✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dalalinmu na kafa tashar talabijin ta Al-Irshaad – Sheikh Jingir

A kwanakin baya ne Kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah ta Kasa ta gudanar da taron kaddamar da tashar talabijin  tauraron dan Adam mai…

A kwanakin baya ne Kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah ta Kasa ta gudanar da taron kaddamar da tashar talabijin  tauraron dan Adam mai suna Al-Irshaad a Birnin Tarayya Abuja. Wakilinmu ya tattauna da Shugaban Majalisar Malamai ta Kasa ta Kungiyar Sheikh Muhammad Sani Yahya Jingir kan manufar kafa tashar da abubuwan da ta kunsa kamar haka:

Aminiya: Mene makasudin bude tashar Al-Irshaad da kungiyar Izala ta yi?

Sheikh Jingir: Kowa ya san aikin wannan kungiya shi ne wa’azi da karantarwa. Kuma karantarwar nan ta kunshi makarantun firamare da sakandare da manyan makarantu. Kuma salon karantarwar nan bayan tsari na makaranta, akwai tsarin tarurrukan wa’azi. An san mu da wa’azi a kauyuka da garuruwa da birane a dukkan jihohin kasar nan, da kasashen waje.

Yanzu Allah Ya kawo mu zamanin da akwai rediyo da talabijin da jaridu da mujallu. Kuma dukkan wadannan hanyoyi ne na isar da sako zuwa ga mutane a birane da kauyuka.

Don haka manufar bude wannan tasha ta Al-Irshaad da wannan kungiya ta yi ita ce domin mu ci gaba da gudanar da wannan aiki da muka sanya a gaba,  na wa’azi da karantar da  addinin Musulunci, don mu dora bayin Allah a kan shiriya, don  tsamo su daga bata.

Shi ya sa muka sanya wa tashar suna Al-Irshaad, ma’ana shiriya daga Allah. Wato a shiryar da mutane su bar bata, su dawo kan hanya ta gaskiya.

Saboda haka za ka ga shirye-shiryen da tashar take gabatarwa na karantar da Alkur’ani Mai girma da hadisan Manzon Allah (SAW) da litattafan fikihu da maganganun aure da noma da gado da sana’o’in hannu da hulda a tsakanin al’umma da sauransu.

A takaice wannan tasha shirye-shiryen da take gabatarwa, sun shafi rayuwar dan Adam baki daya. Don haka muka bude tashar don sakonmu ya shiga ko’ina a duniya.

Kuma idan ka dubi duniyar yau a harkokin watsa labarai, za ka ga ko labari aka bayar cewa wani ya kai babansa Makkah ya saya masa gida, ba su cika mayar da hankali kan irin wannan labarai ba. Sai labaran yake-yake da fadace-fadace. Amma ita wannan tasha tana mayar da hankali ne kan labaran alheri.

Aminiya: Wato a takaice wannan tasha za ta zama kamar garkuwa ce ga al’umma?

Sheikh Jingir: Kwarai da gaske ita wannan tasha garkuwa ce ga al’umma baki daya, Musulmi da wadanda ba Musulmi ba. Domin zuwa yanzu mun samu masu rubuto mana fatar alheri da godiya daga al’ummar Musulmi, har da Kiristoci sun ce mana suna samun tarbiyyar ’ya’yansu da matansu da makwabtansu ta hanyar shirye-shiryen da wannan tasha take gabatarwa. Saboda haka wannan tasha garkuwa ce ga dukkan ga al’umma da Musulmi da wadanda ba musulmi ba.

Aminiya: Wannan tasha tana watsa shirye-shiryenta ne a wani sashi na duniya, ko tana watsawa ne ga duniya ne baki daya?

Sheikh Jingir: To wannan tasha tana watsa shirye-shiryenta ne ga duniya baki daya. Domin ka ga a wajen Musulmi cibiyar duniya ita ce Makkah. Wata rana ina tafiya a birnin Makkah bayan an sauko daga Arfa, a aikin Hajjin da ya gabata, sai wani mutum ya tsare ni ya ce ya san ni. Na ce a ina ya san ni? Ya ce a talabijin yake ganin wa’azina ya ce shi daga Ghana yake.

Bayan ya wuce muka sake haduwa da wani ya ce shi ma daga Beljiyum yake shi ma yana ganin wa’azina a talabijin. Akwai mutane da dama daga kasashen Afirka da Turai da Asiya da suka rubuto mana cewa suna ganin shirye-shiryen da muke gabatarwa a kasashen da suke zaune. Don haka wannan tasha tana gabatar da shirye-shiryenta ne ga duniya baki daya.

Aminiya: Mene ne babban burin wannan kungiya kan wannan tasha?

Sheikh Jingir: Babban burinmu shi ne Allah Ya ba mu ikon ci gaba da wannan aiki na wa’azantarwa da muka sanya a gaba.

Aminiya: Ganin akwai tashoshin talabijin da suke nuna shirye-shiryen da ba su dace da addinin da al’adunmu ba, wane kira za ka yi ga al’ummarmu kan irin wadannan tashoshi na Al-Irshaad da suke nuna shirye-shiryen addini?

Sheikh Jingir: Yana daga cikin abin da nake fada maka, ka ga wanda Allah Ya taimake shi, Ya sanya wannan tashar gidansa, to ya bude makaranta ta musamman a gidan. Domin da shi da matansa da ’yayansa da ’yan uwansa da sauran makwabtansa za su samu alherin wannan tasha. Domin wannan tasha daga cikin karantarwar da malamanmu suke yi akwai tarbiyyantar da dan Adam da tarbiyyantar da yara da tarbiyyar zaman aure da dukkan abubuwan da suka shafi rayuwar dan Adam ta duniya da Lahira.

Don haka halin da ake ciki na tabarbarewar tarbiyya muna kira ga jama’a su yi kokari su kauce wa tashoshin gidajen talabijin da suke nuna wa iyalansu batsa, domin su tsira a duniya da Lahira.