Aminiya

Dalilan da na kafa gidan rediyon Fulatanci – Usman S. Usman

Malam Usman Shehu Usman

Usman Shehu Usman, gogaggen dan jarida ne da ya shafe shekaru da dama a aikin; a yanzu shi ne Babban Editan Sashen Hausa na Rediyon Deutsche Welle da ke kasar Jamus. A kwanakin baya ya kawo ziyara a Najeriya; inda Aminiya ta tattauna da shi game da dalilansa na kafa gidan rediyo mai watsa shirye-shirye a gajeren zango cikin harshen Fulatanci mai suna Koode Radio International:

Mene ne dalilinka na kafa Koode Radio International?

A gaskiya dalilan da yawa, amma manyansu guda hudu ne. Na farko shi ne yadda na ga manyan gidajen rediyo na duniya ba sa yada labarai ta harshen Fulatanci; wanda kuma babban harshe ne a duniya. Alhali da akwai wasu kananan harsuna da kafofin labaran ke watsa labarai da su kamar BBC da DW da BOA da RFI suke yi, kuma kasashen da harsunan suke ma ba su kai Najeriya ba. A sanin da na yi wa harkar watsa labarai, da zarar wata kafa ta fara watsa shirye-shirye da wani harshe, to sauran ma za su bi sahu. Kuma mun ma cimma nasara, saboda RFI ya fara watsa labarai da harshen, bayan sun ga muna watsawa.

Na biyu shi ne karfafa harshen Fulatanci. Duk harshen da ba a rubuta shi, ba a watsa shi to ba zai rayu ba. Na uku shi ne, ba wai mu karfafa harshen a rediyo kawai ba; a’a so muke mu yada harshen Fulatanci ta hanyar koyar da shi a cibiyar koyar da aikin jarida da makarantu, kuma alhamdulillahi, har mun samu  takardun makarantar. Mun kuma kammala tuntubar farfesoshi akalla 10 za su yi aikin tsara manhajar koyar da harshen, zuwa karshen shekarar nan, insha Allah, kuma Koode Radio ne za ta dauki nauyin wannan. Na hudu kuma shi ne so muke mu kare yadda ake juya labaran da suka shafi Fulani. Idan munanan labarai sun shafi Fulani kafafen labarai na kambama batun; ba wai muna cewa kada a fadi laifin Fulani ba ne, in sun yi laifi a fito a fada; amma dai su ma ya kamata a fito a kare hakkinsu. Sai kuma dalili na baya-bayan nan na fadace-fadacen manoma da Fulani makiyaya. Za mu mai da hankali wajen ilimantar da Fulanin.

Ka yi batun kirkiro da makarantar koyar da Fulatanci; ko za ka yi karin haske a kai?

ADVERTISEMENT

Sunan makarantar Koode Media Academy, kuma tana da mazauni a Abuja. Kuma za ta rika koyar da aikin jarida da kuma harshen Fulatanci. In Allah Ya yadda za mu kuma bullo da koyar da harsunan Jamusanci da Faransanci a Koode Media Academy. Amma dai babban abin da muka fi bai wa fifiko a yanzu shi ne farfadowa da koyar da harshen Fulatanci da kuma aikin jarida.

Ba ka ganin kamar an bar ku a baya, ganin yadda yanzu an koma watsa labarai ta hanyar zamani (digital), amma ku kuna kokarin kafa rediyo?

Gaskiya ne duniya tana canjawa. Misali yanzu a inda nake aiki a Jamus, kusan sauran sassan sun daina amafani da Frekuency wajen watsa shirye-shirye, sun koma hanyar Satelite da kuma abokan huldarsu. Mu sashen Hausa na DW ne kawai muke yada shiri ta dogon zango. Babu makara ko daya. Amma mun sanya rigar zamani mu ma, don muna watsa shirinmu ta hanyar Tunein da WhatsApp groups na Fulanin duniya kuma babbar hanyar da aka fi sauraronmu ita ce ta Intanet. Muna amfani da shafukan Facebook da na WhatsApp. Misali yanzu wadansu Fulani a kasar Kanada har suna tambaya idan ba a dora shirin Koode a kafar WhatsApp ba, sune cewa yaya har yanzu ba mu ji labaran Koode Radio ba. Akwai Fulani sosai a Turai da Kanada da Amurka.

Kuma Bafulatani shi ne yake kan gaba wajen amfani da rediyo. In ka lura har yanzu su kansu manyan kafafen labaran har yanzu suna kashe kudi sosai wajen inganta kafar watsa labaran rediyo. Akwai dimbin Fulanin da ke sauraranmu ta rediyon, kuma rediyo shi ne kafa mafi sauki wajen yada shiri; ko a dokar daji kake za ka iya sauraron shiri ta rediyo idan ka saka batura biyu kawai. Kuma kashi mafi yawa na masu sauraron labaran Hausa, Fulani ne, kuma muna kan turba mai kyau.

Wane kalubale ka fuskanta wajen kafa  Koode Radio International?

Babban shi ne wajen samun ofishin gidan rediyon, sakamakon rashin isassun kudi. Da farko mun so mu yi abin a hankali, amma sakamakon rigingimun da suke faruwa ya sa muka gaggauta fara watsa shiri a Koode. Akwai kuma matsalar samun ma’aikatan da za su yi aikin. Tunda ba kowa ba ne zai iya aikin labarai ta harshen Fulatancin. Mun sha wahala wajen samun Fulanin da suka iya aikin rediyon kuma suka iya harshen. Kamar harshen Hausa, ba kowane Bahaushe ne zai iya karanta maka labarai ba. Haka yake ga Fulantancin. Saboda harshen da ake yadawa a rediyo daban yake da wanda ake magana da shi a kan titi.

