✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dakin sayar da abinci na Lionel Messi yana raba abinci kyauta a Ajentina

Rahotannin da ke fitowa daga Ajentina sun ce wani dakin sayar da abinci mallakar Lionel Messi  ya fara raba wa talakawa abinci kyauta na tsawon…

Rahotannin da ke fitowa daga Ajentina sun ce wani dakin sayar da abinci mallakar Lionel Messi  ya fara raba wa talakawa abinci kyauta na tsawon kwana 15 don saukaka musu kuncin rayuwa.

Rabon abincin ya fara ne daga ranar 5 zuwa 20 ga watan nan na Yuli.

Nau’in abincin da shagon yake raba wa jama’a kyauta sun hada da shinkafa da madara da shayi da kayan makulashe.

Kamar yadda rahoton ya nuna, Ajentina tana fama da matsalar tattalin arziki a halin yanzu wanda hakan ya sa da yawa daga cikin mutane suke kwana a kan titi ba tare da sun yi kalaci ba.

Wannan ya sa shagon sayar da abinci na Lionel Messi mai suna  BIP ya yanke shawarar ciyar da mabukata abinci kyauta na tsawon kwana 15.

“Muna ciyar da mabukata abinci kyauta tun daga karfe 7 zuwa karfe 9 na dare a kullum har na tsawon kwana 15.  Kuma mun fara wannan taimako ne daga ranar 5 zuwa 20 ga watan nan (Yuli),” inji Ariel Almanda, Manajar da ke kula da shagon sayar da abincin.

Ajentina dai ta fada matsalar tattalin arziki ne wanda hakan ya sa da yawa daga cikin mutanen kasar ba sa iya samun kalaci a mafi yawan lokuta saboda talauci.