Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Dalibi ya sa allura a cikin mafitsararsa don ya farka ya yi karatu da dare

Hoton allurar da yaron ya saka a cikin mafitsararsa

Wani yaro da aka sakaya sunansa mai kimanin shekara 12 daga garin Shandi, a Gundumar Dian da ke kasar China, ya fahimci cewa dabarar da zai iya yi wajen ya farka daga barci don ya samu damar yin karatu cikin dare da sauran ayyukan makaranta da aka ba shi ya yi a gida shi ya sa ya samu allura mai tsawon santimita 10 ya zura a cikin mafitsararsa, a cewarsa wannan ita ce kadai mafita.

Shi dai wannan matashi ya damu matuka a kan ya farka game da abin da zai sa shi ya farka daga barci don ya yi nazarin karatunsa, wannan yaro ya yi abin da ya bai wa kowa mamaki saboda ganin yadda ya daukar wa kakarsa allurar da ake amfani da ita wajen cire duk wani abu da ya makale a jikin mutum sannan ya tura ta a cikin mafitsararsa. Sai dai duk da haka wannan dabara ba taimaka masa ya farka daga barcin ba. A cewarsa mahaifiyarsa ce ta sa ya aikata haka, wannan abu na da matukar wahala wajen fitar da ita cikin sauki, kuma wannan ya sa ba ya iya tafiya kamar yadda ya dace sakamakon radadin allurar da ya zura a jikinsa.

ADVERTISEMENT

Mahaifiyar matashin ce ta fara fahimtar abin da yake faruwa, saboda ganin yanayinsa ya sauya da yadda ta saba ganinsa, tun a ranar 25 ga Yuli, yaron ya ki zuwa a wajen motsa jikin da ya saba. Wannan ya sa mahaifiyar yaron ta yanke shawarar fita da danta wajen motsa jiki saboda kwanakin da ya shafe bai yi ba, daga nan ne ta fahimci cewa yana tafiya ne a hankali ba kamar yadda ya saba yi ba.

Kafar sadarwa ta Asia One ta ce, mahaifiyar yaron ne ta yi sanadiyar sanya yaron ya aikata hakan cikin fushi, a cewar yaron wannan hanya ce za ta ba shi damar farkawa cikin dare ya yi nazarin karatunsa.

ADVERTISEMENT

Yaron, ya ce “A duk lokacin da zai yi nazarin karatunsa sai ya fara barci, na yi abin da nake tunanin zai iya hana ni barci, don haka na zura allura a cikin mafitsarata.”

Bayan mahaifiyar yaron ta ji abin da danta ya aikata ta razana sosai, sai ta kai shi wani asibiti mafi kusa, inda wani likita mai suna Wang Shengding ya yi masa tiyata ya ciro allura daga cikin mafitsararsa daidai kusa da abin da ke rike masa fitsari, wanda hakan zai iya haifar masa da wani ciwo na daban ko ya toshe masa wata hanyar jini.

Wang, ya kara da cewa, an yi nasarar ciro allurar mai tsawon santimita 10 da take mallakin kakarsa ce ba tare da an ji masa rauni ba.

Wannan rahoto wadansu dalibai da dama nata tafka muhawara, inda wadansu ke kallon abin da yaron ya aikata a matsayin karatun cike gibin da bai yi ba a baya don haka ya fusata ya dage ya tabbatar da ya cika burinsa. A wani bangare kuma wadansu na kallon abin a matsayin jahilci da kuruciya ce tasa ya aikata haka.