✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dakatsalle zuwa Kwanar Dangora hanyar mutuwa ce – Direbobi

A Jihar Kano, direbobi sun koka kan lalacewar hanyar da ta tashi daga Dakatsalle zuwa Kwanar Dangora, inda suka bayyana ta da cewa hanyar mutuwa ce.…

A Jihar Kano, direbobi sun koka kan lalacewar hanyar da ta tashi daga Dakatsalle zuwa Kwanar Dangora, inda suka bayyana ta da cewa hanyar mutuwa ce.

Aminiya ta gano cewa kusan kullum akan rasa rayuka da dukiyoyi saboda aikin da ake ci gaba da gudanarwa a tagwayen hanyoyin. Wadansu daga cikin direbobin da suka zanta da wakilinmu sun koka da tafiyar hawainiyar da aikin ke yi tare da yin kira ga gwamnati ta bude wasu bangarorin titin da aka rufe domin a samu saukin wucewar ababen hawa.

Sun ce halin da ake ciki a yanzu zai tsananta idan ba a kammala aikin ba har zuwa daminar badi. Sun kuma yi zargin cewa ’yan fashi da makami na yin amfani da wannan dama wajen tare masu ababen hawa da ke bi ta hanyar.

Malam Abbas Abdullahi, yana daya daga cikin direbobin da suka bayyana yawan shingaye daga Dakatsalle zuwa Kwanar Dangora a matsayin Sambisa saboda yawan rasa rayuka da ake yi a wajen sanadiyyar hadarin mota.

“Gaskiya abin da muke gani a kan hanyar Kano zuwa Abuja babu kyau, musamman saboda wannan gyaran hanya da ake yi. Mun ga bala’o’i a wannan hanya kuma a kullum gani muke yi kamar aikin ba mai kammaluwa ba. Babbar damuwarmu daga Kano zuwa Abuja shi ne wani shinge mai nisan kusan  kilomita 70 daga Dakatsalle zuwa Kwanar Dangora saboda a wannan dan tsakani an rasa rayuka sosai saboda lalacewar hanyar.

“Duk inda ka duba ramuka ne kuma duk kokarin da ka yi na kauce musu akwai hadari. Na ga lokuta da dama da manyan motoci ke kokarin kauce wa rami sai su danne karamar motar da ke kusa, tare da hallaka mutanen da ke ciki,” inji shi.

Ya kara da cewa baya ga hadurra, ’yan fashi na cin karensu babu babbaka ba tare da sun fuskanci kalubale daga jami’an tsaro ba.

Lamir Abubakar ya ce Dakatsallle zuwa Kwanar Dangora ba ta biyuwa daga karfe 8 na yamma zuwa 5 na safe saboda ’yan fashi. “Yanzu mukan kwashe sa’o’i uku da rabi zuwa hudu kafin mu isa Kaduna saboda lalacewar hanyar. Baya ga hadarin mota wanda yanzu ya zama ruwan dare, da wuya ka wuce ta Dakatsalle zuwa Kwanar Dangora ba ka ci karo da ’yan fashi ba. Da yawan direbobinmu sun rasa rayukansu,” inji shi.

Shi ma wani direba, Abdulkadir Malami ya koka da tafiyar hawainiyar gyaran hanyar tare da yin kira ga hukumomi su matsa wa ’yan kwangilar domin su kammala aikin cikin lokaci.

Alhaji Abubakar Habibu, wanda shi ne Mataimakin Ma’ajin Kungiyar Direbobi ta NURTW reshen Na’ibawa Kano, ya lissafa wasu shingaye da ke kawo matsala a kan hanyar, musamman ga direbobi masu zuwa Kano da Abuja. Ya yi kira ga gwamnati ta matsa wa kamfanin da ke aikin, domin saukaka wa direbobi matsalolin da suke fuskanta.

Alhaji Zubairu Saleh, Mataimakin Shugaban Kungiyar NURTW a Na’ibawa, ya yaba wa ingancin aikin da ake yi amma kuma ya nemi gwamnati ta sanya ido wajen ganin an kammala aikin cikin lokaci domin jin dadin al’umma masu amfani da hanyar.