Notice: Undefined index: show_thumbnails in /var/www/html/am20pow/wp-content/plugins/jetpack/modules/related-posts/jetpack-related-posts.php on line 199

Notice: Undefined index: show_headline in /var/www/html/am20pow/wp-content/plugins/jetpack/modules/related-posts/jetpack-related-posts.php on line 200
Dalilin da na koma PDP – Maman Taraba - Aminiya
Aminiya

Dalilin da na koma PDP – Maman Taraba

Sanata Jummai Alhassan wadda aka fi sani da Maman Taraba ta canja sheka daga Jam’iyyar United Democratic party (UDP) zuwa Jam’iyyar PDP.

Maman Taraba wacce ta shahara a fagen siyasa a Jihar Taraba da kasa baki daya, ta rike mukamin Minista a karkashin Gwamnatin Muhammadu Buhari, kafin ta bar Jam’iyyar APC.

Sanata Jummai Alhassan ta bayyana canja shekar ta ce da magoya bayanta, a wani taro a Jalingo da ta gudanar tare da ’ya’yan Jam’iyyar UDP daga mazabu 168 da ke a jihar, inda ta ce kashi 80 na magoya bayanta da suke cikin Jam’iyyar UDP sun amince  su koma Jam’iyyar PDP.

Sanata Jummai Alhassan ta kara da cewa bayan kammala zaben bana an kafa wani kwamiti a karkashin jagorancin Alhaji Abdulmumini Baki, daya daga cikin manyan ’ya’yan Jam’iyyar UDP domin zaga daukacin mazabun jihar 168 ya ji ra’ayoyin ’ya’yan jam’iyyar kan wace jam’iyya ya kamata su koma.

Ta ce bayan kammala jin ra’ayoyin ’ya’yan jam’iyyar ce, sai sakamako ya nuna ra’ayin  mafi yawansu ya karkata ne ga a koma Jam’iyyar PDP .

ADVERTISEMENT

Sanata Jummai Alhassan ta ce ita ce ta ji dadin ganin cewa magoya bayanta ba su nemi a koma Jam’iyyar APC ba.

Ta ce ita ta bunkasa Jam’iyyar APC a Jihar Taraba har ta samu nasara a lokacin zaben shekarar 2015 amma daga bisani bayan jam’iyyar ta samu karbuwa a jihar aka yi mata kora da hali wanda ya sa ta fice  daga Jam’iyyar APC ta koma Jam’iyyar UDP.

Ta kara da cewa rashin adalci da kama karya na Shugaban Jam’iyyar APC na Kasa ya sa ta fice tare da magoya bayanta zuwa Jam’iyyar UDP.

Ta ce yanzu kuma magoya bayanta sun nuna cewa suna bukatar  su koma Jam’iyyar PDP.

Ta bayyana cewa za ta taimaka wajen gina Jam’iyyar PDP a Jihar Taraba.