Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Dabi Alonso ya zama kocin matasa a Real Sociedad

Tsohon dan kwallon kulob din Liberpool da ke Ingila da Real Madrid da ke Sifen da kuma Bayern Munich da ke Jamus Dabi Alonso ya zama kocin matasa a kulob din Real Sociedad da ke Sifen.

Alonso wanda ya taba buga kwallo har na tsawon shekara 12 a Real Sociedad kafin ya canja sheka zuwa Liberpool ya zama kocin matasan ne (Team B) a wata sanarwa da mahukunta kulob din suka fitar a shekaranjiya Laraba.

ADVERTISEMENT

Alonso ya shiga sahun tsofaffin ’yan kwallon kafa da suka zama koci bayan sun yi ritaya. Kadan daga ciki sun hada da Ole Gunnar Solkjaer kocin Man United da Frank Lampard na Chelsea da Zinedine Zidane na Real Madrid da Thierry Henry na Arsenal da sauransu.

A wata hira da ya yi da manema labarai jim kadan bayan ya zama kocin Alonso ya ce “Ina matukar godiya ga Allah da Ya nuna mini wannan rana.  Duk da ban taba rike wata kungiya a baya ba, amma yadda na shafe shekara 20 ina buga kwallo a kulob da dama hakan zai ba ni damar rike kulob din matasa na Real Sociedad ba tare da matsala ba.”

ADVERTISEMENT

“Na yi wasa a karkashin masu horarwa da dama, kuma hakan zai ba ni damar jan ragamar wannan kulob ba tare da matsala ba.