Search
Subscribe
Daga wanke-wanke  na mallaki gidajen abinci  7 –  Okoro Isaac

Mista Okoro Isaac Wada

Daga wanke-wanke  na mallaki gidajen abinci  7 –  Okoro Isaac

Mista Okoro Isaac Wada (JP), shi ne Mamallaki kuma Manajan Daraktan Gidan Abinci na Aroma Restaurant da ke Gombe. A tattaunawarsa da Aminiya ya ce daga wanke-wanken tukwane da kwanuka a otel din Libarty ne, ya mike har ya mallaki manyan gidajen abinci na zamani guda 7 a jihohin kasar nan:

Yaya aka yi ka faro wannan sana’a?

Sunana Okoro Isaac Wada, ni ne mamallaki kuma Manajan Daraktan gidan abincin nan da yake tashe yanzu a garin Gombe, wanda ake kira da Aroma Restaurant

Da farko dai da aikin wanke-wanken tukwane na fara aiki a otel din Liberty da ke Gombe a 1983, inda na yi aiki na tsawon shekara 10 da wata 11. A wannan aiki na wanke-wanken har na kai matsayin mataimakin babban mai dafa abinci a otel din, har na zama ni ne babban mai dafa abinci. Sa ido da nake yi ne wajen kula da yadda ake sauran ayyukan har na iya na kaiwa  wannan mataki na babban mai dafa abinci. Saboda yadda na fara aikin daga kasa ne wato wanke-wanke sai na ji ina shawa’ar ni ma a gaba in bude nawa; har Allah kuma Ya amsa addu’ata.

Kafin ka kai matakin babban mai dafa abinci, ka je wani kwas ne kan girki?

Ban yi kowanne kwas ba, yau da gobe kawai da nake sa ido ne, domin ni karatun boko ma ban yi nisa ba. Iyakacina aji bakwai na firamare, ban kara gaba ba saboda iyayena ba su da kudi. Amma sai ga shi yanzu har masu digiri nake bai wa aiki a gidan abincina na Aroma.

Ka ce yau da kullum ne ya sa ka kware wajen iya girki, ashe ko mutum bai yi karatun koyon girki ba zai iya ke nan, mene ne sirrin?

Gaskiya na tsaya ne na yi aiki ba ha’inci, saboda ina da sha’awar bude nawa a gaba, idan na samu dama. Shi ya sa na tsaya na koyi girkin. Ba wata makaranta na je ba kuma babu wani sirri sai dai kawai Allah Ya sa sayar da abinci ne sanadin arzikina kawai.

Kana da kamar shekara nawa ka fara aiki a otel din Liberty?     

Lokacin ina karami ne, na gama firamarena aji 7 a  1979. A 1980 zuwa 1981 na fara koyon gyaran babur. A 1982 na zo Gombe daga garinmu; inda mai otel din Liberty Mista Adelaja ya dauke ni aiki a wajen da yake sayar da madarar Ice Cream mai suna Gardel Nigeria Limited. Lokacin ana sayarwa a mota, daga nan sai ya mayar da ni otel dinsa na fara wanke-wanke. Ka ji yadda na fara aiki a gidan abinci ke nan.

Bayan ka shafe shekara 10 da wata 11 kana aiki a otel din Liberty, da ka bar nan ne ka bude gidan abinci na Aroma ko yaya aka yi?

A’a, bayan na bar otel din Liberty sai na koma aiki da ‘Making Touch’ inda nan ne masaukin Shugaban Kasa yake yanzu. A 1995 na yi aiki da su, nan na shekara daya sai na bari na koma wani gidan abinci mai suna Rahama Restaurant a Jekadafari, kusa da wajen sayar da motoci na Alhaji Gambo Isari. Muna aiki tare da matar mai gidan abincin na tsawon shekara 9 da wata 6, nan ma sai na bari.

Yaya aka yi da ka bar aiki da Rahama Restaurant?

