Da Dumi Dumi

Daga kiwon kaza zuwa shanu 150: Yadda manomi dan shekara 28 ya zama miloniya

Yayin da yake dan shekara 5 zuwa 7 wata mata ta ba Muhammed Abdullahi kaza domin ya kiwata. Daga baya kazar ta haifi kaji 50 wadanda suka raba da matar. Nasarar  ta sanya wata matar daban ta ba shi akuya domin ya kiwata. “Na kiwata akuyar har ta haifi ’ya’ya 30,” kamar yadda ya tuna. “A wancan lokaci ban ma san ko me zan yi da wadannan kudi ba. Iyayena kan sayar da su domin saya mini muhimman abubuwan da nake bukata musamman a lokacin Sallah. To a daidai lokacin ne na lura akwai yiwuwar kiwo ya karbe ni, saboda duk dabbar da na kiwata sai ta bunkasa. Ta haka na fara kiwo,” inji shi.

Ya kara da cewa: “Wata rana, sai na gaya wa kaina tunda ina da ilimin kiwo kuma yana kai mini me zai hana in ci gaba da harkar watakila har ta kai ga in samar wa matasa ayyukan yi. Hakan ne ya karfafa mini gwiwar fara kiwon.”

A yau Alhaji Muhammad Abdullahi yana da garken shanu da kadan daga cikinsu ne kawai na gida, yayin da sauran na waje ne da ya tagwaita halittarsu ta hanyar fasahar zamani. “Muna sayen maniyyin na waje mu saka wa na gida. Ya danganta da abin da muke son mu yi ne. Idan ina son bijimi ko karsana, za mu same su da zarar sun haihu, sa’annan sai mu fara horar da su kan yadda za susaba da yanayinmu,” inji shi.

“Na biyu kuma muna hada shanun Brahman na Amurka da matan shanunmu na gida, sai su haifa mana manyan shanu fiye da kashi 100 na idan da mun hada auren shanun Brahman da Brahman na Amurka,” inji shi.

Manomin ya ce yana da ma’aikata 65 da ke aiki a gonarsa. Kuma yana da shanu 150 da agwagi da tsuntsaye da awaki da kaji da tumaki da yake kiwatawa agonar tasa.

ADVERTISEMENT

 

 

Share
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya