Subscribe
  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin
Dakingari ya zama Jakadan Gwandu

Dakingari ya zama Jakadan Gwandu

Mai martaba Sarkin Gwandu Alhaji Muhammad Iliyasu Bashar, ya nada Alhaji Abubakar Maigandi Dakingari a matsayin sabon Jakadan Gwandu.

An nada sabon Jakadan ne a fadar Abdullahin Gwandu da ke Birnin Kebbi a ranar Asabar 19/10/2019. An haifi Alhaji Abubakar Maigandi a ranar Juma’a 1/10/1968 a garin Dakingari da ke Karamar Hukumar Suru a Jihar Kebbi. Mahaifinsa Alhaji Maigandi shi ne Sarkin Alhazzan Dakingari.

Alhaji Abubakar Maigandi ya soma karatun allo a makarantar Malam Usman Dakingari  daga nan ya shiga makarantar firamare a 1973 zuwa 1979, sannan ya zarce zuwa Kwalejin Horon Malamai (GTC) da ke Argungu, a 1979 zuwa 1984 daga nan  ya zarce zuwa Kwalejin Kimiyya da Sana’a ta Birnin Kebbi a 1984  zuwa 1987 inda ya samu takardar shaidar  malanta ta kasa (NCE).

Bayan ya kammala ne sai Ma’aikatar Ilimi ta tsohuwar Jihar Sakkwato ta dauke shi aiki inda aka tura shi makarantar Sakandaren Gwamnati da ke Dakingari a matsayin malami, daga bi sani ya canja wurin aiki zuwa Hukumar Kula da Ilimin Firamare inda aka tura shi garin Wurno a matsayin injiniya. Daga Wurno sai aka yi masa canjin aiki zuwa garin Tambuwal daga nan sai ya sake komawa Kwalejin Kimiyya da Sana’a ta Birnin Kebbi inda ya sami takadar karamar diploma daga baya ya kara samun babbar diploma (HND) a fannin injiniya.  Daga nan sai aka tura shi Jihar Kwara don yin hidimar kasa.

Bayan ya kammala hidimar kasar ce da ya dawo sai ya canja wurin aiki zuwa  Hukumar Kula da Harkokin Kananan Hukumomi inda aka tura shi Karamar Hukumar Suru a matsayin injiniya.

A shekarar 2004 Alhaji Abubakar Maigandi ya ajiye aikin gwamnati inda ya rungumi aikin gona da kasuwanci yana sayen fata daga Dakingari da Sakwatto da Gusau har zuwa Kano.

Daga bisani Alhaji  Abubakar Maigandi ya shiga harkar sayar da man fetur inda ya samu daukaka har ya kafa kamfani mai suna Garima Petroleum Limited, inda ya ke zaune a Minna da Abuja kuma ya bude rassa a sassan kasar nan.

An zabi Alhaji Abubakar Maigandi a matsayin Shugaban Kungiyar Dillalan Man fetur ta Kasa (IPMAN)  reshen Daffon NNPC da ke Minna kuma an sake zabensa a matsayin Mataimakin Shugaban IPMAN na Kasa.

Alhaji Abubakar Maigandi yana da matan aure biyu da ’ya’ya da dama.

A bisa gudunnawar da yake ba Jihar Kebbi da kuma samar wa ’yan asalin jihar da sauran ’yan Najeriya ayyukan yi ne ya sa Masarautar Gwandu ta ga ya dace a nada shi a wannan sarauta ta Jakadan Gwandu.

Da yake zantawa da Aminiya bayan kammala nadin, sabon Jakadan Gwandu Alhaji Abubakar Maigandi Dakingari, ya mika godiyarsa ga Mai martaba Sarkin Gwandu, da majalisarsakan nada shi a wannan sarauta, ya kuma ce da yardar Allah ba zai ba Masarautar Gwandu kunya ba, kuma zai kara kaimi sosai wajen ci gaban Jihar Kebbi da al’ummarta.

Daga nan ya mika godiyarsa ga ’yan uwa da abokan arziki wadanda suka halarci wannan biki da aka yi na nadinsa.