Search
Subscribe
Dalilin da nake son barin Super Eagles – Gernot Rohr

Dalilin da nake son barin Super Eagles – Gernot Rohr

Kocin kungiyar kwallon kafa ta Najeriya, Super Eagles Gernot Rohr ya bayyana dalilan da za su sa ya ki  sabunta kwantaraginsa da Super Eagles idan ta kare a badi.

Rohr ya bayyana haka ne a wata tattaunawa da ya yi da kafar labarai ta Naija News a ranar Lahadin da ta wuce.

Ya ce dalilan sun hada da yadda wadansu ’yan Najeriya ba su gamsu da salon horarwarsa ba kuma suke nuna masa kiyayya da matsalar  shugabanci a Hukumar NFF da kuma yadda Hukumar NFF ta yi masa alkawurra masu yawa amma ta kasa cikawa.

“Alal misali, jim kadan bayan an fitar da Super Eagles a gasar cin Kofin Afirka a Masar, Shugaban NFF Mista Amaju Pinnick ya yi mini alkawarin tura ni kulob din Bayern Munich da ke Jamus don samun horo na musamman, amma har wannan lokaci hakan bai yiwu ba,” inji shi.

Rohr wanda kwantaraginsa zai kare  a badi alamu sun nuna da wuya ya ci gaba da horar da kungiyar ganin yadda kasashe da dama a Afirka suke zawarcinsa ciki har da Maroko da Kamaru da Mali da  Kongo da sauransu.

Duk da nasarar da kocin ya yi na kai Super Eagles gasar cin Kofin Duniya a Rasha da kuma gasar cin Kofin Afirka a Masar da yawa daga cikin magoya bayan kungiyar ba su gamsu da salon horarwarsa ba.

 

 

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin