✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dalilin da na kafa Kungiyar Uwa Tagari – Maryam Mai Hange

Hajiya Maryam Adamu Mai Hange ita ce Shugabar Kungiyar ‘Uwa Tagari’ mace ce mai kazarkazar wajen neman ilimi da tallafa wa marayu ta hanyar  ba…

Hajiya Maryam Adamu Mai Hange ita ce Shugabar Kungiyar ‘Uwa Tagari’ mace ce mai kazarkazar wajen neman ilimi da tallafa wa marayu ta hanyar  ba su tallafi don su rike kawunansu. A zantawar da ta yi da Aminiya, ta yi bayani kan yadda ba da taimako ke da muhimmanci a rayuwa da yadda take hada ayyukan gida da na kungiyarta:

Tarihina a takaice

Sunana Hajiya Maryam Adamu Mai Hange. An haife ni a garin Jimeta a 1962, kuma na girma a Jimeta. Allah Ya hada ni da miji mai tausayi kuma ina jin dadin zama da shi. Na dauki lokaci a cikin gidansa ban haihu ba, amma daga baya Allah Ya albarkace ni da ’ya’ya, yanzu ina da ’ya’ya uku, biyu mata da namiji daya kuma biyu sun rasu. Ni ce ’ya ta 11 a wajen iyayenmu kuma ’ya ta uku a wajen mahaifiyata. Sunan mahaifiyata Fadimatu sunan mahaifina Alhaji Ahmadu Baba Numo. Na  tashi ban yi karatun boko ba saboda iyayenmu a da ba su damu da karatun mata ba. Suna ganin kamar karatun boko ba ya da amfani a wajen ’ya mace. Amma duk yayyena maza sun yi karatu kuma sun zama manyan mutane. Domin a cikinsu akwai Usman Ahmed Dada wanda ya kai matsayin Babban Sakatare.

Amma da na girma sai na ga cewa karatun nan yana da amfani a wajen mace. Na shiga tunanin abin da ya kamata in yi domin samun ci gaban al’umma musamman mata.

Ina ganin yadda mata ke wahala da yadda maza ke barin matansu suna wahala, hakan ya sanya ina son taimaka musu amma ga shi ban yi karatu ba. Kuma ina son samun matsayi a gwamnati ta yadda zan taimaka musu, don haka ana bude makarantar yaki da jahilci na shiga a Nafan Accademy. Ina daya daga cikin daliban da ake shirin ba su shaidar kammala karatu.

A makarantar na shawarci matan da muke karatu da su kan ina son bude kungiya, sai suka ce dama abin da ake bukata ke nan, kuma za su ba ni goyon baya. A haka na zo na kafa kungiyata, yanzu haka kungiyar mai suna  ‘Uwa Tagari’ ta yi shekara tara da kafa ta.

Alhamdulillahi Allah Ya taimake ni na yi abubuwan da na kwadaitu in yi ga mata .A kowace shekara ina tallafa wa marayu 64. Kuma ni nake yi da kai na ba wai a asusun matan da muke tarawa ba. Bayan haka, ina zuwa asibiti, ina dan sayi omo da sabulu ina ba su. A cikin matan da muke tare da su idan na ga wadda take wahala sosai sai in tambaye ta kan wani irin aiki take ganin za ta iya yi.  Duk abin da suka ce sai in ba su kamar Naira 5,000 in ce ta dawo da Naira 5,500 cikin wata biyu domin a sake bai wa wata ita ma ta yi sana’a.

Maigidana yana taimaka mini sosai, akwai lokacin da ya dauki nauyin mata a wata uku yana biya musu kudin makaranta. Kuma yana tallafa mini a bisa kokarin da nake yi.

Burina lokacin da nake karama

Tun ina karama ina da burin gina masallaci amma har yanzu Allah bai nufe ni da yin hakan ba har ’yar uwata ta riga ni ginawa. Har yanzun ina da burin yin haka kuma ina rokon Allah Ya kara buda mini domin cimma wannan buri. Ina son in ga Allah Ya ba ni damar kara taimaka wa marayu. Marayu 64 da nake taimakawa kowace shekara, ina son in ga na rubanya zuwa kamar 200 duk shekara domin tausaya musu da nake yi.

Kalubale

Babu wani kalubale amma aiki da mata akwai wahala. Mutane na zuga mijina game da aikin tallafin da nake yi. Amma yana ba ni goyon baya dari bisa dari. Babban kalubalen dai shi ne muna bukatan tallafi a wannan kungiya domin tunda muka kafa kungiyar babu wanda ya taba ba mu tallafi sannan mutane da dama na bukatar mu taimaka musu.

