✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dalilan da ke hana ’yan Arewa haskawa a kwallon kafar Najeriya

Kullum sai kara samun matasa da suka iya taka leda a Arewacin Najeriya ake yi, amma yawancinsu gwanancewar tasu kan kare ne a kwallon layi…

Kullum sai kara samun matasa da suka iya taka leda a Arewacin Najeriya ake yi, amma yawancinsu gwanancewar tasu kan kare ne a kwallon layi ko kuma su yi tashe na dan lokaci.

Daga zamanin da ake kiran kungiye kwallon kafa ta Najeriya da Green Eagles zuwa yanzu da ta koma Super Eagles, yawan ’yan Arewa a cikin tawagar sai kara raguwa yake yi.

Idan ana batun zaratan ’yan kwallon Najeriya, tun a da zuwa yanzu, ’yan asalin Arewa wadanda akalla suka buga Gasar Cin Kofin Afirka ba su wuce tara ba kacal.

An yi dan wasa Anas Ahmad da Shafiu Mohammed wadanda ’yan wasan fitacciyar tsohuwar kungiyar kwallon kafa ta Racca Rovers ce ta jihar Kano, wadda ta yi fice sosai a tsakanin shakarun 1978 zuwa sama.

Anas ya buga Gasar Cin Kofin Nahiyar Afirka ta shekarar 1978, shi kuma Shafiu ya buga ta shekarar 1980, inda Najeriya ta lashe gasar a karon farko.

Shafiu yana cikin wadanda suka lashe gasar a matsayin dan wasan gaba.

Wadanda aka fi sani

A Gasar Cin Kofin Nahiyar Afirka ta shekarar 1984, an samu ’yan asalin Arewa biyu da suka buga —Ibrahim Mohammed da Ali Baba. Sai Abdul Aminu da ya buga gasar a 1990 da 1992.

Akwai kuma wadanda aka fi sani, irinsu Garba Lawal wanda ya fi kowane dan Arewa fice da dadewa yana jan zarensa. Garba Lawal ya buga Gasar Cin Kofin Afirka a 2000 da 2002 da 2004 da 2006.

Sannan akwai ai Tijjani Babangida wanda ya buga ta 2000 da 2002, sai Sani Kaita da ya buga ta 2006 da 2010.

Sauran ’yan wasa irinsu Dahiru Sadi da Sale Lato da sauransu sun taba buga wa Najeriya, amma ba su taba zuwa Gasar Cin Kofin Afirka ba, ballantana Kofin Duniya.

A jerin gasannin da Najeriya ta lashe na Cin Kofin Afirka, sau daya ne kacal, ta shekarar 1980, aka samu dan asalin Arewa a ciki, wato Shefiu Mohammed.

A yanzu haka, Shehu Abdullahi, wanda yake buga wa kungiyar Bursaspor ta Turkiyya, wanda kuma dan jihar Sakkwato ne kadai dan asalin Arewa, idan aka cire kyaftin din Super Eagles na yanzu, Ahmed Musa, wanda aka ce yana da alaka ne da jihar Edo, duk da cewa da yawa suna cewa dan asalin Jos ne a jihar Filato.

Wani kaulin kuma na cewa mahaifinsa Ahmed Musa din dan Kano ne, mahaifiyarsa ce tababar kasancewarta ’yar Jos din ce ko Edo. Bari dai mu bar wannan magana mu karasa batun da muka dauko.

‘Yan kasa da 17 da 20

Idan ana batun matasan ’yan kwallo, musamman duba da yadda ’yan asalin Arewa ke taka leda a gasannin ‘yan kasa da shekara 17 da ‘yan kasa da shekara 20 da ma Olympic, za a ga cewa akwai kwarewa a tattare da su, amma kuma sai su kasa kai bantensu.

Akwai matasan ’yan kwallo da suka buga gasar kasa da shekara 17 da 20 da Olympic irinsu Alhaji Gero da Sadiq Umar da Usman Mohammed da Aminu Umar da Musa Mohammed da Lukman Abdulkareem da Rabiu Ali da Musa Yahaya da sauransu.

