✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dalilin da na zabi surukina don ya zama Gwamnan Kano – Kwankwaso

Za mu hadu da su a zaben fid-da gwani-Tsohuwar PDP A ranar Asabar da ta gabata ce kafar labarai ta Daily Nigerian ta ce tsohon…

Za mu hadu da su a zaben fid-da gwani-Tsohuwar PDP

A ranar Asabar da ta gabata ce kafar labarai ta Daily Nigerian ta ce tsohon Gwamnan Jihar Kano Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya zabi surukinsa kuma tsohon Kwamishinan Ayyuka a zamaninsa, Alhaji Abba Kabiru Yusuf domin yin takarar Gwamnan Jihar a karkashin Jam’iyyar PDP. Washgari kuma jaridar ta ruwaito cewa Kwankwaso ya kuma zabi wadansu surukansa biyu Mukhtar Yarima don takarar Majalisar Wakilai daga Tarauni da Nasiru Sule Garo a mazabar Gwarzo/Kabo tare da amincewa surukin Shugaban Riko na PDP a jihar kuma na hannun daman Kwankwaso Rabi’u Sulaiman Bichi, mai suna Munir dahiru ya tsaya takarar dan Majalisar Wakilai daga Dawakin Tofa/Tofa/Rimin Gado.

Sai dai da yake kare wannan salon a tuwona maina da ake zarginsa da yi Sanata Rabi’u Kwankwaso ya ce ya yi haka ne domin gudun kada a maimaita abin da magajinsa Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya yi musu na cin amana.

A hira da ya yi da BBC, Kwankwaso ya ce a shekarar 2015 sun duba mutumin da ya fi kowa shekaru da girma da mukami wajen tsayar da shi dan takarar Gwamnan Jihar Kano, inda suka ba wa Ganduje, bisa zaton za a zauna lafiya ba za a yi butulci da cin amana ba, kuma za a yi wa jama’a aiki amma sai suka samu sabanin haka.

Sanata Kwankwaso ya ce bayan nazari da tuntuba da shawara da suka yi da mutane da dama tsawon shekara uku da doriya domin duba wanda ya kamata su tsayar a takara ba tare da an sake maimaita abin da ya faru ba ne aka amince Abba K. Yusuf ne ya fi dacewa.

Sanatan ya ce wanda suka yanke shawarar tsayarwar shi ne Kwamishinan Ayyuka a wa’adin gwamnatinsa na biyu, shi ne ya jagoranci dukan ayyukan ci gaba da aka yi a jihar da suka hada da gadojin sama da na kasa da sabuwar Jami’ar Jihar (North-West a da) da manyan makarantun jihar da rukunan gidajen da a da ake kira Kwankwasiyya da Amana da Bandurawo.

Sanata Kwankwaso ya ce yana bakin cikin watsi da gwamnatin jihar ta yanzu ta yi da wadannan ayyuka, amma Abba ya fi shi bakin ciki a kai, don haka yana ganin idan har ya samu hawa kujerar Gwamna za a raya wadannan ayyuka, a kuma dora a kai.

Game da cewa ya tsayar da Abba ne saboda surukinsa ne, sai ya ce ba ’yarsa da ya haifa Abban yake aure ba, amma gidansu babban gida ne kuma gidan sarauta yana da dangi da ’yan uwa da iyaye mata da ’ya’ya da jikoki, “Ba za ka hana wani ya ce yana so zai aura, kuma idan wani ya aura daga ciki ba za ka ce da shi a’a me ya sa ka aura ba. Kuma wannan bai kamata ya zama wata matsala a cewa wanda ya yi aure a cikin family (iyali) dinka ka ce wata dama ta zo za ka hana shi, abin da ba a so shi ne ka fitar da shi kan son zuciya, amma babban abin da yake akwai shi ne kowa ya san halinsa kowa ya san aikinsa, to wannan su ne ginshikai,” inji shi.

Dangane da zargin cewa wanda ya tsayar takarar ba ya da farin jini, ba a san shi sosai ba, kuma yana da girman-kai, sai Sanata Kwankwaso ya ce lamarin ba haka yake ba, a cewarsa Abba aikinsa kawai yake sanyawa a gaba, mutum ne da ba za ka gan shi a wuri na assha ba, saboda haka abin da ake so shi ne aiki da rike amana da gaskiya da sauran abubuwa da za su taimaka wa Jihar Kano.

Kan hana Farfesa Hafizu Abubakar takarar kuwa Sanata Kwankwaso ya ce, ya san tsohon Mataimakin Gwamna Farfesa Hafizu Abubakar sama da shekara 40.

