✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dalilin da na kafa makarantar Al-Iman – Amina Shu’aibu

Hajiya Amina Shu’aibu ita ce Shugabar Makarantar Al-Iman da ke Yola. Mace mai tausaya wa marayu da talakawa don ganin sun samu ilimin addini da…

Hajiya Amina Shu’aibu ita ce Shugabar Makarantar Al-Iman da ke Yola. Mace mai tausaya wa marayu da talakawa don ganin sun samu ilimin addini da na boko a saukake. Malama ce a bangaren addini da harshen Larabci. A zantawarta da Aminiya, ta bayyana sirrin zaman gidan aure da yadda sababbin ma’aurata za su tafiyar da al’amuransu.

Tarihina

Sunana Hajiya Amina Shu’aibu. Ni haifaffiyar Adamawa ce, an haife ni  a 13 ga Afrilun 1963 a kauyen Digil da ke Karamar Hukumar Mubi ta Arewa a Jihar Adamawa. Na kasance ’ya ta biyu a cikin 10 da mahaifana suka haifa. Iyayena su ne Malam Muhammad Bello da Hajiya Fatima Bello mutane ne da suka fi karfafa sanya mu a makarantun addini hakan ya sanya suka sanya a Firamaren  FOMWAN bayan na gama firamaren suka sanya ni a Makarantar Nazarin Addinin Musulunci (HIS) a nan Jihar Adamawa inda na samu ilimin Alkur’ani da Hadisi da sauran fannoni. Allah Ya albarkace ni da ’ya’ya hudu. Wannan shi ne takaitaccen tarihina.

Burina lokacin da nake karama

Alhamdulillahi! A lokacin da nake karama ba ni da wani buri illa in zama malamar makaranta. Ina sha’awar in ga na fahimtar da yara game da ilimin addinin da na samu. Sai ga shi yau da gobe na kasance mai makaranta. Da na lura makarantun kudi sun yi tsada dan talaka ba zai iya kai dansa ba saboda yawan kudin da ake sanyawa, ya sa na tausaya wa masu karamin samu da kuma marayu na bude makarantar ilimin addini da boko domin su samu sauki a al’amuransu.

Kalubalen rayuwa

Kafin in bude makarantar na dan fuskanci kalubale game da wanda na baiwa rikon makarantar. Na sanya kudi an kafa makaranta sai daga baya kuma na ce zan dora shi a kan albashi ya ce in bari. Bayan makaranta ta girma sai ya nemi mu raba ribar tare. Hakan kuma ba abu ne mai yiwuwa ba. Na ce sai dai in dora shi a kan albashi, domin na sanya kudi mai yawa wajen kafa wannan makaranta. A takaice na fuskanci matsala sosai har sai da muka nemi jami’an tsaro inda suka kwatar min hakkina, sannan na sallame shi.

Nasarori

Na samu nasarori da yawa domin yau ga shi na yi shekara goma da bude makarantar Al-Iman. Ni a wajena ina ganin wannan babbar nasara ce gare ni.

Shawarar mahaifiyata da ba zan manta ba

Shawarar da nake rike da ita wacce har yanzu ban manta ba, ita ce, lokacin da za a kai ni gidan miji. Da na zauna a gabanta ta ce mini, “To yau ke ma Allah Ya sa za ki tafi dakinki. Shawara gare ki ita ce ki rike uwar mijinki kamar ita ta haife ki. Ko ruwan zafi in kika zuba ki sa mata da rabonta. Domin mahaifiyar miji mahaifiyarki ce kuma yadda kike sona haka za ki so ta. Insha Allahu idan kika bi wannan shawarar ba za ki samu damuwa ga uwar miji ba.” Gashi ta haife mu mu mata biyar kuma duk a cikinmu babu wadda ta samu matsala da uwar miji, alhamdulillah.

Tufafi

Na fi sha’awar sanya atamfa domin rashin nauyinta ga kuma sakewa babu wani takura.

