✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Daga taskar tsohon mai hoto BABA SHETTIMA (9

Alhaji Shehu Usman Aliyu Shagari, zababben shugaban qasa da ya yi mulki a tsakanin 1 ga watan Oktoba 1979 zuwa 31 ga watan Disamba, 1983.  An sake zabarsa a karo na biyu a shekarar 1983 amma Cif Obafemi Awolowo na Jam’iyyar UPN da Alhaji Waziri Ibrahim na Jam’iyyar UNPP sun kalubalanci sahihancin zaven a kotu amma daga baya kotun daukaka kara ta tabbatar da Shagari a matsayin wanda ya yi nasarar lashe zaben  Sai dai a ranar 31 ga watan Disamba 1983 ne Janar Muhammad Buhari ya yi masa juyin mulkin da ba a kashe kowa ba.  Gwamnatin Buhari ta tsare shi a wani gida har na tsawon shekara biyu da rabi ba tare da ya ga hasken rana ba al’amarin da ya ja masa matsalar dusashewar ido tun daga wancan lokaci