Kuma duk wata dama da ya samu ta ya taimaka masa ya taimaka masa kuma zai ci gaba da taimaka masa, ba fada suke yi ba, ya ce, amma abin da aka ce da shi, shi ne ya nemi kujerar Sanata da Kwankwason yake kai a yanzu, amma Farfesan bai nuna sha’awa ba, kamar yadda Malam Salihu Sagir Takai, aka nemi ya yi takarar Sanatan Kano ta Kudu amma ya ki.

Ya ce maganar da wadansu ciki har da wadansu da aka ce ’yan Kwankwasiyya ne ke yi cewa matakin da suka dauka na tsayar da Abba Kabiru Yusuf takara zai ba wa Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na APC damar cin zabe a saukake, ya ce wannan sharrin makiya ne, kuma idan ma wadansu nasa sun fadi hakan to ai ba su ne mutanen Kano ba.

Bayanai sun ce Farfesa Hafiz ma ya yanki fom din takarar Gwamnan don fafatawa da surukin Gwamnan a zaben fitar-da-gwanin na PDP. Kamar yadda Alhaji Salihu Takai ya yanka don fafatawar da shi.

Wannan fitar da ’yan takarar da Sanata Kwankwaso ya yi ta jawo cece-kuce a tsakanin al’ummar Jihar Kano inda wadansu ke wa lamarin kallon son kai ko karfa-karfa da ake son yi wa Jam’iyyar PDP.

Sai dai SakatarenTsare-Tsare na Jam’iyyar PDP Sanusi Surajo Kwankwaso ya yi wa Aminiya karin haske a kan batun inda ya ce ba wai jagoransu na Kwankwasiyya ne ya fitar da ’yan takarar ba, “Kafin a fitar da sunayen sai da jagora ya kira taron wakilan jam’iyya daga dukan kananan hukumomin Jihar Kano, ba kawai ’yan Kwankwasiyya ba har da ’yan tsohuwar PDP. A wannan taro ya bayar da dama ga jama’ar su fitar da ’yan takara su kuma suka fitar da wadancan gwarazan mutane bisa cancantarsu. Sannan aka tura sunayen ga wani kwamitin mutum biyar don kara tantancewa. Kuma da farkon da aka yi wannan aiki an sanya da’yan tsohuwar PDP ciki har da Salihu Sagir Takai. Bayan an yi haka aka sanar da ’yan takarar to a lokacin ne Takai ya ce ba zai karbi takarar Sanata ba ya ce Gwamna ya ke so. A wannan lokaci sauran mutanensa irin su Ali DattiYako suka nuna cewa ba za su bi shi ba inda kuma suka karbi takarar da aka ba su.”

Sakataren ya musanta zargin cewa jagoran nasu ya bayar da takarar ga surukansa inda ya ce “Mutum daya ne jal wanda yake da alakar surukuntaka da jagoran nasu wato wanda aka tsayar takarar Gwamna Injiniya Abba K. Yusuf. Ina so jama’a su fahimci cewa ba an ba shi takarar Gwamna ba ne don yana surukin jagoranmu ba, a’a kowa ya san duk nasarorin da aka samu a mulkin Kwankwaso to da hannun Abba Yusuf a matsayinsa na Kwamishinan Ayyauka a wancan lokaci. Haziki ne, jajirtace ne kuma gwarzo ne kuma ina tabbatar miki mutane sun karbi wannan dan takara.”

Wani jigo a Jam’iyyar PDP, bangaren Alhaji Aminu Wali da ya nemi a boye sunansa ya ce. “Ba mu da matsala da Sanata Rabi’u Kwankwaso, kuma fitar da ’yan takara da ya yi, ya yi ne a radin kansa bai tuntube mu ba. Kamar yadda kowa ya ji a gari mu ma haka muka samu labari, amma duk da haka ba ma kallon lamarin a matsayin abin tashin hankali da zai kawo matsala a tsakaninmu.”

Ya ce sai dai hakan ba zai hana su tsayar da nasu ’yan takarar ba, “Akwai ’yan takararmu da muke da su tun kafin Kwankwaso ya shigo wannan jam’iyya don haka lamarin ba na tayar da jijiyar wuya ba ne. Akwai zaben fid-da-gwani da za a yi nan ba da dadewa. Don haka za mu kawo namu ’yan takarar wadanda za su nemi mukaman tare da nasa ’yan takarar. Abin da za mu ce shi ne Allah Ya ba mai rabo sa’a,” inji shi.