✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dalilin da mutane ke ganin Buhari ya yi watsi da ni – Tony Momoh

Cif Tony Momoh na daya daga cikin jagororin jam’iyyu 3 da dunkulewarsu ta samar da APC wadda ta karbe gwamnati daga hannun PDP a 2015.…

Cif Tony Momoh na daya daga cikin jagororin jam’iyyu 3 da dunkulewarsu ta samar da APC wadda ta karbe gwamnati daga hannun PDP a 2015. Aminiya ta nemo inda yake, inda ya bayyana dalilin rashin jinsa da ake yi a gwamnatin APC, karkashin Shugaba Buhari da kuma matsayarsa a kan shugabancin jam’iyyar a yanzu da sauransu:

 

Shin wane ne Yarima Tony Momoh?

Ana mini lakabi da Yarima (Prince) ko Cif Tony Momoh, tsohon Ministan Watsa Labarai da Al’adu, dan jarida kuma tsohon Editan jaridar Daily Times kuma tsohon Shugaban Hukumar Gudanarwar Kamfanin Jiragen Sama na Najeriya. Mamba a Kungiyar Yakin Zaben Buhari (TBO) daga shekara ta 2003, sannan a 2011 aka zabe ni Shugaban Jam’iyyar CPC. Sannan daya daga cikin jagororin jam’iyyu 3 da suka hada da Ogbunnaya Onu na ANPP da Bisi Akande na ACN, jam’iyyun da suke shugabanta, suka game don samar da jam’iyya mai karfi ta APC da ta tunkari PDP a zaben shekarar  2015, ta samu nasara kuma take mulki har zuwa yau.

Wadannan nasararori da na samu a gwamnati da siyasa duk sun samo sila ne daga aikin jarida da na yi. Na samu digirina na farko a aikin a 1967, sai na biyu a bangaren Shari’a a 1974. Na riki Editan Daily Times daga 1976 zuwa 1980. Saboda haka zan iya bayyana kaina a matsayin dan jarida, lauya, jami’in gwamnati kuma dan siyasa.

Bayan APC ta samu nasara, an yi tsammanin a gan ka a cikin wadanda ake damawa da su sosai a gwamnatin amma ba a ga hakan ba. Me za ka ce kan wannan?

Wa ya ce maka ba a damawa da ni, alhali ina cikin na gaba-gaba a gwamnatin? Sai dai abu guda game da ni, ni ba mai zalama ba ne. Masu zalama ne kadai ba su san lokacin da ya kamata su dakata daga karba ko neman jagoranci ba. Na yi minista ina dan shekara 46, sannan na gudanar da kamfanin jiragen sama na Najeriya tsawon shekara 4 a matsayina na Ministan Watsa Labarai da Al’adu.

A lokacina ne na jagoranci samar da sauyin da rage cinkoso a sashin labarai na kasar nan tare da samar da Hukumar Kula da Rediyo da Talabijin (NBC), inda na rage babakeren gwamnati a bangaren. A lokacin ne aka rage karfin ikon Hukumar Talabijin ta Kasa (NTA) da Rediyon Najeriya daga kasancewar su kadai ne ke da ikon gudanar da watsa labarai a bangaren. Hakan ya ba wa kafofin watsa labarai masu zaman kansu damar shigowa a yi gogayya da su. A lokacina ne aka samu Kungiyar Fina-Finai ta Najeriya (Nollywood). Ba bangaren da ban taba ba a sashin wajen samar da sauyi. Na maida harkar tallace-tallace a kafofin watsa labarai da bangaren hulda da jama’a a matsayin sana’a mai zaman kanta. Na samar da doka da ta ba su kariya. Na riki mukamin Shugaban Kungiyar Ministocin Watsa Labarai na Afirka gaba daya, tsawon shekara biyu kuma mataimaki ga na al’adu, shi ma shekara biyu. Duk wadannan mukaman na rike su ne kafin in kai shekara 50. To mene ne ban cimma ba a wancan lokaci, da zan cimma a yanzu, a lokacin da na kai shekara 80 a bara? Duk wadanda ke rike da mukamin minista a gwamnatin nan, kana iya kiransu yarana . Ashe zai zama zalama in ce zan sake rike mukamin minista a yanzu.

