Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Dalilan da suka sa Real Madrid ke shan wahala

‘Yan wasan Real Madrid

A makoni biyu da suka gabata ne aka yi waje da kungiyar Real Madrid a gasar Kofin Zakarun Turai bayan Ajada ta biyo ta har gida ta dkoke ta, duk da cewa ta kasance tana cin Karan ta ba babbaka a gasar tun 2016.

Cikin mako daya an rusa wa Real Madrid burin lashe kofuna a kakar 2018/2019 bayan Barcelona ta fitar da ita daga gasar Copa del Rey kuma ta kara ba ta tazara a La liga kafin Ajad ta fitar da ita daga gasar Zakarun Turai a Bernabeu.

ADVERTISEMENT

Real ta lashe kofin gasar zakarun Turai sau uku a jere, sau hudu kuma cikin shekara biyar.

Karon farko da Real Madrid ta gaza tsallaka wa zuwa zagayen dab da kusa da karshe ke nan tun a shekarar 2010.

ADVERTISEMENT

Akwai wasu dalilai da ake ganin suka janyo wa Real Madrid shiga wannan halin kamar yadda BBC ta rawaito, kuma sun hada:

Shekarun ‘yan wasa

Ana ganin Gareth Bale da Benzema sun kai karshen ganiyarsu a Madrid, duk da Benzema yana kokarin cin kwallaye bayan tafiyar Ronaldo.

’Yan wasa kamar Luka Modric da Isco da Marcelo ba su taka rawar da suka saba takawa ba kamar a shekarun baya da suka taimaka wa Real Madrid lashe kofin Zakarun Turai sau uku a jere.

Shekarun manyan ’yan wasan ya yi tasiri, kamar Luka Modric shekararsa 33, Sergio Ramos shekara 32, Toni Kroos shekara 29 yayin da kuma Karim Benzema ke da shekara 31.

Ana ganin tauraruwar Isco da Marcelo ta disashe sabanin baya, duk da cewa ’yan wasan na ikirarin cewa babu wani abin da ya sauya.

Babu wani babban dan wasa masanin raga da zai iya farfado da kwazo da karfin Madrid na cin kwallaye.

Ana ganin Real Madrid na bukatar zubin sabbin ’yan wasa domin farfado da martabar kungiyar.

Rashin Ronaldo

Yadda aka fitar da Real Madrid tun a zagayen ’yan 16 a Zakarun Turai ya nuna kungiyar ba ta iya lashe kofin sai da Ronaldo.

Wannan ce kuma Shekarar farko da Real Madrid ta fara rayuwa ba Ronaldo, bayan ya koma taka leda a Jubentus a kakar da ta gabata.

Karon farko ke nan tun 2015 da aka fitar da Real Madrid a gasar Zakarun Turai.

Masu sharhi da dama na ganin rashin Ronaldo ya yi tasiri sosai ga rashin nasarorin da Madrid ke fuskanta a kakar bana. Tun daga fatarar cin kwallaye zuwa ga nasarar lashe wasanni.

Kuma har yanzu Real Madrid ta gaza maye gurbinsa da wani fitaccen dan wasa.

A bana Benzema ne dan wasan da ya fi ci wa Real Madrid kwallaye a gasar Zakarun Turai inda ya ci kwallo hudu, kuma yake bayan Robert Lewandowski na Bayern Munich da ke da kwallo takwas da kuma Lionel Messi da ke da shida.

Sauyin Koci

Tun tafiyar Zinedine Zidane abubuwa suka dagule wa Real Madrid. Zidane ne ya lashe wa Real Madrid kofin zakarun Turai sau uku a jere, tarihin da babu wani koci da ya taba kafawa a Turai.

A karshen kakar 2017/2018 ne Zidane ya ajiye aikinsa na horar da ’yan wasan Real Madrid, watanni 10 kuma yanzu bayan tafiyarsa abubuwa sun sauya wa kungiyar.

Sauye-sauyen koci a kaka daya wasu yana cikin abin da ya jefa Real Madrid cikin halin da take ciki a yanzu.

A watan Nuwamba ne Santiago Solari ya karbi aikin horar da Real Madrid bayan korar Julen Lopetegui.

Duk da Solari ya yi nasara a wasanninsa na farko, amma yadda babbar abokiyar hamayyarsu Barcelona ta bi Real Madrid har gida Santiago Bernabeu ta doke ta a Copa del Ray da La Liga ya nuna ba zai iya ba.

Kocin dai ya ci gaba da tafiyar da Real Madrid tare da zubin ’yan wasan da ya gada ba tare wani sabon zubi ba.

Ko da yake wasu na ganin ya yi kokari yadda ya tada matasan ’yan wasa kamar Binicius Junior da ake ganin zai gaji Ronaldo da kuma wasu matasa kamar Albaro Odriozola da Sergio Reguilon da Dani Ceballos da kuma Marcos Llorente.

Wasu na ganin cewa ’yan wasan ba wai ba sa kokari ba ne, kawai dai kwarewa suke bukata daga koci.