✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dalilin da nake so in zama sabon ‘James Bond’

Fitaccen jarumin fina-finan Hollywood Denzel Washington ya fara kamfen don ya zama sabon jarumi James Bond da ke fitowa a fina-finan 007 na Amurka.Jarumin, wanda…

Fitaccen jarumin fina-finan Hollywood Denzel Washington ya fara kamfen don ya zama sabon jarumi James Bond da ke fitowa a fina-finan 007 na Amurka.
Jarumin, wanda ya fito a fim din ‘The Training Day’ yana fatan maye gurbin jarumi Daniel Craig ne don ya zama jarumi bakar fata na farko da zai shiga jerin jaruman da suka amsa sunan James Bond a fina-finan 007.
Jarumin ya fara kamfen din ne a shafinsa na twitter, inda ya bukaci ’yan kallo su taya shi kamfen don ya cim ma burinsa.
Ya ce: “Ya kamata su (furodusoshi) su yi batun sabon jarumin da zai amsa sunan James Bond, ba ni da buri kamar in zama James Bond…Daniel Craig ya yi nasa saura Denzel, ku shiga Twitter ku rika rubuta Denzel sabon James Bond. Ku rubuta James Washington. Denzel Bond! Ku taya ni kamfen.”
Ya ce: “Ina son zama jarumin ne saboda ina rawar da zan taka da za ta burge masu kallo.”
Hakan ya sanya masu kallo suka rika rububin rubuta #DenzelisJamesBond a shafin twitter.