Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Daga sana’ar walda na koma sayar da kayan gini – Aliyu Sulaiman

Aliyu Sulaiman

Wani matashi mai suna Aliyu Sulaiman da ke zaune a Unguwar Sabuwar Kasuwa da ke cikin garin Katsina kuma ke karatun digiri ak an harkokin kasuwanci a Jami’ar Umaru Musa, ya ce, sana’ar sayar da kayan gini ta fiye masa yin aikin gwamnati. Matashin ya shaida wa Aminiya a Katsina dalilansa na fadin haka.

“Ni dai mahaifina sana’ar walda yake yi da kuma ita ya taso daga Kano ya dawo nan Katsina. Kuma kamar yadda muka samu labari, a lokacin da ya zo nan Katsina shi ne Bahaushen farko da ya zo yana yin wannan sana’ar. Da ita muka tashi a gidanmu muka ga ana yi. Ita ce kuma sana’ar da muka fara koyo. Duk da shiririta ta yarinta ba ta hana ni ci gaba da koyon sana’ar ba. Ga zuwa makarantar boko da ta allo ga kuma zuwa wajen aiki in an taso. A haka dai har na koyi wannan sana’a ta walda tare da sauran dangina. Muna tafiya a cikin wannan yanayi, wani lokaci a yi kailula, wani lokaci a bi abokai wankan tafki da sauransu,” inji shi.

ADVERTISEMENT

Aliyu ya kara da cewa, mahaifinsu ya lura da sun kama hanyar koyon sana’ar kuma sun iya, sai kuma ya kara fadada harkar inda ya bude wajen sayar da kayan gini.

“To maganar gaskiya wannan harka ta sayar da kayan gini ita ce ni zan ce na fi mayar da hankali a kanta sosai. Kuma ina tabbatar maka cewa, duk wani abin alheri wanda za a ce sana’a ko kasuwa ko wani aiki ya kawo wa mutum na ci gaba, to wannan harka ta yi mini shi kuma cikin yinta nake. Don ni yanzu wannan harka ta fiye mini aikin gwamnati, saboda shi yana da wa’adi ita kuwa sai dai mutuwa. Koda zan yi aikin gwamnati duk da ina karatu a yanzu sai dai in yi don kariya kawai amma ba don abin dogara ba. Ka ga na yi gida, na yi aure ga abin hawa ga abubuwan rufin asiri duk Allah Ya hore mini ba tare da na je na matsa wa kowa ba. Kowane lokaci mahaifinmu yana gargadinmu a kan cewa, mu yi kokarin dogaro da kai ba ga wani ba koda shi da ya haife mu, domin za a wayi gari babu shi,” inji shi.

ADVERTISEMENT

Daga nan sai matashin ya yi kira ga matasa su rungumi sana’o’i da harkokin kasuwanci ba wai su jira aikin gwamnati ba wanda ya ce, ya yi karanci a hanlin yanzu ga kuma masu bukata kullum na karuwa. “Sannan muna yin tuni ga gwamnati musamman ta Jihar Katsina a kan cewa, ta rika waiwaye a kan alkawuran da ta dauka cewa, duk wani aiki in za ta ba da to za ta ba dan jihar ne, haka kuma sayen kayan aikin za ta yi shi ne daga ’ya’yan jihar. To gaskiya mafi yawan lokuta sai dai mu gani ana kawowa bayan ga su muna da su a gida,” inji Aliyu Suleiman.