✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dalilin da nake hada walimar buda baki a gida- Yusuf Salihu

Zababban Dan Majalisar Kawo a Majalisar Jihar Kaduna, Yusuf Salihu ya bayyana cewa yana shirya walimar buda baki a gidansa ne tare da mutane domin…

Zababban Dan Majalisar Kawo a Majalisar Jihar Kaduna, Yusuf Salihu ya bayyana cewa yana shirya walimar buda baki a gidansa ne tare da mutane domin nuna jin dadi da dogiya a gare su bisa gudunmuwar da mutanen suka bayar.

Yusuf Salihu ya bayyana haka ne a lokacin taron buda baki da ya shirya wa masu kare muradun Jam’iyyar APC a kafafan sadar da zumunta wadanda ake kira ’yan social media a gidansa, wanda kuma ya zo daidai da lokacin da wasu wadanda suka hada har da ’yan Jam’iyyar suka kai masa ziyarar taya  murna da kuma gabatar masa da kyauta ta musamman a gidansa.

Da yake jawabi a wajen gabatar da kyautar, wani jigo a Jam’iyyar PDP ya bayyana cewa duk da cewa shi dan PDP ne, ya san cewa Yusuf Salihu ya cancanci zama dan majalisar jiha, inda ya kara da cewa ya san inda zababban dan majalisa ya rika taimakon al’umma tun kafin ma ya samu nasara, inda ya bukaci day a ci gaba da taimakon da aka san shi da shi bayan an rantsar da su. Sannan daga karshe ya taya shi murna da kotu da dawo masa da nasararsa, inda ya ce da a ce irinsu Yusuf Salihu ne a tafiyar, da tun tuni sun jawo su tafiyar APC.

Shi ma jagoran tafiyar, Hassan Goma ya bayyana cewa kasancewar ya san Yusuf Salihu tun suna kanana, kuma ya san mutumin kirki ne, shi ya sa ya ga cewa ya dace ya taya shi murnar nasarar da kotu da tabbatar masa.

“Wannan kadan ne. Tun tuni dama nake fata Allah Ya tabbatar masa da nasara, sai kuma kotu tam aka adalci wajen kwato maka hakkinka. Wannan ya sa na gay a dace in zo domin taya ka murna a matsayina dad an uwanka. Alakata da kai ta wuce maganar siyasa ko jam’iyya. Magana ce ta sanin cancantar ka. Kuma na san za ka iya. Sannan kuma ina maka fatan alheri da addu’ar Allah Ya kara daukaka.”

A wajen walimar, an gabatar wa Yusuf Salihu da kyautar gudunmuwar riguna da huluna masu dauke tambarinsa na shirin rantsuwa, inda ya ce, “wannan ne kyauta ta farko da aka ba ni tun bayan da kotu da dawo min da nasarata. Don haka ina godiya da karamci,