✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dalilin da muke zaune lafiya a masarautata – Sarkin Dass

Garin Dass yana da nisan kilomita 51 a Kudu maso Yamma da birnin Bauchi. Kuma Mai martaba Sarkin Dass Alhaji Usman Bilyaminu Othman daya ne…

Garin Dass yana da nisan kilomita 51 a Kudu maso Yamma da birnin Bauchi. Kuma Mai martaba Sarkin Dass Alhaji Usman Bilyaminu Othman daya ne daga cikin sarakuna masu daraja ta daya su shida  da ke  Jihar Bauchi. Shi ne Sarki na 8 a jerin sarakunan Dass, wanda ya hau sarauta tun bayan rasuwar mahaifinsa Alhaji Bilyaminu Usman a shekarar 2009. Yanzu shekara 10 yana kan karaga, inda ya amsa tambayoyin manema labarai kan masarautar da al’amuran sarauta:

Bayan rasuwar mahaifinka aka nada ka Sarkin Dass wadanne darussa ka koya bayan hawa karagar sarauta?

Gaskiya na samu darussa masu yawa tun lokacin da Allah Ya sa na zama Sarki bayan mahaifina ya yi sarauta na tsawon shekara 30, kuma ya rasu a ranar 9 ga Satumban 2009. Duk da cewa akan samu kalubale da yawa wajen warware al’amura, amma kalubalen bai kunshi tashe-tashen hankali ko rikici ko hatsaniya ba. Domin al’ummarmu mutane ne masu kaunar zaman lafiya. Akwai zaman lafiya amma in mutum yana jagorantar mutane sama da dubu 250 dole ka samu wasu kalubale na yanayin jama’a. Ka ga akwai bukatu da yawa na jama’a bukatar kayayyakin kyautata rayuwa da yanayin zamantakewa duk da cewa nan muna zaune lafiya, babu fada a tsakaninmu. kuma mutanenmu suna da kwazo wajen noma da neman ilimin addinin da na boko. Al’ummarmu kuma suna yin sana’o’i musamman noma komai na tafiya ba tare da wata matsala mai girma ba. Don haka babban burinmu shi ne jama’a su zauna lafiya.

Ko Mai martaba zai ba mu takaitaccen tarihin wannan masarauta?

Fiye da shekara 2000 kabilun Jarawa da suka fito daga Gabas ta Tsakiya suka shigo Afirka ta Tsakiya suka taho nan Najeriya ta kasar Barebari inda suka fara zama a Ngazargamu da ke Jihar Yobe a yau. Bayan sun zauna na wani lokaci sai suka fito har suka iso kasar Bununu da ke Tafawa Balewa a yau shekara 1500, nan suka zauna har zuwa shekara ta 1800 Miladiyya, lokacin da makiya suka yi ta aiko musu da takarda cewa su bi su ko kuma su zo su yake su  sai kakanninmu a lokacin Mummuni ke sarauta suka yanke shawarar barin Bununu su koma wajen da za su iya samun kariya. Sai ya gano wannan dutse na Mbula, ya kasance shi ne wajen kariya daga mahara da mayaka, sai suka koma kan wadannan duwatsu na Dass. Dutsen yana da girma da tsawo don in mutum yana ciki (kansa) ba za ka gane akwai mutum a wajen ba, a nan aka samar wa wajen suna Dass domin a kan dustsen Mbula akwai ciyawa da ke tsirowa da ake kiranta da Dassa da harshen Hausa. Idan mutum zai je wajen sai a ce masa ya je wajen da Dassa take tsirowa a gindin dutsen. Kuma sun zabi wannan waje ne saboda akwai koguna da yawa da mutane za su iya fakewa a ciki, kuma akwai wani tafki a saman dutsen. Sannan wadannda suke kan dutsen suna iya ganin mutum in yana zuwa daga nisan kilomita 30, sai su sanar da maza su shirya su hau don su kare garin. Don haka in mutum yana daga nisan kilomita 30 daga kan dutsen Mbula za ka iya hango shi.

Bayan an zauna a wajen a 1840 sai muka samu wadansu mutane suka zo wajen karshin jagorancin Jarawa, sai aka shata kan iyakokinmu don mu kare kasarmu tare da wadannan al’ummar da muka samu ta hanyar haka ne muka zauna a kasar Dass muka kasance al’ummar da yaki bai taba cinsu ba.

Wadannen irin al’adu ne yanzu ba a yi?

Mudai a nan muna da kabilu biyu Jarawa da Bankalawa, kuma muna magana da juna mukan yi wasu al’adunmu tare da su, mukan yi bikin girbin amfanin gona tare mukan yi sauran bukukuwa na al’adu tare.