Wadanne shirye-shirye ne Koode Radio take gabatarwa?

Akwai shirin siyasar duniya, da ke tattauna ababuwan da suke faruwa a duniya da shirin da ke duba al’adun Fulani da noma da kiwo da kuma wanda ke kula harkar mata da shirin kiwon lafiya. Sakamakon yadda aka mayar da Fulani kurar-baya a fagen kiwon lafiya a Najeriya; ta yadda za ka ga a wuraren zamansu babu ko asibitin sha-ka-tafi. Muna duba harkar tattalin arzikin da ta shafi yadda za a iya kiwon shanu ta hanyar zamani su bada riba da sauransu. Sa’annan akwai shirin da muka bullo da shi a baya-bayan nan, shi ne na tarihin Shehu Usman Dan Fodiyo. Mun dauko tarihin nasa daga tushen haihuwarsa har zuwa yadda ya yi ilimi ya kuma jagoranci jihadi da kuma kafa dauloli da sauransu. Za mu kuma bi dukkan masarautun da ya bai wa tuta don jin yadda suke. Sa’annan muna da shiri na musamman a kan matasa manyan gobe, wanda zai wayar musu da kai game da matsalolinsu. Akwai kuma shirin kade-kaden zamani da tsofaffin wakoki na Fulani.

Ko akwai wata hulda ko hadin gwiwa da kuke da ita da wata kafar labarai a nan Najeriya ko duniya?

Akwai, don Koode Radio shi ne kadai mamba a nan Najeriya da ma yammacin Afirka a wata hukuma ta duniya da ke kula da gidajen rediyo masu watsa shiri ta gajeren zango. An zabe shi ne a wani taron da aka gudanar a watan Janairun bana a Tunisiya. Kuma mun yi wani taro a kan haka a birnin Buenos Aires na Ajantina, inda ake duba matsalolin da suke samuwa a tsakanin masu watsa shirye-shirye ta gajeren zango. Kuma tashar DW ta kawo wata na’ura ta wucin-gadi domin gwajin yadda za a fahimci ko ana sauraron tashar rediyo ta gajeren zango yadda ya kamata ko a’a. Mun kuma kulla kawance da wani kamfanin da ya fi kowane sayar da gidajen rediyo da ke kasar Holland; za su rika horar da injiniyoyinmu yadda za su koya don su ma su koyar da wadansu. Ma’aikatanmu za su iya gyara duk wasu matsaloli da suka shafi yada shirin rediyo ta gajeren zango. Kuma a halin yanzu mun tsara da wannan kamfanin cewa za mu tura daya daga cikin ma’aikatanmu zuwa Holland inda zai je ya fara samun horo; kuma da zarar ya kammala, wani ma zai tafi.

Wace irin gogayya kuke fuskanta daga kafofin labarai da suka jima a fagen yada labaran rediyo, kamar su DW da BBC da BOA da kuma RFI?

Babu wani kalubale ko gogayya da muke fuskanta daga gare su. Ba ma gogayya da kowa, sakamakon mu ta harshen Fulatanci kawai muke yada shirye-shiryenmu. Mu kadai muke yada labarai ta harshen, ba wai Fulantancin a matsayin wani harshe na daban ba; a’a duk shirye-shiryenmu a cikin harshen ne suka ta’allaka. Su kansu kowa kokari yake ya bullo da shirye-shiryen da za su burge masu sauraronsu. Bil hasali ma akwai kyakkyawar hulda tsakaninmu da su, tunda har sun ma fara tuntubar yadda za su yi hulda da mu.

Kwanaki Hukumar Ilimin Makiyaya (NCNE) ta sanar da yunkurinta na kafa gidan rediyon makiyaya; ko akwai wata alaka tsakaninku?

Lallai hakan abu ne mai kyau; amma ba mu da wata alaka da su, sai dai kawai muna yada shirinmu ta harshen Fulantanci ne kuma su ma za su yada ta harshen. Amma ba ni da masaniya a kan rediyon, kuma ina maraba da shi.

A ina kake fatan ganin tashar Koode Radio International, nan da shekaru masu zuwa?

Insha Allahu Rediyon Koode zai zama babbar cibiya ta sauraren rediyo da ke watsa shirye-shirye da harshen Fulantanci a duniya baki daya. Sa’annan ina da yakinin cikin shekaru masu zuwa Rediyon Koode zai kasance dandali na wadanda suke da niyyar koyon Fulatanci. Sa’annan ina fata zai zama wata babbar kafa da Bafulatani a duniya zai rika alfahari da ita domin kawo zaman lafiya da sasanta rigingimun da suka shafi Fulani insha Allahu.

Kasancewarka Bafulatani, me za ka ce game da ce-ce-ku-cen da ake yi kan samar da rugagen kiwo ga Fulani makiyaya a kasar nan?

Matsalar daga Arewa take. Ra’ayina shi ne abin yana da kyau; kiwon zamani dole ne a shiga, saboda yadda duniyar take sauyawa. Wasu gwamnatocin jihohin Arewa su ke taimakawa wajen datse ko kuma sare burtalolin kiwon a yankin. Matsalar tamu ce mu ’yan Arewa. Gwamnatin Tarayya ba ta damu da harkar kiwon dabbobi ba kwata-kwata, saboda ba ta ware wani kaso komai kadan dinsa ga sha’anin kiwon shanu a Najeriya. Amma hatta injin janareta  a Fadar Shugaban Kasa ana tanada masa kudi a kasafin kudin kasa; amma ba ruwanta da abin da ya shafi matsaloli da wuraren kiwon shanu ko dabbobi da magungunan dabbobin a kasa. A bangaren Ma’aikatar Noma din ma wani, dan sashe ne kawai ta samar na bitinare.