Da Dumi Dumi

Dalilin da Gwamnati za ta hana almajiranci

  • Hana almajiranci babban bala’i ne – Dahiru Bauchi
  • Ba almajiranci ne matsalar tsaro ba – Sheikh Jingir
  • Abin da ya kamata gwamnati ta yi maimakon hana almajiranci – A.K. Daiyabu

A karshen makon jiya ne Gwamnatin Tarayya ta ce za ta hana tsarin karatu na almajiranci don magance matsalar tsaro da kasar nan ke fama da ita. Mashawarcin Shugaban Kasa kan Harkokin Tsaro Manjo Janar Babagana Moguno (mai ritaya) ne ya bayyana haka ga taron manema labarai bayan kammala taron Majalisar Tattalin Arziki ta Kasa (NEC) da Mataimakin Shugaban Kasa Yemi Osinbajo ya jagoranta a Abuja.

Janar Monguno wanda ke tare da Sufeto Janar na ’Yan sanda Mohammed Adamu da gwamnonin jihohin Adamawa Ahmadu Fintiri da na Anambra Willie Obiano da na Ondo Rotimi Akeredolu, wanda ya ce tsarin alamjirancin yana yaye mutanen da suke zama barazana ga tsaro ya ce yana da muhimmanci a hana wani rukuni da ke kara-kaina da sunan neman wani ilimi da ba tsararre ba ne wanda ya fara jawo matsaloli ga jama’a.

Sai dai ya ce ba za a dauki matakin ta hanyar da za a cutar da almajiran ba ne, za a yi aiki ne tare da gwamnatocin jihohi wajen tilasta bayar da ilimi kyauta a matakin farko ga kowane yaro. Ya ce za a bi tsarin da aka yi amfani da shi a jihohin Yamma a shekarun 1950 zuwa 1960 lokacin da Firimiya ya mayar da ilimi kyauta kuma tilas ga daliban firamare da sakandare.

Ya ce idan aka dubi dimbin almajiran da ake da su za su iya taimakawa wajen bunkasa kasar nan idan suka samu ilimin zamani.

Janar Monguno ya ce gwamnati za ta hada hannu da dukkan bangarorin da abin ya shafa don magance matsalar almajiranci inda ya yi tambayar kasashen nawa ne suke gudanar da irin wannan tsari na almajiranci? “Wajibi ne mu fada wa kanmu gaskiya, tilas mu duba wannan batu da muke kawar da kai daga gare shi. Don haka lokacin da na yi wa Majalisar Tattalin Arziki bayani na ankarar da ita hadarin da ke cikin wannan tsari kuma Shugaban Kasa yayin kaddamar da ita y ace wajibi ne a bayar da ilimi kyauta kuma tilas. Ba muna kokarin tozarta wani rukunin mutane ba ne,” inji shi

ADVERTISEMENT
Share