Da Dumi Dumi

Dalilin da na kafa gidauniyar taimakon al’umma – Fatima Jajere

Fatima Jajere tana ba da tallafin kayan asibiti
Fatima Jajere tana ba da tallafin kayan asibiti

Wata ’yar kasuwa kuma ’yar siyasa a Jihar Yobe Hajiya Fatima Isa Jajere, ta ce ta kafa gidauniya don taimakon al’umma ne bayan rasuwar mijinya inda ta sanya wa gidauniyar sunan F-Jajere Foundation don taimakon marasa galihu.

Hajiya Fatima Jajere, ta bayyana wa Aminiya cewa barinta da marayu biyar da mijinta ya yi, kuma ba ta da kowa sai mahaifiyarta, hakan ya zaburar da ita wajen kafa gidauniyar don taimakon marasa karfi.

Ta ce, ayyukan Gidauniyar F-Jajere Foundation ba su tsaya a garin Jajere ko Jihar  Yobe kadai ba, sun hada har da wasu jihohi,  inda ta ce a kwanakin baya ta hada lauyoyi bakwai zuwa gidan fursuna na Goron Dutse da ke Jihar Kano, inda ta fitar da daurarrun mata masu yawa, ciki har da wadda ta haddace Alkur’ani a gidan kurkukun.

A cewarta,  ita da kanta take tafiyar da harkokin gidauniyar, daga ribar da take samu a kasuwancinta. Sai dai yanzu tana son jawo gwamnatin Jihar Yobe ciki.

Ta ce yanzu haka tana shirin tara mata 100 wadanda mazansu suka rasu a dalilin rikicin Boko Haram da kuma gwagware daga kananan hukumomi hudu na yankin Potiskum, don koya musu sana’o’i da suka hada da dinki da tuyar waina da sana’ar karago da sauransu, inda ta ce za a ba su jarin Naira dubu 10  kowaccensu a matsayin abin dogaro.

ADVERTISEMENT

Hajiya Jajere ta ce, Gidauniyar F-Jajere Foundation, za ta nemi gwamnatin Jihar Yobe ta saka wa mata da suka zabe ta,  sakamakon yadda ta ce, gidauniyar ta kira matan wajen su fito su zabi gwamnatin, tare da yi musu alkawarin cewa idan aka ci zabe aka kafa gwamnati za a taimaka musu, kuma yanzu haka akwai mata fiye da dubu takwas da suka yi rajista da gidauniyar.

Baya ga taimaka wa mata tana kuma ba da gudunmawar magunguna da kayan asibiti daban-daban da litattafan karatu ga wasu makarantun gwamnati da na al’umma a sassan jihar.

Daga nan sai ta ce za ta karfafa wa mata gwuiwa wajen fitowa da kayayyakin da suka koya a karkashin Gidauniyar F-Jajere Foundation don ta saya ta kuma kawo masu saya don nuna musu cewa wannan kayayyakin da suka yi masu muhimmanci ne kuma za a rika saye.

Share