✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dalilan hani a kan shaye-shayen magunguna barkatai ga masu juna biyu

Wai me ke sa wa a hana mata masu juna biyu shaye-shayen magunguna barkatai ne? Daga Sani Umar Malumfashi Amsa: Tsoron illar da maganin kan…

Wai me ke sa wa a hana mata masu juna biyu shaye-shayen magunguna barkatai ne?

Daga Sani Umar Malumfashi

Amsa: Tsoron illar da maganin kan yi ga ban da ke ciki ake jiye wa mata masu juna biyu. Shi ya sa ake ji ma’aikatan lafiya na yawan gargabi a guji shaye-shayen magunguna barkatai yayin da aka samu juna biyu, musamman a watannin ciki uku na farko, lokacin da ban tayi ke zama jariri. Ba magungunan asibiti ba har na gida akwai wabanda za su iya yi wa ban tayi illa. Wasu ma sinadaran masu yi wa ban ciki illa ba a magunguna ba ne, kayan nishabi ne irin su ruwan barasa da taba da wiwi da hodar iblis da shayin kofi da yawa, duk sukan iya sa irin wannan illa ga ban ciki. Wasu ma a abinci ne kamar wabanda ba a dafa sosai ba, misali banyen kwai. Wasu ma a allurar rigakafi suke samun matsala. Shi ya sa ba a yi wa masu juna biyu allurar rigakafi masu bauke da kwayoyin cuta masu rai.

To wani ya ce takamaimai wabanne irin illoli wabannan magunguna da abubuwa kan yi wa ban tayi? Abubuwan sun bambanta, tun daga nakasa ta jiki kamar rashin yatsu, hannaye, kafafu ko idanu, ko wata dai jirkitacciyar sifa, ko kuma magungunan su sa barin jaririn gaba baya ya shanye.

A tsakanin shekarun 1958 zuwa 1960 a kasashen Turai da Amurka an haifi dubban yara marasa kafafu da hannaye, bayan iyayensu sun yi amfani da wasu kwayoyin magunguna da ke sa barci da kwantar da amai. Rabin wabannan jarirai mutuwa suka yi bayan an haife su. Bayan an zurfafa bincike ne aka gano cewa wannan nakasa da ta auku a wabannan dubban jarirai sanadiyyar wabancan kwayoyin ne. Da ma dai an riga an san akwai kwayoyin magungunan amma ba a taba ganin abu mai girman wannan ba, wanda aka danganta da wata kwaya kai-tsaye sai a wancan lokaci. To tun daga wancan lokaci ne aka karfafa dokokin shaye-shayen magunguna barkatai ga masu juna biyu. Wabannan matakai ne suka sa a yanzu akwai kundin magungunan da ma’aikatan lafiya ba sa ba da su ga mai juna biyu domin an tabbatar zai yi wa ban da ke ciki illa, (mai juna biyu za ta ga an rubuta ‘contra-indicated in pregnancy’ a jikin kwalin maganin) akwai kuma wabanda akan ce a yi taka-tsantsan da amfani da su idan ana da juna biyu (su kuma za a ga an rubuta musu ‘use with caution during pregnancy’ a jikin kwalin). To ka ji dalilan da ya sa ake hana mata shan magunguna barkatai a lokutan da suke da juna biyu.

Sai dai kuma a hannu guda fa akwai magunguna da sinadarai, wabanda idan babu su a jikin mace a lokacin da ta samu juna biyu shi ma cikin yana cikin habarin barewa ko ya samu nakasa ta jiki, kamar irin su rashin dubura, yankakken baya da tsagaggen lebe. Wabannan matsaloli, da sauran ire-irensu, su kuma duk an tabbatar cewa idan mace ba ta shan kwayoyin folic acid yayin da ta samu juna biyu, jaririnta zai iya samunsu.