Da Dumi Dumi

Dalilin da Hukumar NCNE ke son kafa Gidan Rediyon Fulani – Farfesa Bashir Haruna

Wadansu ’ya’yan Fulani makiyaya suna daukar karatu a Ungwar Maigero
Wadansu ’ya’yan Fulani makiyaya suna daukar karatu a Ungwar Maigero

Farfesa Bashir Haruna Usman, shi ne Babban Sakataren Hukumar Kula da Ilimin Makiyaya ta Kasa, (NCNE) da ke da hedkwata a Kaduna. A tattaunawarsa da Aminiya, ya yi karin haske kan shirin hukumar na kafa gidan rediyo domin ’ya’yan Fulani makiyaya da ba su zama wuri guda da ’ya’yan masunta. Ya kuma yi bayani game da kalubalen da hukumar ke fuskanta wajen isa ga makiyayan sakamakon matsalolin tsaro:

Mene ne ayyukan da suka rataya a wuyan Hukumar Kula da Ilimin Makiyaya (NCNE)?

An kafa hukumar a 1989 a karkashin wata dokar soja lokacin mulkin Janar Ibrahim Badamasi Babangida. Akwai ayyuka da kudirorinmu a hukumar. Nauyin da ke rataye a kanmu shi ne mu ilimantar da rukunin al’ummar da ba su da galihu, wadanda ba sa zama wuri daya, kamar Fulani makiyaya da masunta da ke kaura daga wannan wuri ruwa zuwa wancan tare da manoman da ke yawan hijira. A wannan kasar, muna da rukunin al’ummar da ke kaura daga wannan yanki zuwa wani, suna bidar ruwan sama. Alal misali, a lokacin rani a Arewa akwai mutanen da suke hijira daga Arewa zuwa yankin tsakiyar kasar nan da kuma Kudu, inda ake samun ruwan sama na dogon lokaci a shekara. Don haka suke kaura zuwa can da nufin yin noma, sa’annan su sake dawowa Arewa lokacin damina don sake yin noma. Wadannan su ne rukunin al’ummar da nauyin ilimantar da su ya rataya a kanmu, dalilin haka shi ne saboda makiyaya ba sa zama wuri daya. Hikimar shugabannin wancan lokacin ita ce, idan dai aka mai da wannan rukunin al’ummar saniyar ware, to ba shakka akwai yiwuwar faruwar wani mummunan abu, kuma ga shi hakan na faruwa a yanzu. Sun kasance suna ganin an bar su a baya, ba sa samun ilimi, kawai abin da suke tunani shi ne tayar da zaune-tsaye, kamar yadda muke gani a halin yanzu. Amma da a ce mun yi aiki da wannan hikimar tun wancan lokaci yadda ya dace, da ba mu tsinci kanmu cikin wadannan matsalolin ba.

Amma idan muka fadada bayanin ayyukanmu, hukumarmu ita ce ke da hakkin tsara manhajar karatu. Don haka muna tsara manhajar kuma muna tara su wuri guda, sakamakon wuyar sha’anin riskarsu, kuma muna sa ido kan koyar da su don sanin ko suna samun abin da ya kamata su sani. Don haka da muka gamsu da tsarin makarantunsu, sai muka yanke shawarar matsawa zuwa mataki na gaba. Amma nauyin samar da malamai da gine-gine da sauransu ya rataya ne kan hukumomin ilimi bai-daya na jihohi. Wannan shi ne bambancin ayyukan hukumomin ilimi na jihohi da na tarayya. Su ne za su samar da malamai mu kuma mu tsara manhaja.

Mun hada gwiwa da jami’o’i hudu wajen yin nazari tare, inda muka fito da manhajar karatun da za ta yi daidai da bukatun wadannan rukunonin jama’a, saboda wadannan rukunonin na da yawan gaske. Ban da ma wadanda na ambata a baya,  akwai kuma kabilun da ke zaune a yankin Tafkin Chadi a Arewa maso Gabas da suke yawan kaura, kamar  Shuwa Arab da Kwayam da Budum da bakaken Buzaye. Don haka mun tsara manhajar karatunsu, mun kuma mika wa hukumomin ilimin bai-daya na jihohin domin su aiwatar.

ADVERTISEMENT

Ko makarantun nasu za su rika yin kaura daga wuri zuwa wuri, kamar yadda makiyayan suke yi?

Eh, muna da tsarin makarantu iri uku; akwai na wuraren kiwonsu, inda muke tsammanin su zauna na kimanin wata uku, don haka muna yin gine-gine na dindindin a wurin. Amma idan sun tashi kaura, muna da tsarin ajujuwan tafi-da-gidanka. Yayin da suke tafiya cikin ruwa, nan ma muna da ajujuwan da ake koyarwa cikin kwale-kwale, inda za a koyar da su yayin da jirgin ruwan ke tafiya.

Sai dai babbar matsalar da muke fuskanta a baya ita ce ta rashin samun malaman da za su bi su duk inda suka koma. Amma da zuwana, na yi kokarin shawo kan matsalar ta hanyar bullo da daukar malamai daga cikinsu masu shaidar karatun NCE, wadanda za su rika koyar da su ko’ina suka kaura, yadda za su yi kishin suna koya wa ’yan uwa da sauran danginsa karatu. Mu a Hukumar NCNE, muna lura ne da karatun firamare da na karamar sakandare, daga nan ne za su shiga babbar sakandare, wadda ita ba huruminmu ba ce, sai dai na ji tsohon Ministan Ilimi Malam Adamu Adamu ya ce za a kafa manyan makarantun sakandare a tsarin namu

Kwanan nan maganganu sun yawaita a jaridun kasar nan game da wannan hukuma taku, kan kokarinku na kafa gidan rediyon Fulani; ko za ka yi mana karin bayani kan haka?

