Da Dumi Dumi

Dalibai a Nijar sun yi zanga-zangar adawa da sojojin kasashen waje

A Jamhuriyar Nijar dalibai sun gudanar da zanga-zanga tare da nuna adawa da kasancewar sansanonin dakarun kasashen waje a kasar.

Labaran da jaridun kasar suka fitar na cewa, dubunnan dalibai ne suka taru a gaban ginin Majalisar Dokoki da ke Yamai inda suka bukaci sojojin kasashen waje su fice daga Nijar, sannan gwamnati ta kyautata harkokin ilimi.

Daliban dai sun bukaci sojojin Amurka, Faransa da na Jamus da su bar kasar Nijar inda suka rika daga allunan da ke cewar “Allah daukaka sojojin Nijar” Allah tsine wa sojojin kasashen waje”.

Wani daga cikin jagorin kungiyar daliba Nijar Abdou Moussa ya bayyana cewa suna so ne a karfafa gwiwar sojojin Nijar tare da yin zanga-zanga ga sojojin kasashenw aje da ba sa amfanar kasar da komai.

Moussa ya kara da cewar sakamakon yajin aiki malaman makarantu harkokin ilimi a Nijar sun shiga tsaka mai wuya inda a wannan zangon karatun ba a yi komai ba musamman ma a jami’o’i.

ADVERTISEMENT

A wasu garuruwan na Nijar daban-daban an gudanar da zanga-zanga makamanciyar wannan din ita duk da bukatar ganin sojojin na kasashen waje sun fice daga kasar kamar yadda TRT ta ruwaito.

 

Share