✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dabbobi fiye da dubu 14 suka samu allurar rigakafi a Yobe

Fiye da dabbobi dubu 14 ne aka yi wa allurar rigakafin kamuwa da mabambantan cututtukan dabbobi a karamar Hukumar Yunusari da ke cinin Jihar Yobe,…

Fiye da dabbobi dubu 14 ne aka yi wa allurar rigakafin kamuwa da mabambantan cututtukan dabbobi a karamar Hukumar Yunusari da ke cinin Jihar Yobe, sanadiyar barkewar wata annobar gudawa ga dabbobin.
Bayanin hakan dai ya fito ne daga bakin Daraktan Gudanar da Mulki na karamar Hukumar Yunusari, Alhaji Tonga Bularafafa a tattaunawarsa da Aminiya dangane da annobar gudawa da ta kunno kai a karamar hukumar, kwanakin baya.
Annobar, wadda ta haifar da kamuuwar dabbobi masu yawan gaske, Daraktan ya kara da cewar, dabbobin da aka yi wa wannan allurer rigakafin sun hada da shanu kimanin 3950, sai awaki da tumaki kimanin dubu 10, hade da karnuka 100; wadanda duka an yi masu wannan allura ta rigakafi.
Ya ci gaba da cewa, dangane da jin barkewar annobar, karamar hukumar ba ta yi kasa a gwiwa ba, nan da nan sai ta sanar da ma’aikatar kula da lamuran dabbobi a jihar tare da cefano wadansu magungunan rigakafi don taka wa annobar birki.
Ya bayyana cewa, garuruwa da kauyukan da aka gudanar da wannan allura ta rigakafi ga dabbobin sun hada da Yunusari, Kanamma, Fulatari, Kafiya, Garin Gawo, Dalari, Mirari da sauransu. Don haka ne ya kirayi jama’ar yankunan da ke fama da wannan annoba ta cututtukan dabbobi, da su rika kai rahoton duk wasu alamomin jinya da suka gano daga jikin dabbobinsu cikin hanzari, tun kafin lamarin ya munana; don a samu a shawo kanta cikin lokaci.