwanci (ko da yawa daga ciki) da zan yi bayani akan su, ba baki ba ne a wannan fili, watakila ma ya taba karanta su a filin, sai dai a wannan karon zan mayar da hankali ne wajen jawabi akan su, mai makon fadin su kawai a wasu makalun da na yi a baya. To Bahaushe ya yi gaskiya a karin maganar da ya ke cewa ‘Dabara daukar daki’, domin ita dabara ba wata aba ba ce bakuwa, illa abin da mai basira ya gani da za a iya sarrafawa a samu wata biyan bukata in an jarraba yin hakan. Wannan shi ne abin da yara ke cewa ‘Ga abu akan matar sarki, da tana da ido ido da ta gani…’ Su kuwa manya sukan ce ‘da magani a gonar yaro, sai ya nome bai sani ba.’
To, Dabarar Kasuwanci da zan fara da ita a wannan makon ita ce dan kasuwa ya biya kansa albashi yayin da yake tafiyar da harkarsa ta kasuwanci. Wasu za su ji wannan magana banbarakwai, wai ‘namiji da suna Hajara’, kamar yadda wata karin maganar Hausa ke cewa. Na kan ji ‘yan kasuwa na cewa su ba ‘yan albashi ba ne, ko kuma ka ji wasu ma na yi wa juna shegantaka, su na cewa, “haba wane, yaya kake al’amura kamar dan albashi?”  
Biyan kanka albashi daga harkar da kake yi na daya daga cikin jiga-jigan alkaluman lissafin da za su iya fahimtar da dan kasuwa ko ya na cin riba a harkar da yake yi, ko kuma akasin haka, wato faduwa ya ke. dan kasuwa zai yi anfani da wannan basira kamar haka: Misali, ni Malam Abdu mai sayar da kayan miya a Kasuwar Barci Kaduna, a kullum ina tashi daga gidana a unguwar Malali da karfe bakwai na safe in je  Kasuwar Rigasa in sawo kayan miya in kawo Kasuwar Barci in kasa. Zan wanke, in tsince marasa kyau daga ciki, in kuma gyara wadannan kayan miyan kafin in kasa in sayar. Kuma na kan kai karfe biyar na yamma ina tafiyar da wannan harka tawa a kasuwa a kullum kafin in tafi gida. To abin yi anan sai ni, Malam Abdu, in yi nazarin cewa idan zan dauki wani mutum ya yi min wannan dawainiya, nawa zan biya shi albashi, a mako ko a wata. To mu kaddara zan ba shi Naira dubu biyar a kowanne mako, wato Naira dubu 20 ke nan a wata. To wannan shi ne albashin da zan biya kaina daga cikin wannan harka tawa.
Kamar yadda na rika jaddadawa a makalun baya, lissafin jari akai-akai domin gano ko ana cin riba ko ba a ci na cikin sirrin dorewar harkar kasuwanci. Saboda haka idan Malam Abdu na lissafin jarinsa wata-wata, ko wata uku-uku ko kuma wata shida-shida, ko ma shekara, to ya zama dole ya shigar da wannan albashi nasa cikin wahalhalun da yake yi wa harkar tasa domin gano ribarsa. To idan yana lissafinsa kowanne wata ne, misali sai ya ga ya ci ribar Naira dubu 40 a watan Yunin bana, ba tare da ya cire albashinsa na dubu 20 ba, to ribarsa ta zahiri ita ce Naira dubu 20; in kuwa ribar kasa da dubu 20 ya samu kafin ya debe albashinsa, to faduwa ya samu ke nan ba riba. Zan yi karin bayani akan wannan da kuma yadda wannan dabara za ta hana dan kasuwa cinye jarinsa a makala ta gaba idan Allah Ya kai mu mako mai zuwa.