✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Daga yanzu ’yan sandan F-SARS za su rika sa kayan sarki

Sufeto Janar na ’Yan sandan Najeriya Ibrahim Idris ya bayar da umarnin yin gyara a kan irin ayyukan da jami’an yaki da fashi da makami…

Sufeto Janar na ’Yan sandan Najeriya Ibrahim Idris ya bayar da umarnin yin gyara a kan irin ayyukan da jami’an yaki da fashi da makami (F-SARS) za su rika yi a kasar nan baki daya.

Wasu daga cikin gyare-gyare da aka yi wa sashin sun hada da cewa daga yanzu jami’an za su rika sanya kakin ’yan sanda a lokacin da suke kan aiki kuma za su daina tsayawa a kan hanyoyi da sunan bincike, sai idan ya zama dole.

Shugaban Kwamitin da Sufeto Janar ya nada domin ilimantar da jami’an F-SARS a kan sanin makamar aiki, Mataimakin Kwamishinan ’Yan Sanda Adepoju Ilori ne ya fadi haka lokacin da kwamitin ya ziyarce jami’an a Ibadan. Ya ce, an yi kyakkyawan tanadi wajen yin wannan gyara ne domin tsabtace ayyukan sashin na F-SARS da aka kakkabe hannunsa daga shiga cikin wasu ayyuka da suka shafi sassa daban na ’yan sanda. Daga yanzu jami’an sashin za su rika lura da ayyukan yaki da fashi da makami da masu garkuwa da mutane ne kawai.

Adepoju ya shaida wa ’yan jarida cewa sanya kakin ’yan sanda ga jami’an a lokacin da suke aiki zai taimaka kwarai wajen dakile masu yin sojan gona ga wannan muhimmin aiki na tsaron lafiya da dukiyar jama’a. Ya ce, an dora wa kwamitin nasa  alhakin ziyartar bangaren F-SARS na sashen Kudu maso Yamma ne domin gudanar da laccoci ga jami’anta tare da ilimantar da su sanin makamar aiki kan yadda za su rika mu’amala da jama’a.

Ya ce, aikin da suke yi a yanzu a wannan sashe, umarni ne daga fadar Shugaban kasa, musamman saboda yawan koke-koken da jama’a suke yi kan rashin gamsuwa da kasancewar ’yan sanda cikin farin kaya rike da bindigogi.