Da Dumi Dumi

Dalilin da rashin tsaro ke ci gaba a Najeriya duk da lashe Naira tiriliyan 2.02  – Kwararru

Kwararru a fannin satro sun ce matsalar da ta yi katutu a cikin harkar tsaron kasar nan ta wuce batun samar wa soja da sauran jami’an tsaro kudi kawai. Batu ne da ke da bukatar majalisun kasa su zauna su sake sabon lale don samo sahihiyar hanyar warware ta.

Majiyoyin Aminiya da suke cikin hukumomin soja da sauran hukumomin tsaro sun ce karuwar rashin tsaro a kasar nan wata alama ce da ke nuna ya kamata a yi garanbawul ga ayyukan jami’an tsaro na farin kaya (DSS) da jami’an Hukumar Shigi da Fici da sauran  hukumomin tsaro da ayyukansu suka shafi hana aikata laifuffuka a cikin kasa.

Da suke tsokaci game da yawaitar ayyukan ta’addanci da ’yan bindiga masu garkuwa da mutane, wadanda suka yi sanadiyyar mutuwar jama’a da dama, masanan sun ce jami’an soja wadanda aikinsu shi ne tsare kasa daga duk wani farmaki ko barazana da wata kasa ka iya yi ga kasar nan, a yanzu sun sanya hannu dumu-dumu a cikin ayyuka cikin gida wadanda suka kamata a ce ’yan sanda ne ke gudanar da su. Da yake jawabi a Majalisar Dattawa a ranar Laraba, 2 ga Okutoban bana, kan tabarbarewar tsaro a hanyar Kaduna zuwa Abuja, Shugaban Majalisar, Sanata Ahmed Lawan ya bukaci Zauren Majalisar ya binciki yadda jami’an tsaro suke kashe makudan kudaden da ake ba su.

Lawan ya ce “Ya dace mu dubi rahoton Kwamitin Tsaro na Majalisa, sannan ne za mu iya jin ra’ayin mutane a kan harkar tsaro, domin a wannan tafiya ta yanzu kwalliya ba ta biyan kudin sabulu dangane da yadda jami’an tsaro suke gudanar da ayyukansu.”

Aminiya ta gano cewa baya ga matsalar garkuwa da mutane da Shugaban Majalisar ya yi tsokaci a kanta, akwai matsalolin ’yan bindiga da na fadan makiyaya da manoma da fadace-fadacen kabilanci da masu tayar da kayar baya a yankin Neja Delta da uwa-uba matsalar Boko Haram, wacce ta addabi Arewa maso Gabas da jami’an tsaron suke ta fama da su.

ADVERTISEMENT

Wani tsohon soja da muka sakaya sunansa, ya bayyana cewa “Abin takaicin shi ne, yawan sojin da ake da su bai wuce dubu 150 ba don haka zai yi wuya su iya kawar da matsaloln.” Duk da yake shafin Intanet na Rundunar ’Yan sanda bai bayar da sahihin yawan jami’an da take da su ba, majiyarmu ta tabbatarda cewa yawansu bai kai dubu 400 ba. Su kuwa jami’an Shigi da Fici da na Sibil Difens, kowannensu yawansu bai  kai haka ba.

Yayin da a waje daya kuma kididdigar Majalisar Dinkin Duniya ta nuna yawan ’yan Najeriya ya kai miliyan 202 da dubu 363 da 773 wanda hakan na nufin duk dan sanda daya yana kare lafiyar fiye da mutum 500 ke nan.

Adawa da cin hanci na tauye ayyukan jami’an tsaro

Wani tsohon hafsan soja ya ce adawa da juna ne ya hana jami’an hukumomin tsaro yin tsayin-daka don yin yaki cbisa gaskiya don kawar da abokan gaba. Ya ce “Adawar bai ta tsaya a tsakanin hukumomin soja ba, har ta ratsa a tsakanin ’yan sanda da DSS da na Sibil Difens.

“Kowace hukuma tana adawa da ’yar uwarta a kan karfin fada-a-ji, ta haka ne za ka ga hukumomin tsaro suna aiwatar da tarurrukan manema labarai daban-daban a kan wata matsala guda daya. Don haka za ka ga suna satar bayanan juna domin su dakushe kaifin aiki a tsakaninsu. In ba haka ba, ta yaya har jami’an Rundunar Sojin Sama suka saki bama-bamai a garin Rann da ke Arewa maso Gabas, yayin da kuma sojin kasa suke kan aiki a ciki?

