✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dakatar da hako ma’adinai a Zamfara zai inganta harkokin tsaro a jihar?

A farkon makon nan ne aka bayar da umarnin dakatar da harkokin hako ma’adinai a Jihar Zamfara a ci gaba da kokarin kawo karshen harkokin…

A farkon makon nan ne aka bayar da umarnin dakatar da harkokin hako ma’adinai a Jihar Zamfara a ci gaba da kokarin kawo karshen harkokin ta’addanci da ’yan bindiga suka jefa jihar. Wannan ya sa wadansu ke tunanin mece ce alakar ta’addanci da hako ma’adinai. Wannan ya sa wakilan Aminiya suka zagaya domin jin ra’ayoyin mutane a kan wannan batu, kuma ga abin da suke fada:

 

Hakan zai iya taimakawa – Babangida Dankutogo

Daga Ibrahim Babangida Surajo

“A gaskiya wannan zai taimaka sosai wajen tabbatar da tsaro a Jihar Zamfara. Domin kuwa idan ba a yi haka ba, ai ana yin bosoruwa ne kawai, wai rufe gida da barawo. Don haka dakatar da hako ma’adinan zai taimaka matuka a nawa ra’ayin.”

 

Babu alaka tsakanin hako ma’adinai da ta’addanci – Shu’aibu Umar

Daga Ibrahim Babangida Surajo

“Ni dai gaskiya  a ra’ayina babu alaka tsakanin harkar hakar ma’adinai da abin da yake faruwa a Zamfara. Ya kamata gwamnati ta yi kokarin samo hanyoyin magance rikicin ne kawai wanda da ya ki ci ya ki cinyewa. Wannan shi ra’ayina a takaice.”

 

Zai taimaka matuka – Aminu Aliyu

Daga Jamilu Adamu

“Dalilina kuwa shi ne wadansu daga cikin masu hakar ma’adanan ba abin da yake kai su ba ke nan, suna fakewa da hakar ma’adanai suna shuka barna. Sannan kuma gwamnati ta samu bayanin sirrin kafin ta hana wannan harka. Ina kira ga gwamnati ta sama wa wadannan mutanen wata hanya ta harkar hako ma’adanan domin za su iya zama barazana gare ta.”

 

Hanawar ba za ta kawo karshen matsalar ba – Abubakar Abdullahi

Daga Jamilu Adamu

“Dalilina kuwa shi ne, mene ne alakar da ke tsakanin masu hakar ma’adanai da masu kashe-kashen Jihar Zamfara? Na tabbata babu wata alaka ta kusa ko ta nesa. Hasali ma dakatarwar za ta haifar da tabarbarewar tsaro, saboda wadannan mutane da suke hakar ma’adanan za su shiga wani hali mai wuya, a sanadiyyar haka za su iya komawa ’yan ta’adda, ko su hade da ’yan ta`addan. A karshe ina kira ga gwamnati  ta duba ta kawo wata hanyar da za ta kawo karshen rikice-rikicen Jihar Zamfara.”

 

Dakatar da hako ma’adanai zai inganta tsaro – Aminu Tukur

Daga Rabilu Abubakar, Gombe

“Dakatar da hako ma’adinai zai inganta tsaro saboda dalilin ma’adinai din ne ake hai hare-haren a nawa tunanin. Masu son amfani da ma’adinan ba sa son su fitar da kudi su sayi filin sai dai su kwata da karfi. Idan aka hana harkar hako ma’adinan baki daya za a samu ingantuwar tsaro sosai, don haka a ra’ayina dakatarwar da aka ta yi daidai.”

 

Dakatar da hako ma’adinai ba zai inganta tsaro ba – Babangida Usman

Daga Rabilu Abubakar, Gombe

“Dakatar da hako ma’adanai ba zai inganta tsaro a Jihar Zamfara ba. Gwamnati ita ta san yadda za ta shawo kan matsalar tsaro a kasa, don haka hakkinta ne ta bi yadda za ta bi. Ina da yakinin cewa babu wata matsalar da za ta gagari gwamnati sai dai idan ba ta so ba.”