✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dalilin da muka kafa Kungiyar Matasan Jos

Kungiyar Ci gaban Matasan Jos (COJOYA) ta dukufa don bayar da gudunmawa wajen bunkasa ci gaban garin Jos da kewaye. Barista Buhari Ibrahim Shehu shi…

Kungiyar Ci gaban Matasan Jos (COJOYA) ta dukufa don bayar da gudunmawa wajen bunkasa ci gaban garin Jos da kewaye. Barista Buhari Ibrahim Shehu shi ne Shugaban Kungiyar, ya bayyana wa Aminiya cewa sama da mutum 1000 ne, suka amfana da shirin kiwon lafiya da kungiyar ta gudanar kwanakin baya a Jos da sauran ayyukanta:

Mene ne dalilin kafa wannan kungiya?

A bara mun lura cewa al’ummarmu na garin Jos suna zaune babu wasu abubuwan ci gaba da matasa suke kawowa. Domin a tunaninmu ya kamata matasa su rika bada gudunmawa wajen ci gaban al’ummarmu. Don haka muka hada kanmu muka  kafa wannan kungiya.

A baya  gwamnatin Jihar Filato ta fara wasu aikace-aikacen gyara hanyoyin cikin garin Jos, amma aka dakatar. Hakan ya sa muka rubuta wa Gwamnan Jihar, Barista Simon Lalong, cewa akwai matsaloli kwarai da gaske kan dakatar da aikin gyaran hanyoyin. Don haka ya kamata a ci gaba da wannan aikin da aka fara. Nan take gwamnatin ta zo ta ci gaba da aikin gyaran hanyoyin.

Sai muka ce idan har za mu yi wannan  gwamnati ta saurare mu, me zai sanya ba za mu hada kanmu mu mayar da wannan tafiya ta zamanto kungiya da za ta taimaka a bangarorin da suka shafi ci gaban al’ummarmu ba? Dalilin kafa wannan kungiya, ke nan.

Zuwa yanzu wadanne nasarori kuka samu?

Mun samu nasarori masu yawa. Domin a shekara daya da kafa kungiyar, Allah Ya taimake mu mun gabatar da ayyuka masu yawa. Bayan hanyoyin cikin garin Jos,  mun zauna mun yi magana kan babbar matsalar da take damun garin Jos, Sara-Suka. Mun gayyaci kwararru kan harkokin tsaro da ayyukan al’umma, muka tattauna kan hanyoyin magance wannan matsala, inda muka  gano cewa matasan da suke wannan mummunan al’amari, wadansu na yi ne saboda rashin aikin yi, wadansu saboda shaye-shaye. Don haka muka fito da shirin wayar da kan matasa kan illolin wannan mummunar dabi’a ta Sara-Suka da kuma illolin shaye shaye. Sannan mun zauna da manyan gari muka ba su shawara kan a farfado da aikin banga.

Bayan haka mun shirya taron karfafa gwiwa wajen neman ilimi, inda a bara, muka samu makarantu 33 da suke cikin garin Jos muka shirya musu gasar kacici-kacici da muwahara, an samu gagarumar nasara kan wannan shiri. Yaran da suka yi kokari a wajen wadannan tarurruka, manyan gari sun ba mu hadin kai ta hanyar biya wa wadansu kudin rubuta jarrabawar NECO da WAEC.

Sa’annan a duk bayan mako biyu, muna zuwa makabartar hanyar Zariya da ke nan Jos, domin gyara ta. Muna cike ramuka da cire ciyayin da ke cikinta.

A karshen bara, mun shirya tarurrukan wayar da kan jama’a kan gwaje-gwajen da ake yi kafin aure. Yanzu wasu jihohin kasar nan ba a yarda a daura aure, dole sai an yi gwajin cututtukan da ake kamuwa da su, amma a nan Jos ba a yin haka. Kuma hakan yana haifar da matsalol, don haka muka shirya taron wayar da kai tare da hadin gwiwar Kungiyar Jama’atu Nasril Islam, Reshen Karamar Hukumar Jos. Mun gayyaci likitoci da malaman addini,  sun wayar mana a kai kan wannan al’amari.

Mun gabatar da shirin tallafa wa al’umma da magunguna, mun dauko jami’an kiwon lafiya akalla 20, muka je Unguwar Sabon Layi da ke nan Jos. Mun ba su gudunmawa kan cututtukan hawan jini da hanta da maleriya, akalla sama da mutum dubu ne suka amfana,da wannan shiri.

Kungiyarmu ta bayar da gudunmawa a wajen taron zaman lafiya da Kungiyar Zaman Lafiya ta Jihar Filato ta shirya. Har gasa kungiyarmu ta ci a wannan taron zaman lafiya.

Yaya ka ga yadda al’ummar Jos uka karbi kungiyar?

Al’ummar Jos sun karbi ayyukan kungiyar hannu bibbiyu. Kamar ayyukan da muka dauka na makabarta, mutane da yawa wadanda ba ’ya’yan wannan kungiya ba ne, sun fito sun ba mu gudunmawa wajen  yin aiki. Wani ya kawo ruwa, wani ya kawo cincin da sauransu. Hakan ya nuna mutane sun gamsu da ayyukan da muke yi.

Wane sako kake da shi ga al’ummar Jos?

Sakona ga al’ummar Jos shi ne wannan kungiya tamu ce baki daya wato ta kowa da kowa ce. Saboda haka ina kira ga duk wanda yake son ci gaban garin Jos, ya zo mu tafi tare.