✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dahuwar kabeji mai nama

Barkanmu da warhaka Uwargida tare da fatan ana lafiya. Yaya yara? Allah Ya ba mu ikon tarbiyyantar da su yadda ya kamata. A yau na…

Barkanmu da warhaka Uwargida tare da fatan ana lafiya. Yaya yara? Allah Ya ba mu ikon tarbiyyantar da su yadda ya kamata. A yau na kawo muku yadda ake girka kabeji mai nikakken nama a cikinsa. Akwai abubuwan karyawa da dama, yawan girka abinci iri daya na ginsar yara da maigida. A kullum mutum yana son cin sabon girki. Don haka dole ne mata a dage wajen koyon nau’o’in girke-girke domin kayyatar da abincin da ake dafawa a gida.

Abubuwan da za a bukata

  • Nikakken danyen nama
  • kabeji
  • Attarugu
  • Koren tattasai
  • Albasa
  • Magi
  • Karas
  • Kori
  • Citta
  • Tafarnuwa
  • Man gyada

Hadi  

A wanke nama sannan a markada shi a na’urar nika nama a ajiye a gefe. A dora tukunya a wuta da gishiri kadan sannan a samu kabeji a bare shi manya-manya a tafasa da gishiri kadan na tsawon minti biyar. Sannan a tsame a ajiye a gefe.

A dora tukunya a zuba man gyada kadan sannan a zuba albasa da nikakken naman a zuba magi da kori da garin citta da tafarnuwa da jajjagen attarugu da yankakken koren tattasai a yi ta gaurayawa har sai naman ya nuna ya soyu sannan  a kwashe.

A sami kabejin da aka tafasa sannan a shimfida shi kamar tabarma sai a debo hadin nama a zuba a ciki sannan a yi masa nadin tabarma a tottoshe gefe-gefen.

Sai a dora tukunya a kan wuta a zuba man gyada kadan ba mai yawa ba, sannan a zuba wannan ninkin kabejin a cikin man a soya sama-sama sannan a kwashe,

Za a iya cin wannan hadin kabejin da shayi mai zafi da safe a matsayin abin karyawa.