✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dalibin Jami’ar FUD ya zama zakara a kasar China

Wani dalibin Jami’ar Tarayya da ke Dutse (FUD) a Jihar Jigawa, Malam Ahmad Baba ya zama zakara a gasar tsabtar muhalli ta jami’o’in duniya da…

Wani dalibin Jami’ar Tarayya da ke Dutse (FUD) a Jihar Jigawa, Malam Ahmad Baba ya zama zakara a gasar tsabtar muhalli ta jami’o’in duniya da aka gudanar a kasar China.

Gasar wacce ta tattaro daliban da suka fi nuna kwazo daga sassan kula da muhalli na jami’o’in sassan duniya (Enbironmental Studies) kimanin 95 ne suka fafata a kasar China, inda Malam Ahmad Baba ya zama zakara.

Shugabar Jami’ar  FUD ce Farfesa Fatima Batula ta sanar da haka a bikin yaye dalibai 582 da aka gudanar a ranar Asabar da ta wuce a harabar jami’ar.

Ta ce dalibi Ahmad Baba ya zama gwarzo ne bayan ya doke dalibai 94 da suka fafata a gasar wadanda suka fito daga jami’o’i 95 na sassan duniya.

Shugabar ta kara da cewa wannan nasara da Ahmad Baba ya samu, tuni jami’ar ta yanke shawarar ba shi aiki kai-tsaye da zarar ya dawo Najeriya.

Ta ce Jami’ar FUD ta kulla yarjejeniya da wasu manyan tsangayu da ke jami’o’i daban-daban na duniya da suka hada da Jami’ar  Dakota da Jami’ar Morgan da suke Amurka da kuma Jami’ar International Islamic Unibersity da ke Kalentan a kasar Iran da sauransu.

Ta ce dalibai 839 ne suka kammala karatunsu a jami’ar ciki har da wadanda suka yi karatu a matakin gaba da digiri wato Post Graduate a tsakanin shekarar 2017 zuwa 2018.

Ta ce daga cikin wannan adadi dalibai 14 ne suka samu shaidar karatu mafi daraja wato First Class yayin da dalibai 222 suka samu nasarar fita da sakamako mai daraja ta biyu (Second Class Upper) sai dalibai 222 suka fita da sakamako mai daraja ta biyu (Second Class Lower).  Sai kuma dalibai 70 da suka fita da sakamako mai daraja na uku.

Ta ce wannan shi ne karo na farko da jami’ar ta yaye daliban da suka fi nuna kwazo tunda aka kirkiro jami’ar da hakan ya nuna ana samun ci gaba.

Jami’ar FUD dai Gwamnatin Tarayya a zamanin Goodluck Jonathan ne ta kirkiro a shekarar 2011 tare da wasu jami’o’i takwas.