✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dalilin da ba za mu daina muzahara ba – ’Yan Shi’a

Zanga-zangar da ’yan kungiyar IMN ta mabiya Shi’a ke ci gaba da yi a Abuja don neman a saki jagoransu, Sheikh Ibrahim Zakzaky ta zafafa…

Zanga-zangar da ’yan kungiyar IMN ta mabiya Shi’a ke ci gaba da yi a Abuja don neman a saki jagoransu, Sheikh Ibrahim Zakzaky ta zafafa a wannan mako, inda a ranar Litinin da ta gabata ta kai ga asarar rayuka 6 daga bangaren mabiyan da kuma Mataimakin Kwamshinan ’Yan  sandan Abuja, mai kula da Gudanar da Ayyuka Usman M.K. Umar da kuma wani dan jarida mai aikin hidimar kasa a Gidan Talabijin na Channels.

Zanga-zangar wadda ’yan Kungiyar IMN da ’yan sanda suka ce adadinsu ya kai 3000 , ta kunshi matasa da yara maza da mata kuma ta faro ne daga Wuse da misalin karfe 12 na rana suka nufi Sakatariyar Tarayya, kamar yadda bayanai suka nuna. Har wa yau ta haddasa asarar dukiya, musamman motoci, baya ga wadanda suka tsira da raunuka.

A sanarwar da ’yan sanda suka fitar ta hannun Kakakinsu na Kasa DCP Frank Mba, ya ce masu zanga-zangar sun kai wa ’yan sanda hari a kusa da Sakatariyar Tarayya a yunkurinsu ’yan sandan na hana su isa wajen, inda a sanadiyyar haka DCP Usman Umar ya rasa ransa.

’Yan sandan sun tabbatar da rasuwar dan jarida mai suna Precious Owolabi a yayin artabunsu da ’yan Shi’ar, sai kuma wasu ’yan sandan 2 masu mukamin ASP da suka samu raunuka.

Daga bangaren masu zanga-zangar, sun sanar da cewa kimanin mutum 30 sun samu raunuka, wadansu daga cikinsu na cikin mutum sama da 50 da ’yan sanda suka ce sun kama kan zargin hannu a tashin hankali.

Sun ce ’yan sandan sun dauko su ne daga gadajensu a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Abuja da ke Gwagwalada, inda aka garzaya da su don yi masu jinya bayan sun tsira da raunuka.

’Yan sanda sun ce za su gurfanar da wadanda suka kama a gaban kotu da zarar sun gama bincike.

A ranar Talatar da ta gabata ma ’yan kungiyar IMN sun sake gudanar da wata zanga-zangar a Unguwar Wuse 2 a Abuja. Sai dai tun a farkon taruwarsu ’yan sanda suka tarwatsa su, suka kama wadansu.

’Yan Shi’ar sun yi jana’izar mutum 6 a Suleja da ke Jihar Neja a yammacin ranar, wadanda suka ce ’yan sanda ne suka kashe a zanga-zangar ranar Litinin.

Bayan jana’izar, Aminiya ta zanta da Malam Abdulhamid Bello, Shugaban Gidauniyar Shahidai ta Kungiyar IMN, inda ya nanata manufar kungiyar ta ci gaba da  zanga-zangar da ya ce mambobinsu na gudanarwa a kullum sama da shekara daya ke nan a yanzu.

  Marigayi DCP Usman Umar
Marigayi DCP Usman Umar

Ya ce masu shawartarsu su jingine zanga-zangar su rungumi tuntubar manya don neman a saki Sheikh Elzakzay ba su yi musu adalci ba. Ya ce “Babban dalilin da ya sa muke wannan muzahara da kara tsananta ta a yanzu shi ne, sakamakon bincike da wasu likitoci da suka zo daga waje ya nuna cewa yana dauke da guba. To gubar nan kuma ta kisan mummuke ce. Wannan ya sa muka zafafa kira na lallai sai a sake shi kamar yadda kotu tun farko ta ba da umarni, ko akalla a ba shi dama ya je a duba lafiyarsa. Kuma su mahukuntan idan ba sa son wani abu sai su kirkiri wata karya don su samu damar aukawa a kanmu, su ce mun yi wani abu.”

Game da zargin cewa ’yan kungiyar na da hannu a kashe Mataimakin Kwamshinan ’Yan sandan Abuja, Malam Abdulhamid Bello ya ce “Lamarin a fili yake saboda yanzu ana daukar komai a waya da sauransu. Sai su nuna lokacin da ya iso wajen da lokacin da yake magana da ’yan uwa tare da gudanar da cikakken bincike a lamarin. Amma duk ba su yi haka ba, sai kawai suka yi sauri suka binne shi ba tare da yin wadannan abubuwan ba. Ba za mu taba yarda da wannan zargin ba, don ba aikinmu ba ne kuma ba mu taba yi ba kuma idan ma harbin nasa ne aka yi, to wani daga cikinsu ne ya aikata kamar yadda suka saba yi. Su kashe dan uwansu, su ce wani ne ya kashe shi.”

Ya ce, sun tabbatar da kashe musu mutum shida, kuma suna da yakinin akwai wasu gawarwakin jama’arsu da ba a mika musu ba.

A baya-bayan nan dai zangar-zangar ta ’yan Shi’a da ta dauki sabon salo, ta rutsawa da jama’ar da ba su ji ba ba su gani ba, musamman ma ma’aikatan gwamnati kko masu kai ziyara a wasu ma’aikatu, inda a wani zubin ake lalata motoci ta hanyar fasa gilasansu sakamakon jifa ko rubuce-rubuce da jan fenti a jikinsu da ake rubuta “A Saki Zakzaky.” Rubuce-rubucen sun hada har da a jikin gine-genen ma’aikatu da kuma gefen titi.

Ko a ranar Litinin, an banka wuta ga wata karamar cibiyar Hukumar Agajin Gaugawa (NEMA) da ke  kusa da Sakatariyar Tarayya kuma kusa da wasu muhimman wurare, kamar Ma’aikatar Kudi da ta Harkokin Kasar Waje da Majalisar Dokoki da Kotun Daukaka Kara da Kotun Koli da  kuma daya daga cikin mashigar Fadar Shugaban Kasa.

A jawabin da ya yi bayan ziyarar gani da ido, Babban Daraktan Hukumar NEMA, Injiniya Mustafa Maihaja ya zargi ’yan Shi’ar da kona musu motoci biyu da suka hada da ta tafi-da-gidanka don daukar marasa lafiya da motar daukar gawarwaki.