✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Daliba na rubuta jarabawar WAEC a cibiyar COVID-19

Mai shekara 16 da ta kamu da COVID-19 na rubuta jarabawar WAEC a cibiyar killacewa

Wata daliba mai shekara 16 tana rubuta jarabawar kammala sakandare ta WAEC a cibiyar killace masu cutar COVID-19.

Kakakin kwamitin yaki da COVID-19 a Jihar Kwara, Rafiu Ajakaye ya ce dalibar ta rubuta jabawar Kimiyyar Noma a ranar Laraba, karkashin sa idon jami’an jarabawar ta WAEC.

Shugabar tawagar lura da masu cutar a jihar Kwara, Dakta Kudirat Oladeji-Lambe ta ce alamun cutar ba su bayyana a tare da dalibar ba kasancewar tana cikin mutanen da cutar ba ta yi wa lahani.

“Mara lafiyar na daga cikin daliban ajin karshe na sakandare da suka yi rajistar jarabawar WAEC da ke gudana a yanzu, wanda take rubutawa daga nan. Babu wata alamar illa da cutar ta yi mata”.

Dakta Kudirat ta kara da cewa dalibar “Ta harbu ne bayan ta samu kusanci da mai dauke da cutar a cikin danginta”.

Hakan na zuwa ne yayin bayan wasu rahotanni daga Jihar Gombe da ke cewa wani dalibi mai dauke da cutar yana rubuta a makarantarsu.

A shafin Twitter na Hukumar Kula da Lafiyar Al’umma da Bayar da Taimakon Gaggawa ta Gombe, @GombePHEOC, ta ce an dauko dalibin ne daga inda aka ware wa masu fama da cutar cikin mortar daukar marasa lafiya.

A lokacin ta ce zai rubuta jarabawarsa ne ta biyu ta gwajin sinadarai (Chemistry practical) a makarantar sakandare ta kimiya da ke garin Gombe, (GSSS, Gombe).

Sai dai rahoton bai fayyace ko a ware dalibin zai yi tashi jarabawar ba ko kuma tare da sauran dalibai.