✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dalilin da kwale-kwale ya hallaka mutum 7 a Nasarawa

A karshen mako jiya ne kimanin mutum 7 suka rasa rayukansu sakamakon kifewar wani kwale-kwale a kauyen Gwayaka da ke yankin Raya Kasa na Lafiya ta…

A karshen mako jiya ne kimanin mutum 7 suka rasa rayukansu sakamakon kifewar wani kwale-kwale a kauyen Gwayaka da ke yankin Raya Kasa na Lafiya ta Gabas a Jihar Nasarawa.

Wakilinmu ya ziyarci inda lamarin ya auku inda ya tattauna da Shugaban Yankin Raya Kasa na Lafiya ta Gabas Shu’iabu Zanwa wanda ya ce rahoton binciken da ya samu dangane da lamarin ya gano cewa yawancin wadanda lamarin ya shafa manoman tumatir ne ’yan asalin Jihar Kano mazauna yankin.

A cewarsa bayan sun taso daga gonakinsu za su koma gida ne da yamma sai suka gamu da wannan bala’i. Ya ce wadanda lamarin ya shafa sun yi wa kwale-kwalen yawa, don a cewarsa sun kai su 20 har da matukin kwale-kwalen.

Ya ci gaba da bayyana cewa, “Akan hakan ne ma ya sa matukin kwale-kwalen ya nemi su bari ya fara daukar wasu cikinsu ya kai kafin ya dawo ya kwashe sauran amma sai suka ki amincewa da hakan kasancewar yamma ta riga ta yi kuma suna tunanin yaudararsu yake yi idan ya kwashe wadansu ya kai ba zai dawo ya kwashe sauransu ba. Da suka ki suka shiga kwale-kwalen dukkansu sai direban ya ce ba zai tafi ba ya fasa tafiyar. A nan take ne sai daya daga cikinsu ya fara tuka kwale-kwalen. Sai da suka kai tsakiyar kogin sai kwale-kwalen ya kifar da su,” inji shi.

Ya kara da cewa kawo yanzu an gano tare da fitar da gawarwakin mutum 7 daga cikinsu yayin da sauran da suka rayu aka fito da su da rai a hannun Allah.

Dangane da matakin da mahukuntan yankin suke dauka dangane da magance aukuwar rasa rayuka sakamakon kifewar kwale-kwalen da ke faruwa a yankin, Shu’iabu Zanwa ya ce tuni suka yi gargadi ga direbobin kwale-kwale da ke yankin dangane da daukar fasinjoji fiye da kima inda ya ce sabuwar dokar da mahukuntan yankin suka yi, ita ce duk wanda aka kama da laifi za a gabatar da shi a kotu inda za a tuhume shi da laifin kisa da gangan da sauransu.

A cewarsa a kwanakin baya ma an yi asarar buhunan shinkafa 50 sakamakon nauyi fiye da kima a wani kwale-kwale a yankin inda ya ce ya zame wa hukumar dole ta yi wani abu a kan lamarin don ba za ta ci gaba da kallon wadannan direbobi suna ci gaba da kashe rayukan al’umma da gangan ba.