Hutu

Idan ba na komai gaskiya ina bude takardu in kara ilimi. Asabar da Lahadi muna zuwa FOMWAN karatun Kur’ani da Hadisi da   Fikihu da  sauransu. Ko ba na komai ina so dai in ga na bude wani littafi domin karin ilimi.

Abinci

Na fi sha’awar cin tuwo. Idan dai tuwo ne ko da wace irin miya, ina maraba da shi.

Yadda nake hada aikin gida da na makaranta

Da farko dai da aikin gida nake farawa idan na tashi da safe na kammala girke-girkena da kuma gyaran gida, a daidai lokacin da

a makarantar an tashi hutawa sai in shiga makarantar inda zan zanta da malaman game da mafita da kuma duba yadda ake tsabtace makarantar hatta ban- dakunan yara nakan shiga domin ganin ko ana wanke su yadda ya kamata. Idan da bukatar mu sayi littattafai ko wasu abubuwa sai mu yi.

Shawara ga matan aure

A lura da yara musamman matan auren da ba su dade a gidan mazansu ba. Kasancewar yaran kanana ne suna bukatar kula sosai domin samun tarbiyya, sannan suna son a sa su a jiki (goyo). Domin idan ka sa yaro a jiki, ko zazzabi ya yi za ka gane. Sannan idan yaro yana tare da uwa, tarbiyyar da uwa za ta yi masa babu wanda zai iya yin irin nata. Idan yaro ya shaku da kai idan akwai abin da ya canja ga yaro mahaifiya za ta gane. Idan ba a shaku da yaro ba, sai an fita, yaro ya tafi makaranta ya dawo, ba a san cinsa ba, ba a san shansa ba. Ko akwai abin da ke damun yaro ba za a gane da wuri ba. Amma idan aka sa shi a jiki, ko mura in ya kama yaro za a gane ballantana zazzabi mai tsanani.

Zaman aure zama ne na hakuri, kada a sakar wa mai aiki komai. Idan maigida ya kawo cefane, dole ne ki sa ido ki ga me aka kawo kada ana sake wa mai aiki komai domin mazanmu amana ne gare mu. A rike makullin wajen adana abinci, saboda gudun masu dauke-dauke.

Shawara ga matasa

Matasan yanzu, musamman ’ya’yanmu Musulmi, iya shawarar da zan ba su ita ce, su tsaya su yi karatu. Idan ka tsaya ka yi karatu, za ka samu rufin asiri. Sannan ko mutum yana son taimaka maka akwai hanyar da zai taimaka maka. Amma idan ba ka yi karatu ba, ko mutum yana son taimaka maka ba ya iya taimaka maka. Matasa a zage dantse a yi karatu domin samun rufin a siri. Sannan akwai wadanda suka mayar da shaye-shaye kamar ado. Wannan ba abu ne mai kyau ba. Allah Ya tsare su da shi wanda yake yi kuma Allah Ya shirya shi. A rike addini a yi karatu. Gaba su muke tsammanin su zama dattawa. Kada su yarda su bata rayuwarsu domin a gaba su za su zama manyan gobe.

Kasar da ke burge ni

Babu kasar da ke burge ni irin kasar Saudiyya. Domin idan ka je za ka yi ibada sannan za ka ji kamar numfashinka ne ya raba ka da Aljanna. Don haka babu kasar da ta fi burge ni kamar Saudiyya. Bayan haka kuma idan ka je Madina, za ka ga inda Manzon Allah (SAW) ya kwanta wannan ma alhamdulillahi abin jin dadi ne da kara imani.

Macen da nake koyi da ita

Matar da nake koyi da ita, ita ce Nana A’isha matar Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam). Ya aure ta tun tana karama sai ga shi ta bayar da ilimi mai yawa da bai misaltuwa.

Abin da nake son a tuna ni da shi.

Abin da yake boye ba za ka sani ba sai Allah sai kuma wadanda suke boye. Amma na san ba za a manta ni ba domin kafa wannan makarantar  daga firamare har sakandare. Kuma na san za a tuna ni a matsayin wadda ta tausaya wa talakawa da marayu wajen bude musu makaranta  don samun ilimin addini da na boko.