Bayan da na bar Rahama sai wani tunani ya zo min a kan ni ma in bude nawa mana tunda kowa a Gombe ya san na iya abinci. Ai da haka ake farawa, shi ne na bude  nawa gidan, na sa masa suna Aroma Restaurant a shekarar 2003. Na bude shi a can kusa da Bankin Unity, kan hanyar zuwa Biu.

Tunda duk inda ka yi aiki yaron aiki kake yi, ba kai ne mai shi ba, da jarin nawa ka bude naka gidan abincin?

Gaskiya a lokacin ba ni da kudin da za su ishe ni jari. Dan abin da nake da shi, da shi na biya kudin haya na shekara biyu sai kawuna mai suna Alhaji Abdullahi Hassan, kanen mahaifiyata (Allah Ya jikansa), shi ne ya ba ni jarin Naira dubu 100. Da su na sayi kujeru, na sayi kwanuka, sai kudin suka kare. Duk kayayyakin abincin bashi aka ba ni a kasuwa. Da bashi na fara dafa abinci a Aroma Restaurant.

Da ka bude Aroma Restaurant, wane ne manajanka na farko?

Ganin ba ni da jari da karfin daukar masu aiki da yawa, ni da kaina nake aikin dafa abincin, ganin cewa ni kwararre ne a kai. Sannan ni ne Manaja, ni ne mai girki sai yara kadan masu ba da abinci.

Bayan da ka bude Aroma a shekarar 2003, zuwa yanzu kasuwancin ya habaka kuwa?

Gaskiya ya habaka, domin da bashi na fara dafa abinci, na bude gidan da ’yan kudi kadan amma yanzu ina da gidajen abinci na Aroma daban-daban kuma wannan na kusa da bankin Unity din shi ne na farko, har Allah Ya sa na bude wannan na Jekadafari, har ta kai ina da rassa guda shida; yanzu ina shirin bude na bakwai a Jihar Adamawa.

Ganin cewa ka samu nasara daga karami ka zama babba, mene ne sirrin?

To ban san mene ne sirrin ba. Gaskiya abin na Allah ne, ni dai na rike sana’ar ce hannu bibiyu Allah kuma Ya ba ni sa’a. Shi ne kawai ba wani abu ba, sannan ina karbar gyara a duk lokacin da mutum ya ci abinci ya kula da gyaran idan aka gaya min ina gyarawa, don su ne masu saye, don su nake yin abinci; idan ban gyara ba, gobe ba za su dawo ba.

Mutum nawa suke aiki a karkashin wannan gidan abinci naka?

Ina da rassa shida, ina shirin bude na bakwai. Masu aiki kuma akalla akwai kamar 300 yanzu, ina ta shirye-shiryen bude wani reshe ne a Bauchi da Adamawa, ina da guda biyu a cikin Gombe, daya a Ashaka biyu a Bauchi, daya a Taraba. Wanda zan bude a Bauchi shi ne zai zama hedkwatarmu na Bauchi, don yanzu haka akwai daya kafin wanda nake shirin budewa.

Wadanne matsaloli ka fuskanta a sana’ar sayar da abinci?

Na fuskanci matsaloli da yawa da adawa daga abokan sana’a, ganin Allah Ya daga ni.

Wace nasara ka samu kuma?

Nasara ai a fili take, na fara da gidan abinci daya, yanzu na mallaki gidajen abinci daban-daban har bakwai ba kuma a iya Gombe ba; ai ba karamar nasara na samu ba.

Daga karshe mene ne kiranka ga masu wannan sana’a?

Kirana shi ne, mutane su yi gaskiya sannan su yi hakuri, domin dole sai an fuskanci matsalolin da sai an jira. Ba lokaci daya ne mutum zai yi arziki ba. Ka ga ni ma ai shekara goma sha shida na yi da watanni ina yi hakan, shi ya sa har na kai inda nake yanzu. Da ban yi hakuri da rayuwa ba, da ban zama abin da na zama ba yanzu.

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin