✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Daga Borno Zuwa Yobe, Zuwa…. (2)

A makon da ya wuce mun fara yin wadansu tambayoyi ne da muke fatar su ba mu haske dangane da abubuwan da ke faruwa dangane…

A makon da ya wuce mun fara yin wadansu tambayoyi ne da muke fatar su ba mu haske dangane da abubuwan da ke faruwa dangane da wadannan matsaloli na kashe-da kashe da rasa dukiyoyin jama’a. An ce an baza jami’an tsaro a jihohi uku da wannan matsala ta yi kaka- gida, ga shi kuma an aza dokar ta-baci na kusan wata shida, ba kuma inda za ka leka ba ka ga jami’an tsaro na wulgaya ba, amma kuma ba sauki a cikin lamarin. Shin ina amfanin wadannan jami’an tsaro a wannan sashi idan har kowace rana ta Allah za a wayi gari ana rasa rayukan bayin Allah da ba su ji ba, ba su gani ba? Yau an kashe bayin Allah a cikin gidajensu, an jima an kashe dalibai a cikin makarantunsu na kwana, gobe ka ji an fatattaka kauye ko gari guda, an iza dubban jama’a gudun hijira, wai kuma a ce muna da gwamnati a Tarayya ko jiha ko karamar hukuma!
Shin ko dai duk abin dodorido ne ake yi wa jama’a? Ina gaskiyar lamarin da ke nuni da cewa jami’an tsaro ba komai suke ba sai zama ’yan kallo a lokacin da ake karkashe mutane, ba su ji ba su gani ba. Wannan na iya zama gaskiya idan rahotannin da ke bullowa daga kafafen watsa labarai abin amincewa ne da ake cewa ’yan ta’adda na cin karensu ba babbaka a duk lokacin da suka kai hari a wani kauye ko gari. Wata sa’a sai su kwashe awa takwas zuwa 10 suna yin abin da suka ga dama a inda suka kai hari, su kuma kwashe inasu-inasu su koma inda suka fito ba mai ganewa ko sanin inda suka nufa. Ta yaya mutane ba za su yarda cewa cikin wannan rawanin akwai lauje ba ganin cewa ’yan ta’addar nan cikin jerin gwanon motocin Hilud suke zuwa, wato mota 15 zuwa 20. Amma kuma su bace bat, ba alama ko wani bayani daga wata hukuma ko jami’an tsaro!
Batun da Shugaban kasa Jonathan ya yi da ke nuna cewa an samu nasara wajen yaki da ta’addanci tunda an samu an kori ’yan ta’adda daga biranen Abuja da Kaduna da Kano da wasu sassa, yanzu sun koma can gefe a Borno da Yobe da Adamawa maganar ’yan sanda ce, domin kuwa wannan ba alamun nasara ba ne, sai ma kara ba ’yan ta’addar dama su kara ci gaba da ta’addancinsu. Hanyar da kurum za a iya tabbatar wa al’umma cewa da gaske ake ita ce a gano masu yin wannan makarkashiya duk inda suke, a kuma tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma a duk inda suke ba wai wani bangare na kasar nan ba! Duk rai; na yaro ko babba, mace ko namiji, na kauye ko na birni yana bukatar kariya da tsaro, ba wai kurum wadanda ke cikin aljannar duniya ba.
Abin da ke da karin tada hankali da ban tsoro bai wuce yadda yawancin al’ummar da ya kamata su sa baki cikin wannan ta’asa ba, suke mui da baki kamar rayukan da ake rasawa a kullum rana ta-Allah ba rayukan mutane ba ne na dabbobi ne. Mu dau karamin misali, a cikin watanni uku kurum an rasa daruruwan rayukan al’umma kusan 300 a yankin da wannan hayaniya ke ta’azzara, kuma abin kullum sai kara girma da daukaka yake yi, ba alamun sauki ko mafita. Halin ko in kula da muke yi, musamman gwamnatocinmu alamu ne da ke ba ’yan ta’addar damar ci gaba da barnar da suke yi, kuma idan ba a kawo hankali kusa ba, abubuwa na iya rincabewa, musamman ganin yadda matsalar ke neman zama ta kasashe a halin yanzu.
Mun fadi haka ne ganin yadda alamu ke nuni da cewa kasashe biyu da ke makwabtaka da Najeriya sun fara shigowa dumu-dumu cikin matsalar Najeriya, wato kasashen Kamaru da Nijar. Idan kuma aka yarda wannan matsala ta manaye wannan yanki ba tare da an yi maganinta ba, to alamun zababbakar ta’addanci a wannan yanki ba abin da za a iya karyatawa ba ne, musamman idan aka yi la’akari da ire-iren waki’ar da ke gudana a kasashen Mali da wasu kasashe da ke rakube da su. Ke nan idan aka bari sakaci ya shiga cikin wannan harka, abin da ya samu matsuguni a Borno, ya shiga zuwa Yobe da Adamawa zai iya zama matsalar Yammacin Afirka ne baki daya.
Saboda haka muke ganin ya dace a mike tsaye don kawo karshen wannan tabargaza tun kafin ta ga karshen al’umma, ba kuma wadanda suka dace su samar da mafita kamar:
•Gwamnatin Tarayya
•Gwamnatocin jihohin da wannan matsala ta fi yin sankara.
•kungiyoyin addini
•Jam’iyyun siyasa
•kungiyoyin matasa da sauransu.
Lokaci ya yi da za mu tashi domin kashe wannan macijin, a kuma tabbata an sare kan sosai don kada ya dawo ya ci gaba da barna. Mu sani cewa ita tashin-tashina farkonta ne kurum za a iya karanta, amma karshenta ba mai iya cewa ga rana ko wata. Haka kuma mu fahimci cewa don muna nesa da inda aukuwar take, wato mu ba mu rasa rayuka da dukiyoyi ba, shi ke nan shakulatin-bangaro…. ba garanti ba ne na cewa mun hau tudun mun-tsira. Har mun manta lokacin da wannan matsalar ta addabi kasa baki daya; ba Musulmi ba Kirista ba, ba dan Arewa ba bako ba, ba yaro ko babba ba, ba kuma mata ko maza kurum ba? Tarihin nan ba nisa ya yi ba, balle a ce mun manta shi haka da wuri.
Yadda kuma wasu da ke Kudanci ke daukar cewa ai matsalar ta Arewa ce ko ta addinin Musulunci ne kurum, shi ma babban kuskure ne, matsalar ta’addanci ta kowa da kowa ce, domin kuwa tamkar maciji ce mai kai goma, ba a san da wanda za a yi sari ba. Saboda haka lokaci ya yi da za mu fada wa kanmu gaskiya, mu fito domin mganin wannan matsala kafin ta kara ta’azzara, ba kuma wanda ya dace ya kasance sahun gaba irin Gwamnatin Tarayya, wadda ke da jami’an tsaro da alhakin tsare rayuka da dukiyoyi. Idan kunne ya ji to jiki ya tsira….