A gaskiya batun gidan rediyon nan al’amari ne mai sauki. Kawai abu biyu ne zuwa uku suke faruwa. Na farko dai aikinmu shi ne ilimantar da wadannan al’ummomi masu kaura daga nan zuwa can. Na biyu akwai batun rikici tsakanin manoma da makiyaya da ya dade yana faruwa amma ya yi kamari cikin shekara uku zuwa hudun da suka gabata. Sai na uku wanda shi ne batun garkuwa da mutane. Shirye-shiryenmu ba sa kaiwa gare su, wadanda muke shiryawa daga nan hukumarmu muke kaiwa tashoshin gidajen Rediyon Tarayya na Kaduna da Ibadan da Bayelsa da kuma Enugu, inda muke sayen filaye na minti 30 don watsa mana shirye-shiryen. Mun lura cewa ya kamata mu samu sababbin hanyoyin sauke nauyinmu na ilimantar da makiyayan. Akwai kuma batun garkuwa da mutane, wanda ko mu da muka sansu, suka sanmu sosai, ba mu tsira daga wannan lamari ba. An taba yin garkuwa da ma’aikatanmu hudu da suka je da nufin isar da sakonninmu. Sai da na biya diyya kafin aka sako su. To hakan ne ya sanya muka ga dacewar tunda dai muna da dakin nadar shirye-shiyenmu kuma muna da motocin tafi-da-gidanka na watsa shirye-shirye kai-tsaye guda biyu da muke fita da su wajen gabatar da wasu shirye-shirye na musamman, sai muka yanke shawarar cewa me zai hana mu inganta wadannan mu sayo na’urorin watsa shirye-shieye na rediyo? Kawai sai muka tuntubi kwararru a bangaren da za su yi nazarin sharuddan da Hukumar Kula da Gidajen Rediyo da Talabijin ta Kasa (NBC) ta gindaya wajen kafa tashar rediyo. Mun gabatar mata da bukatarmu kuma ta ba mu lasisin kafa tashar rediyon, bayan mun biya kudi. Mun nemi a ba mu lasisin kafa tashar a kan zangon FM amma sai suka ba mu zangon AM mai watsa shirye-shirye ga kasa baki daya, ta yadda ba kawai makiyaya shirye-shiryen namu za su kai gare su ba, a’a har da manoma da masunta a yankin Kudu. Kawai abin da muke jira yanzu shi ne mu samu kudin sayen na’urorin da za mu fara watsa shirye-shiryen.

A lokacin da tsohon Ministan Ilimi yake jawabin ban kwana da ofis, a kokarinsa na zayyana irin nasarorin da ya samar a wa’adinsa, ya kira taron manema labarai inda ya ce daga cikin nasarorin da ya samu akwai na samun lasisin kafa gidan rediyo don ilimantar da makiyaya masu kaura daga wuri zuwa guri, wanda da zarar ya fara yada shiri, zai taimaka wajen rage fitinun da ake yawan samu a tsakanin manoma da makiyaya, domin za mu ilimantar da ’ya’yansu. Babban dalilin Ministan na furta hakan bai wuce na damuwarsa kan yawan yaran da ba su zuwa makaranta ba, wadanda suke gararamba kan titunan kasar nan. Ni da shi muna aiki kafada-da-kafada wajen ganin an shawo kan matsalar. Amma abin takaici, kawai wani dan jarida mai son azizita rikici sai ya ba da rahoton cewa wai Gwamnatin Tarayya ta ba da lasisin kafa rediyon Fulani. A kashin gaskiya babu wani abu mai kama da haka, sai dai kawai tasha ce mallakar Hukumar NCNE da zimmar riskar al’ummomin da take muradi.

A takardun da Hukumar NBC ta ba mu don cikewa, sun tambaye mu cewa cikin harsuna nawa kuma wane lokaci za mu rika watsa shiryen-shiryenmu da sauran tambayoyi. Kuma mun shaida musu cewa za mu rika gabatar da shirye-shiryen ne a harsunan Ingilishi da Hausa da Turancin Buroka da Fulatanci, kamar yadda kowace tashar rediyo ke yi a kasar nan. Kuma kowace tashar rediyo na da muradinta, mu a nan Hukumar NCNE muradinmu shi ne ilimantar da wadannan mutane kuma da zarar mun take ka’idojin Hukumar NBC, za ta soke lasisinmu. Abin takaici ne matuka yadda wadansu manyan mutane a Najeriya ke wuce gona da iri suna zargin wai za a sanya kowane dan Najeriya ya koma magana da yare guda, wato Fulatanci. Kawai abin da muke jira shi ne mu samu mu kafa na’urori don fara yada shirye-shirye.

Kun tuntubi kwararrun a harkar watsa labarai ta rediyo, wadanne shirye-shirye za ku rika gabatarwa, idan kuka fara?

Na farko dai shirye-shirye ne na ilimantarwa, kamar wanda a halin yanzu muke gabatarwa a gidajen rediyo mallakar Gwamnatin Tarayya guda hudu. Su ne “Don Makiyaya a Ruga,” wanda shiri ne na minti 30 da ke tabo batutuwan tsabta da kiwon lafiya da nishadantarwa. Kuma za mu hada da wasan kwaikwayo, inda za mu gayyato shahararrun jarumai da ’yan wasan barkwanci su tabo batutuwa kan yadda za a zauna lafiya da juna. Don haka za mu kawo kwararrun da za su yi magana don fahimtar da su a kan muhimmancin zaman lafiya cikin al’umma. Akwai kuma shirye-shiryen da za mu gabatar masu kayatarwa da kuma labarai, amma dai za mu fi ba da fifiko ga shirye-shirye masu ilimantarwa.

Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya