Da Dumi Dumi

Dabid Moyes zai taka rawar-gani, In ji Shugaban masoya Manchester United

Shugaban kungiyar masoya kulob din kwallon kafa ta Mancheter United na kasa, Alhaji Shehu Usman ya yi hasashen cewa sabon mai horar da ’yan wasan kulab din  Dabid Moyes zai yi amfani da kwarewar da yake da ita don  kai kulob din tudun-mun-tsira a kakar wasanni mai zuwa.
Alhaji Shehu Usman wanda ya yi furucin yayin da yake tattaunawa da Aminiya a makon da ya gabata ya ce Moyes ba kanwar lasa ba ne a fagen horar da ’yan wasa.
Ya ce, ‘Ina mai tabbatar wa da jama’a cewa sabon mai horar da ’yan wasanmu Dabid Moyes kwararre ne ba zaben tumun dare muka yi ba. Kowa ya san kulob din da Dabid Moyes ya bari na Eberton ya taka rawar gani.’
  Kodayake ritayar da Ferguson ya yi ta girgiza mu domin mun san mun yi asarar babban kwararren mai horar da ’yan wasa wanda babu kamar sa a duniya amma muna so masu hamayya da mu su sani cewa hasashen da suke yi cewa karshen Manchester ya zo ba haka ba ne domin ba su yi hasashen da kyau ba.
Ya ci gaba da cewa, ‘Ya kamata mutane su sani cewa yawanci duk nasarar da ake samu ba daga mai horar da ’yan wasa ba ne, daga ’yan wasan ne domin su ne suke buga wasa. Ina mai tabbatar maka da cewa har yanzu Aled Faguson yana tare da mu’.