Na wadatu da mukamin da gwamnatinmu ta ba ni na Uban Jami’ar Jos, inda hakan ya ba ni damar taimakawa wajen kyautata sha’anin jami’a kuma ina cike da farin ciki da haka. Wadansu na bukatar rike wani matsayi ne da zai ba su damar karfafa kansu ta kwangila ko wani abu. A rayuwata ban taba fuskantar wata tuhuma ko bukatar in ba da bahasi a kan duk aikin da na gudanar a baya ba. Rikon amanata ce ta kai ni ga haka. A lokacin da na ke minista da farko, albashina Naira dubu 16 ne a shekara, ba fa na ce a wata daya ba.Sannan bayan shekara biyu aka maida shi zuwa dubu 28 a shekara. Gabanin nan lokacin da na bar aikin Editan Daily Times, albashina Naira dubu 32 ne a shekara, amma na gwammace karbar albashin Naira dubu 16 da gwamnati ke bayarwa a lokacin saboda ni ne na amince da hakan.

A lokacin da nake Edita, ina da motata ta shiga samfurin Baswaja, sai ga shi da na bar matsayin minista ba ni da mota. Na shiga aiki ba tare da wani tabo ba kuma na sauka daga kai ba tabo. Saboda haka idan a yau aka ba ni mukamin minista ba zan sauya daga tsarin da nake na baya ba.

Matata ce ta ciyar da ni a lokacin da na riki mukamin a baya. Na riki wurin kudi amma ban sa hannu na dauka ba. Ni ne da na farko a cikin ’ya’ya 65 na mahaifina. Za ka iya bayyana gidanmu da iyali mafi girma a duniyar nan, da ya tafi cikin tsari ba tare da hayaniya ba. Babu yadda zan taba abin da ba ni da hakki a kai don hakan zai bata sunan gidanmu. Na ji wadansu har suna cewa an cuce ni, amma gaskiyar zance shi ne, ba wanda ya cuce ni. Mukamin da nake rike da shi a yanzu sai da na amince na karbe shi kuma zan iya samar da ci gaba daga wannan bangare, ba lallai sai na riki wani mukamin gwamnati na daban ba.

Sai dai bayan dukkan alkawuran da jam’iyyarku ta APC ta yi na samar da sauyi mai ma’ana, al’umma na ci gaba da korafin rashin ganin abin da suka yi tsammani. Yaya kake ji game da haka?

Idan akwai masu korafi kamar na yunwa a yau to za ka samu matsalar tun a baya  aka kafa tubalinta. Ba za ka yi korafin abu ba alhali ba ka fuskanci hanyar magance shi ba. Misalin  da zan ba ka shi ne, gwamnati mai ci ta yi amfani da sashin noma a matayin hanyar bunkasa al’umma fiye da kowace gwamnati. A baya-bayan nan, na ji Shugaban Kungiyar Manoman Shinkafa yana cewa manomanta ba su wuce miliyan 5 ba a baya, amma a yanzu sun kai miliyan 13 kuma samunsu a kullum karuwa yake yi ba raguwaa ba. Muna da rarar filin noma a kasar nan saboda har yanzu ba a kai ga amfani da kashi 87 a cikin 100 na fili a kasar nan ba, shin me muke jira?

Kowa ya saki jiki kawai sai aikin gwamnati, sannan gwamnatocin jihohi sun sa ido a kan kudin mai da ake ba su duk wata, alhali bukatar man nan ba mai dorewa ba ce. Gwamnatoci a baya sun ki bunkasa bangaren. Kudin da ake warewa don aikin tituna sai dai a yi watandarsu, wannan fa shi ne tsarin PDP. Kowa ya ga sauyi a yanzu kuma Shugaban Kasa Buhari na samun nasara a kai. Sai dai alfanunsa ba abu ne da zai samu a lokaci guda ba, sai an nuna hali na sadaukarwa.

Gwamnatin nan ta samu nasarar zabe ne kan tsammanin za ta magance matsalar tsaro, sai dai har yanzu ba a kai gaci ba. Sannan ta gaza daukar matakan sallamar hafsoshin tsaro ko magance takaddama a kan daukar karin ’yan sanda. Yaya abin yake?

Maganar takaddama kan daukar karin ’yan sanda tana gaban kotu, ita ce kadai za ta iya tabbatar da ko shugaban ’yan sanda ne ke da hurumin daukar karin ma’aikata ko kuma hukumar da ke kula da su. Sai dai ba ina nufin ba inda ake da matsalar rashin da’a a gwamanti ba ne, wannan abu ne da ba za ka iya kawar da shi gaba daya ba. Amma dai ka sani, ba ka raba hukuma da ka-ce-na-ce. Maganar hafsoshin tsaro kuma ba bangare ne da irina, irinka zai rika katsalanda a kai ba, wannan kebabben hurumi ne na Shugaban Kasa. Shi ya nada su kuma shi ne kadai ke da ikon nada wadanda ke kan mukamin kuma ya san abin da yake yi da yadda ake yi.