Lallai kamar yadda yake a ko’ina zuwan addinin Musulunci da na Kirista sun sa mutane sun bar wasu al’adu sun koma koyarwar addinai. A yau muna bin koyarwar addinin Musulunci ne, kuma Turawan mulkin mallaka sun zo sun zauna a 1920 sun kafa makarantar firamare ta farko a 1923 sannan a 1929 da 1933 aka kakkafa wasu makarantu. Sannan Kiristoci kuma suna bin koyarwar addinin Kirista, an ilimantar da mutane yadda suka san cewa akwai Allah da Ya kamata su bauta maSa, bayan addinin Musulunci. Da muna yin abubuwa wadanda duk yanzu an bari muna zaune tare. A da akwai dodanni da suke fitowa sau daya a shekara yanzu duk an bar irin wadannan al’adu kuma a da suna fitowa duk wanda ya yi jayayya da su zai mutu ko wasu za su bata ana samun ire-iren haka a da can, amma yanzu wadannan addinai namu sun sauya rayuwar al’umma ba a yin wadancan al’adu.

Wadanne abubuwa ne Mai martaba yake yi da ya zama Sarki yanzu ba ya yi?

Ba wai kawai ina Sarki ba, ko a matsayin dan Sarki ma akwai abubuwa da yawa da ba zan iya yi ba. Ka ga in kai Sarki ne ko shugaba ne dole ka yi jagoranci abin koyi ta hanyar nuna kyawawa kuma nagartattun halaye da jama’arka za suy i koyi da kai. Za ka hada da hakuri da dattaku da sanin ya kamata . kuma dole ka nuna kai mai addini ne. Za ka rika gudanar da rayuwarka cikin tawali’u da tsoron Allah kamar yadda addinin ya shimfida, kuma za ka yi wa mutane jagoranci da tsoron Allah. Za ka rika hada kai da al’ummarka kana halartar tarurrukansu kana sauraronsu kana yi musu ayyukan da za su kyautata rayuwarsu. Wajibi ne ka ga cewa al’ummarka sun samu ilimi, sun kasance masu kaunar zaman lafiya da juna masu biyayya ga hukumomi.

Gaskiya na gaza yin abubuwa da yawa, tafiye-tafiye na daga cikin abubuwan da na fi so musamman tafiya mai nisa. Da ina tafiya daga Bauchi zuwa Legas zuwa Sakkwato da wurare da yawa, ina son tuka mota da kaina amma yanzu ba zan yi haka ba, sai dai a tuka ni. Kuma ina son hawa doki ina sha’awar wasannin motsa jiki.  Da ina wasan kwallon raga amma duk wadannan ba zan yi ba yanzu, koda yake muna da wajen motsa jiki na cikin gida nakan je in yi. Kuma ina yawan karatun Alkurani, ina kuma yin bincike don ni malamin gona ne da nake aiki da hukumomi da dama da kungiyoyin bada agaji da yawa, ina kuma cikin ayyukan kula da lafiyar jama’a ni ne ma Shugaban Kwamitin Wayar da Kai kan Kiwon Lafiya na Jihar Bauchi. Ina yin wannan aiki kusan shekara 20 ke nan.

Da kai ma’aikacin banki ne shin tilasta ka aka yi ka zama Sarki ko yaya?

Ni tsohon ma’aikaci ne na yi aiki da ma’aikatar gona sai kuma na koma Bankin Raya Afirka na koma Bankin Arewa (Bank of the North). Daga nan sai na dawo don yin aiki wa jihata inda na yi aiki a matsayin mai taimaka wa tsofaffin gwamnonin Jihar Bauchi Alhaji Ahmadu Mu’azu da Malam Isa Yuguda.  Kuma na yi aiki da mahaifina a matsayin Chiroma, wadda babbar sarauta ce da ake bai wa ’ya’yan Sarki musamman babba daga cikinsu. Kuma bisa al’ada a matsayina na babban dan Sarki, ka san yawanci in kai ne babba in dai ba wani abu ne zai hana mutum ba, zai yi takarar neman sarauta, mun yi takara da sauran mutum shida kuma ni Allah Ya sa aka zaba a matsayin Sarkin Dass na 8 kuma ina da ’ya’ya 12, shida maza shida mata.

Ka taba tunanin wata rana za ka zama Sarki?

Gaskiya in ka tashi a matsayin dan Sarki a kowace gaba na rayuwarka akwai abubuwa da za a rika tarbiyyantar da kai a kai. Kuma za ka ga yadda jama’a za su rika nuna damuwa da kai kanka. Haka ma manyan masu rike da sarautu a fada, kuma mahaifinka zai rika ba ka tarbiyya, zai nuna maka yadda ya kamata ka kasance a matsayin dan Sarki, kuma a matsayin shugaban jama’a. Ka ga dai a kowane lokaci dole ka zama mutum mai kamun kai da nuna halin girma da dattaku cikin duk abin da kake yi. Kuma za a sa ka tsakanin masu rike da sarautu kuna aiki tare domin ka koyi abubuwa da yawa daga gare su, don ka goge kan al’amuran sarauta. Ta haka ne za ka girma cikin tarbiyya da nagartattun halaye da koyon yadda za ka rike al’umma.

