✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Daliban Zamfara a Jami’ar Jihar Sakkwato na neman agaji

Yau ina tafe da wata matsala ce da daliban Jihar Zamfara masu karatu a Jami’ar Jihar Sakkwato ke fama da ita. Wannan matsala kuwa ta…

Yau ina tafe da wata matsala ce da daliban Jihar Zamfara masu karatu a Jami’ar Jihar Sakkwato ke fama da ita.

Wannan matsala kuwa ta shafi dubban dalibai ’yan asalin Jihar Zamfara,  matsalar ita ce ta karin kudin makatanta da Gwamnatin Jihar Sakkwato ta yi daga Naira dubu 47 zuwa Naira dubu 98.

Mafi yawan wadanda wannan lamarin ya shafa ’ya’yan talakawa ne ’yan Rabbana Ka wadata mu. Wannan matsalar ta samo asali ne daga bara, inda Gwamnatin Jihar Sakkwato ta fita daga cikin Kungiyar da ake cewa SOKEZA wato Kungiyar Al’ummar Sakkwato da Kebbi da Zamfara,  duk da cewa ita ce uwa ga wadannan jihohi.

A bara wadannan bayin Allah dalibai sun yi iya kokarinsu wajen ganin  Gwamnatin Jihar Zamfara ta shiga cikin lamarin, amma saboda rikicin siyasa da ya dauki hankalin gwamnatin ba ta samu damar yin wani abu ba har ta sauka.

Daga karshe wadansu ’ya’yan talakawa sai dai suka bar karatun, duk da cewa sun yi nisa, wadansu na aji hudu wadansu uku wadansu aji biyu wadansu ma an ba su gurbin karatun ke nan amma tilas suka fasa, dalilin rashin abin da za su biya,

Sanin kowa ne cewa ilimin shi ne ginshikin rayuwar dan Adam, idan damar samun ilimi ta kufce masa to tabbass sai dai  ya fada cikin  wata hanyar ko dai mai kyau ko sabanin haka wanda ba a fatar haka.

A baya ’yan Jihar Zamfara masu karatu a Jami’ar Jihar Sakkwato suna sababbin dalibai na biyan Naira dubu 47, sai kuma sauran dalibai na biyan Naira dubu 42,  amma yanzu sababbin dalibai na biyan wuri na gugar wuri har Naira dubu 110 sauran dalibai kuma Naira dubu 98!

A madadin dukkan daliban Jihar Zamfara da ke karatu a Jami’ar Jihar Sakkwato muna mika kokon bararmu ga gwamnatin  Dokta Bello Matawalle a kan ta duba wannan matsalar ta share mana hawaye.

Ibrahim Rabilu Tsafe dan asalin Jihar Zamfara ne da ke dalibta a Jami’ar Jihar Sakkwato za a iya tuntubarsa ta 07064282182