Musamman Musa Mohammed wanda har kyaftin ya yi, da kuma Sadiq Umar wanda ya zura kwallo hudu a gasar Olympic ta shekarar 2016, har ya kasance dan Najeriya da ya fi cin kwallaye.


Dalilan da ke dakile ’yan wasan Arewa

Rashin manyan ejan

A wata tattaunawa da ya da Daily Trust, tsohon dan wasan Najeriya Dahiru Sadi ya ce akwai matsalar rashin ejan da za su zakulo ’yan wasa a lungu da sakon Arewa.

“Misali, ejan a Kudu zai iya kashe wa matashin dan kwallo kudi har zuwa Naira miliyan daya ko biyu domin ganin yaron ya samu shiga.

“Amma a Arewa saboda N100,000 kawai za a iya cire yaro, saboda ejan din ba ya so ya biya, su ma iyayensa ba za su biya ba ko da suna da kudin.

“Ba su san cewa kasuwanci ba ne mai kyau harkar. ’Yan Kudu sun fi wayewa sosai a wannan bangaren”, inji Dahiru Sadi.

A lokuta da dama idan manyan ejan din kwallo suka zo daga kasashen waje su kan taru ne a jihohin Kudu, ko kuma a Abuja, inda ake buga wasannin gwaji domin daukar ’yan kwallo a fitar da su kasashen waje.

Amma sau da tari ‘yan wasa daga jihohin Katsina da Kano da Sakkwato da Zamfara ba za su iya zuwa ba, watakila saboda rashin kudi.

Rashin zuba jari

Wani lamarin da ke kawo wa harkar kwallon kafa tarnaki a Arewa shi ne yadda attajiran yankin ba su fiye zuba jari a harkar, ko da yake yanzu sun fara farkawa.

A Kudu akwai manyan masu kudi da ke sa kudadensu su bude kungiyoyin kwallon kafa, suna daukar nauyin matasa suna buga kwallon.

Suna ciyar da ’yan kwallon, su ba su kayan wasa da lura da lafiyarsu. Amma da wuya ka samu irin hakan a Arewa.

Halin ko-in-kula

A Kudancin Najeriya, matasa da dama sun dauki kwallon kafa ne a matsayin sana’a, kuma iyayensu sun amince da hakan.

Amma a Arewa yawanci matasan sukan yi kwallo ne a boye, kasancewar yawanci iyayensu ba sa so.

Hakan ke sa ko da an bukaci a yi tafiya da yawo domin wasannin gwaji, ba zai iya fada ba a gida.

Ko kuma idan masu horar da su sun zo har sun fada wa iyayen, sai iyayen su ki amincewa.

Irin wannan ma yakan hana manyan ejan zuwa saboda tsoron kada su kashe kudi, a hana yaron tafiya.

Dahiru Sadi ya ce, “Hausawanmu suna da halin ko-in-kula, inda ba sa nuna damuwa da dagiya a harkar.

“Misali, na taba kai wani matashin dan kwallo kungiyar Lobi Stars ta Makurdi. Har an kammala komai jira kawai ake yi a fara wasanni, kawai muka hadu da shi ya dawo Kaduna.

“Da na tambaye shi sai ya ce min mahaifiyarsa ce take gini, shi ne ta ce masa ya dawo ya lura da aikin”.

Shin za ta sake zani?

Lura da yadda lamarin yake a yanzu, inda mutanen Arewa su kan yi tsokacin cewa ba sa ganin ’yan yankinsu, da kuma ganin yadda aka fara samun sauyi a harkokin kasuwancin ’yan kwallo a Afirka, za a iya cewa da alama gaba za ta fi baya kyau.

Akwai zaratan ’yan kwallo da dama da yanzu suke jan zarensu a kasashen Turai, kuma idan suka ci gaba a haka, nan gaba kadan za a gan su a Super Eagles.

‘Yan wasan Super Eagles lokacin suna Green Eagles a shekarar 1980 lokacin da Najeriya ta lashe Kofin Afirka na farko ciki har da Shefiu Mohammed (Hoto: Independent.ng)