Ai ya riki mukamin kwamandan rundunoni uku daga cikin hudu da ake da su. A tarihi ba wanda ya taba rike wadannan wuraren duka. An yi masa shaidar kasancewa kwararre a tsarin dabarun soja. Ya halarci Yakin Basasa daga farkonsa har karewarsa, inda ya mamaye wurare da dama. Ya riki mukamin Gwamna na daukacin jihohin Arewa maso Gabas din nan. Ya yi Minista na shekara uku kuma mamba a Majalisar Koli ta Soja sannan ya riki Shugaban Kasa na soja a baya. Ya fi kowa sanin dalilin da ya ajiye su a wajen. Ni na ji dadin abubuwan bajinta da suka yi. Misali, ka dubi masana’antar soja ta Kaduna da a baya ta takaita wajen aikin kafinta kawai, amma a yanzu ga shi tana kera motocin yaki da sauran kayan yaki na soja. Wannan ba karamin abin alfahari ba ne. Ga kuma takwarorinsu na sama da na ruwa duk suna abin alfahari.

Akwai hasashen cewa zai yi wuya Jam’iyyar APC ta kai ga bantenta bayan wa’adin Shugaban Kasa Buhari, sakamakon yadda abubuwa ke tafiya a jam’iyyar. Me za ka ce?

Bari in gaya maka, jam’iyya ai taron jama’a ce kuma ba ka raba jama’a da rashin daidaituwa a kan wani ra’ayi saboda haduwar al’umma daban-daban ne a cikinta. Ana dariya ana rigima ana kuma kuka, siyasa ta gaji dukkan wadannan. Ina tare da Shugaban Kasa Buhari tun shekarar 2003, a lokacin da aka ba mu kuri’a miliyan 12 a zabe, Aka ba mu kuri’a miliyon 6 a 2007, sai dai mun san cewa magudi aka yi mana, don mun samu sama da haka, kamar yadda marigayi Shugaban Kasa Umaru ’Yar’aduwa da kansa ya furta. A shekarar 2011, an ba mu kuri’a miliyan 12. Sannan muka yi maja a shekarar 2013 don fuskantar PDP a zaben 2015, inda muka samu nasara da kuri’a miliyan 15. Haka a shekara ta 2019 muka sake samun kuri’a miliyan 15 da doriya.

To tunanin da masu hasashen nan ke yi shi ne, idan ya kammala wa’adinsa zai tafi da wadannan kuri’a da ya samu. A baya sun yi yunkurin hallaka shi don kawar da tasirinsa, ta hanyar kai masa harin bam amma Allah Ya kubutar da shi. Sannan kamar yadda ake fada, sun sa masa guba, Allah Ya kare shi bai mutu ba. Ka san ya kamu da rashin lafiya ya yi jinya a Landan, mutane da dama suna da ra’ayin cewa guba aka sa masa. Sannan suka zo suna cewa ai ba Buharin ainihi ba ne, Buharin da ake gani wani Jibrin ne daga kasar Sudan. Sun yi haka ne don kawo rudu a cikin al’umma tare da jawo shubuha a kan kasancewarsa, amma ba su samu nasara ba. To a yanzu sun zo da sabon abu na cewa idan ya kare wa’adinsa zai tafi da kuri’unsa. Sai dai gaskiyar al’amari shi ne, ai a shekarar 2003 ba shi ne Shugaban Kasa ba, haka a 2007 da 2011.

To me za ka ce idan wannan hasashen daga cikin ’ya’yan Jam’iyyar APC ne yake zuwa kamar yadda a baya-bayan nan Gwamnan Ekiti ya fada?

Ba wannan matsala a jam’iyyar. Dole ne a yarda da rabe-raben ayyuka. Muna da shugaban jam’iyya. Babban abu da mutum zai ce shi ne ba ya sonsa, sai dai hakan ba hujja ba ce ka ce shi ke nan ba ka son shugaban jam’iyya dole ya sauka daga kan matsayinsa, alhali akwai hanyar da doka ta tsara shi ne hanyar taron zabe na jam’iyya na kasa. Idan lokacin ya zo wadanda ba su sonsa za su iya amfani da wannan dama su kawar da shi ta hanyar kuri’a, shi ke nan. To a wane dalili ne za a ce Jam’iyyar APC tana da matsala? Ba wata matasala a jam’iyyar. Shin akwai jam’iyyar da za ta bugi kirji ta ce ba wani cece-ku-ce a cikinta? Na takaita maka lallai Shugaban Kasa Buhari ba zai tsaya takara ba, amma zai ci gaba da kasancewa uban jam’iyyar bayan wannan lokaci.