Nasarori

Alhamdulillahi, na samu nasara, duk ranar da na kira taro yadda nake ganin mata na halarta ni kaina abin yana ba ni mamaki. Sai a ga kamar bikin rantsar da Gwamna za a yi.  Allah Ya daukaka kungiyar, sai dai akwai masu yi mana alkawari suna cewa za su taimaka amma babu labari. Akwai wani dan siyasa da ya ce zai taimaka mana, muna nan mun zuba ido, kuma muna fata Allah Ya ba su ikon tallafawa.

Shawara daga mahaifiyata

Mahaifiyata ta rasu lokacin ban wuce shekara 12 zuwa 13 ba, takan ba ni shawarar kan kula da duniya kuma idan an bata min in bar mutum da Allah. Kuma tana yi mini nasiha tare da roka mini Allah Ya ban miji mai tausayi da imani. Domin ba zan manta ba, a daren da mahaifiyata za ta rasu, ranar Talata da asuba na fita zan je in yi alwalla ta kira ni,  ta ce Allah Ya rufa mini asiri, Allah Ya sa in kare da duniya lafiya kuma Allah Ya ba ni miji mai tausayi da imani, wannan addu’ar tana raina. Duk ranar da raina ya baci sai in tuna da ita. Kuma wannan shawara da addu’ar na dora ’ya’yana a kai domin gamawa da duniya lafiya.

Tufafi

Na fi son sanya dogayen riguna atamfa marasa nauyi.

Hutu

Ina motsa jiki idan babu bin da nake yi. Domin shekaru sun tarar da ni yanzu. Ina bukatar kula da lafiyata.

Halayen mahaifiyata da na dauka

Mahaifiyata mace ce mai hakuri. Don da wayona na san irin abubuwan da suka faru da ita da kuma irin hakurin da take yi. Ina ganin na dauki halayen mahaifiyata ce.

Abinci

Ina son shinkafa da wake

Yadda nake hada ayyukan kungiya da kula da gida

Ayyukan kungiya dai suna zuwa lokaci-lokaci ne ba abin da ake yi ne kullum ba. Don haka ina farawa ne da kula da mijina tukuna. Idan na hada masa abincin kari, sai in duba in gani,  ko ina da wani aikin kungiya sai in fita. Kuma a gaskiya babu takurar da nake samu a haka.

Halayen maigida da suke burge ni

Dukan halayensa na burge ni, saboda akwai tausayi akwai kuma imani. Kuma babu wanda bai san halinsa ba. Idan har na yi laifi ina tunanin yadda zan fito masa da zance, shi da kansa zai fada mini sai ya ce ina jin kunyarki. Idan na ce zan yi miki fada idan na ganki sai in ji kunyarki. Ni kuma daga nan sai in ce cikin raha ai Allah ne Ya dora ni a kanka. A halin yanzu mun fi shekara 30 da aure.

Shawara ga ma’aurata

Aure babban abu ne, babu abin da ya fi aure. Yana da kyau mace ta rika kula da mijinta da ba shi darajarsa da abin da yake so. Wadnda suke tunanin aure su sani cewa wannan abu ne da za su yi na dindindin. Misali ka ga mun fi shekara 30 da shi, amma ba a jin kanmu. Don haka hakuri shi ne zaman aure. Idan aka yi hakuri sai a zo kuma kowa yana tunanin guzurin lahirarsa. Idan ’ya’yanka suka girma su ma za su so su yi irin zamantakewar da iyayensu suka yi don haka yana da kyau mu kasance masu hakuri tare da aikata abu mai kyau.

Shawara ga matasa

Matasa su kula da kansu domin rayuwar yanzu akwai matsaloli. Matashiya ta mayar da hankalinta ta natsu sannan ta san me take yi. Idan ta natsu kuma ta san me take yi, a nan Allah zai ba ta mijin da take son ta aura. Mace ya kamata ta kama kanta sannan ta san irin suturun da za ta rika sanyawa. Matasan yanzu a bar shaye-shaye. Allah Ya tsare su Ya kuma kare su domin su ne manya a gaba.

Abin da nake so a tuna ni da shi

Ina son a tunani a matsayin mace mai tausayin marayu. Kuma  a tuna da cewa ina da hakuri, domin kuwa akwai abubuwa da yawa da ake yi min ina hakuri da su. Sannan a san cewa ko da zan rasa komai amma zan bai wa maraya tallafi. Saboda rayuwar da muka shiga wannan shekarar duk rabin abin da nake da shi na sayar na saya wa marayu kaya. Saboda na san Allah ne Mai bayarwa. Ina da tausayin wannan abin a cikin zuciyata. Domin abin da ka bada shi ne naka.