Wadanne al’adu ake yi kafin a zabi Sarki?

Akwai al’adu da yawa amma saboda zuwan addinin Musulunci an bar su, kuma kasancewarmu Musulmi ne an bar yawanci wadancan al’adu da suka saba wa karantarwar addinin Musulunci. Don haka akan yi abubuwa ne bisa karantarwar shari’ar Musulunci. Misali akwai al’adar da ake yi ta zaben sabon Sarki, kuma in za a zabi sabon Sarki akwai wasu matakai; za ka shafe kwana 41 ba tare da kowa ba koda kuwa matarka ce. Za ka tafi da wadansu mutane da za su koya maka yadda al’amuran sarauta suke, sannan za a koya maka abubuwan da addinin Musulunci ya karantar kamar yawan karanta Alkurani da kuma yawaita addu’a domin samun tsawon rai da adduo’’in zama lafiya. Amma gaskiya yawancin al’adun yanzu ba a yin su kamar yadda na ce.

Ko mutane na yi maka kallon shugaban addini ban da sarauta ta gargajiya?

Kwarai kuwa ai duka biyu ne muka hada, kafin zuwan Turawan mulkin mallaka, kowanw Sarki shi ne yake kula da iyakar kasarsa, kuma dukkan haraji da dukkan albarkatun kasa suna karkashin kulawar Sarki ne, kai koda lokacin cinikin bayi ne. Amma da Turawan mulkin mallaka suka zo, sai aka rage wa sarakunan wasu daga cikin ayyukan da suke gudanarwa. Ka ga a da Sarki shi ne ke shugabantar yadda ake gudanar da shari’u da warware rikice-rikecen aure da na al’umma, Sarki na yin horo ga mai laifi, yana ladabtar da wanda ya yi laifi. Sarakuna su ke kula da gidajen yari da karbar haraji su gina tattalin arzikin kasa. Bayan zuwan Turawa duk wadannan sun gushe. Akwai wani gyaran fuska da aka yi wa masarautu wannan gyaran fuska da gwamnati ta yi shi ne ya raba sarakuna da wasu daga cikin wadannan ayyuka, aka kirkiro kananan hukumomi aka cire jami’an tsaro daga karkashin sarakuna, aka kirkiro sojoji da sauran ire-irensu, saboda haka karbar haraji da samar da kayayyakin more rayuwa da gudanar da mulki duk aka maida su karkashin karamar hukuma. Amma lokacin zuwan Turawan mulkin mallaka Sarki shi ne shugaban al’ummarsa, shi ne shugaban majalisar gudanarwar al’ummarsa, kuma shi ke da ma’aikata da ’yan majalisar Sarki. Daga baya duk wata shawara da karamar hukuma ta yanke Sarki sai ya amince tukuna, amma a gyaran fuskar da aka yi wa kananan hukumomi a 1976, sai aka raba sarakuna da wadannan ayyuka aka mika wa kananan hukumomi.

Me ya ba ka sha’awar yin ayyuka da hukumomin lafiya?

Gaskiya mahaifina shi ya fara da PPFN, Kungiyar Kula da Kiwon Lafiyar Iyali, kuma ya halarci kwasa-kwasai da dama da tarurrukan kara wa juna sani da yawa kan kiwon lafiya. Kuma ya hada kai da Gwamnatin Tarayya kan allurar rigakafi a 1998.  Saboda dan ilimin kimiyya da nake da shi sai abin bai mini wahala ba na ci gaba da shiga cikin ire-iren wadancan ayyuka na kula da lafiyar al’umma. Domin a matsayina na shugaba hakkina ne in ga yaranmu na cikin koshin lafiya, matanmu na zuwa asibitoci kuma in tabbatar da cewa an yi wa al’ummarmu allurar rigakafi don kula da lafiyarsu. Muna da hadin gwiwa da kungiyoyin bada agaji na Amurka (USAID) da Asusun Yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) da Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) da sauransu.

A karshe wace shawara za ka bai wa al’umma?

Mu zauna lafiya da juna, mu girmama juna ba tare da la’akari da bambancin addini  ko siyasa ko kabila ba. Idan dukkanmu mun yi imani da Allah Shi ne Ya halicce mu kuma Ya yi mu daban-daban don mu san junannmu mu amfani junanmu, wajibine mu hada kai da juna mu yi hakuri da juna mu hada kai da abokan zamanmu.