✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dalibai nakasassun sun koka a Jihar Nasarawa

Duk da shirin ilimi kyauta ga nakasassu da ke karatu a manyan makarantun gwamnatin jihar Nasarawa da gwamnatin Injiniya Abdullahi Sule ta kirkiro, dalibai nakasassu…

Duk da shirin ilimi kyauta ga nakasassu da ke karatu a manyan makarantun gwamnatin jihar Nasarawa da gwamnatin Injiniya Abdullahi Sule ta kirkiro, dalibai nakasassu da suke karatu a manyan makarantun jihar sun koka cewa har yanzu suna biyan kudi a wadannan makarantu.

Daliban sun bayyana haka ne a wajen tattaunawa ta musamman da ofishin Daraktan Tsare-tsare da Harkokin Watsa Labaran Gwamnatin Jihar ya shirya da aka gudanar a Jami’ar Jihar da ke garin Keffi.

Shugaban Dalibai Nakasassu na Jami’ar Sunday Musa, ya yi korafin cewa har yanzu suna ci gaba da biyan kudin makaranta da sauran caje-caje a jami’ar duk da cewa gwamnatin jihar ta ba da umarnin a daina karbar kudin makarantansu a wadannan cibiyoyi.

Ya bukaci Gwamna Abdullahi Sule ya gaggauta sa baki a lamarin kuma ya tabbatar an maida wa nakasassun kudin makarantar da suka biya a jami’ar da ya yi zargin Hukumar Gudanarwar Jami’ar tana karba ba tare da sanin gwamnati ba.

Ya ce, “Babban kalubale da muke fuskanta a yanzu a makarantar nan shi ne na rashin wadanda ke karbar magana wato Interpreters a muhimman kwasa-kwasan da muke karanta a jami’ar nan da sauransu. Abin takaici ne idan aka yi la’akari cewa a yanzu wadansu daga cikinmu ne ke aikin Interpreters da hakan ke sa sau da yawa yawancinmu ba ma iya fahimtar abubuwa da ake koya mana. Kuma dalibai makafi a cikinmu sukan samu matsala wajen tafiya ajujuwansu.”

Daya daga cikin dalibai nakasassu mai suna Isma’il Abdul ya koka dangane da yadda ya ce bincike ya nuna  kashi 15 na nakasassu da ke jihar kashi 7 na karatu amma kashi 2 ne kacal cikinsu ke samun aiki a gwamnati.

Tun farko a jawabin Mai taimaka wa Gwamnan Jihar kan Harkokin Nakasassu, Alhaji Musa Awe, ya ce a kokarin da gwamnatin jihar karkarshin jagorancin Abdullahi Sule ke yi na inganta harkokin nakasassu a jihar, tuni Gwamnan ya kafa wani kwamiti da zai bincika ya gano matsalolin da suke fuskanta a makarantunsu da wadanda ba su samu damar karatu ba don tallafa musu a wannan bangare.

Shugaban Jami’ar, Farfesa Suleiman Mohammed, wanda ya yi jawabi ta bakin Mataimakinsa (Harkokin Ilimi), Farfesa Peter Osuorji, ya ce Hukumar Gudanarwar Jami’ar tana iya kokarinta wajen taimaka wa nakasassun a fannin karatunsu, inda ya ce a kusan dukkan tsare-tsare da dokokinta takan yi la’akari da jin dadinsu a jami’ar.