✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dahuwar kazar Turai

Sallama a gare ki Uwargida. Allah Ya biya mana bukatunmu na alheri. A yau na kawo muku yadda ake dahuwar kaza mai danko. Na san…

Sallama a gare ki Uwargida. Allah Ya biya mana bukatunmu na alheri. A yau na kawo muku yadda ake dahuwar kaza mai danko. Na san da yawa daga cikinku idan sun ji an ce kaza mai danko, abin da za su fara tunawa shi ne, ko za a iya cin wannan girki? Tabbas za a iya ci. Akwai nau’o’in girke-girke da dama da idan an ga yadda ake dafa su sai a ga kamar ba za a iya ci ba. Kamar yadda nake ba da shawarar yadda uwargida za ta rika canja girke-girke kamar taba girkin gida da kauye da kuma na kasashen waje ba don komai ba sai don nuna wa maigida kwarewarta a irin wadannan girke-girke shi ya sa a yau na kawo muku yadda ake girka kaza mai danko.

 

Abubuwan da za a bukata

•        Cinyoyin kaza/kaza gaba dayanta

•        Citta danya

•        Danyar tafarnuwa

•        ‘Soy sauce’ (yana nan baki a kwalba. za a iya samunsa a manyan shaguna )

•        Attarugu

•        Albasa

•        Magi/gishiri

•        Kori

•        Zuma

•        Man gyada

Hadi

Bayan Uwargida ta wanke kazarta kamar yadda na koya mana a baya, sai ta dora ta a matsami domin ruwan jikin kazar ya tsane. Sannan ta kankare bayan citta kamar rabinta tare da tafarnuwa bayan ta bare ta jajjaga su a wuri daya. Ta dauko attarugu kamar biyu ko uku ta yayyanka kanana. Sannan a dauko albasa ta yi mata yankan tuyar kwai ta ajiye a gefe.

Ta samu roba, sannan ta zuba jajjagen tafarnuwa da citta a ciki sannan ta zuba magi da kori da albasa da kuma ‘Soy sauce’ da zuma kamar cokula uku sannan ta gauraya hadin da cokali ta dauko wankakkiyar kazarta ta tsoma a cikin wannan hadi. Ta gauraya kazar a cikin hadin yadda komai zai shige ta ta dauko leda ta rufe saman kwanon/roba sannan ta bude gidan sanyi (fridge) ta saka na tsawon awa hudu zuwa shida.

Bayan haka, sai ta dauko tukunyar tuya ta zamani (non-stick frying pan) ta dan diga man gyada kadan kamar na tuyar kwai. Bayan ya yi zafi, ta dauko kazar ta sa a cikin tukunyar tuyar tana juya ta gefe-gefe har sai ta yi launin toyuwa. Sannan ta kwashe ta a ajiye a gefe. Ta zuba wannan ruwan hadin da ya rage na hadin kazar a tukunyar ya yi tafasa daya sannan sai ta mayar da kazarta ciki ta gauraya sannan ta sauke. Sai a ci da jus din lemo ko da dafa-dukan shinkafa. A ci dadi lafiya.