Ai ka ga da akwai tuntubar juna a tsakaninsu hakan ba zai faru ba. Sau da dama sojin kasa sukan ce sojin saman sun kasa kawo musu dauki, yayin da su kuma sojin saman sukan ce na kasa ne ba su ba su sahihan bayanai ba,” inji shi.

Haka kuma tsohon jami’in na soja ya bayyana cewa adawar da ta yi katutu a tsakanin jami’an ’yan sanda da na Hukumar Kula da Ayyukan ’Yan sanda ya haifar da dambarwa kan daukar ’yan sanda dubu 10.

Tun a cikin watan Disamban bara Shugaba Buhari ya amince a dauki karin ’yan sandan amma kishi da  adawar da ke tsakanin wadannan hukumomi ya sanya har yanzu ba a kammala aiwatar da haka ba.

Da yake jawabi a gaban Majalisar Dokoki ta Kasa yayin tantance shi don zama Minista, Manjo Janar Bashir Salihi Magashi (mai ritaya) ya ce kirkiro da ofishin Babban Hafsan Tsaro shi ne  ya haifar da hassada da kishi a tsakanin hukumomin soja.

Janar Magashi ya fadi haka ne  lokacin da yake amsa tambayar da Sanata Orji Uzor Kalu na Jihar Abiya ya yi masa game da zargin rashin fahimtar juna da ke tsakanin shugabannin hukumomin soja na kasar nana. Magashi ya ce “Haka ne kamar yadda ka fada, cewa yadda shugabannin tsaro na kasa ke gudanar da ayyukansu akwai rashin jituwa. Hakan ya faru ne tun bayan da aka samar da Babban Hafsan Tsaro.

“Don haka duk wasu ayyuka da za a yi, a ciki da wajen kasa, ana aiwatar da su ne ta hanyar girman kafada. Don haka kamar yadda ka fada, a yanzu shugabannin hukumomin sojan suna kokarin su nuna wa jama’a su ma suna ayyukansu da ba a sani ba,” inji shi.

A kan zargin da ake yi na cin hanci a tsakanin jami’an soja, wata majiyarmu ta shaida mana cewa “Akwai kanshin gaskiya, cewa ana aiwatar da hada-hadar kudi ne a tsakanin gwamnati da manyan jami’an soja kawai.

Soja kuma da suke a bakin daga sai abin da suka gani. Duk da yake hakkinsu ne a ba su kayan aiki da hakkokinsu amma ba su samun abin da ya dace.”

Majiyar tamu ta ce yin sama-da-fadi da ake yi da kudaden da suka kamata a yi yaki da su, shi babban kalubalen tsaron. Wannan ya fito karara a baya-bayan nan da hukumar soja take tuhumar Babban Kwamandan Runduna ta 8, Manjo Janar Hakeem Otiki.

Manjo Janar Otiki ya gurfana a gaban Kotun Soja ta Musamman, inda ake tuhumarsa da karkatar da wasu kudi mallakar rundunar da yake jaogoranta, inda ya sanya aka kwashe kudin daga rundunar kafin daga bisani wadansu kananan sojoji su sace kudin a kan hanyar kai su Kaduna.

Sannan har yanzu ana ci gaba da sauraron karar da ake tuhumar tsohon Mai ba Shugaban Kasa Shawara kan Harkar Tsaro, Sambo Dasuki ga kuma batun tsohon Babban Hafsan Tsaro marigayi Mashal Aled Badeh, kan karkatar da kudin da suka shafi tsaro.

Yadda abubuwa ke gudana a wasu wuraren 

Majiyoyinmu sun ce ayyukan da soja suke gudanarwa sun yi musu yawa a yanzu. Ba ma kamar idan an yi la’akari da wasu kasashe kamar Sudan da Masar, wadanda ba su da yawan jama’a kamar Najeriya amma sojojinsu suna da yawa. Alkalumar kididdigar yawan jama’a na Majalisar Dinkin Duniya sun ce kasar Sudan tana da jama’a miliyan 43 da dubu 99 da 318. Kuma wata cibiyar bincike ta kasar Birtaniya ta ruwaito cewa yawan sojan kasar Sudan sun kai dubu 109 da 300, sauran jami’an tsaro da ba soja ba dubu 17 da 500.

Wani bayani da tashar Talabijin ta CNN ta wallafa a shafinta na Intanet ya ce kasar Masar tana da sojan sama dubu 450, da sojan kasa dubu 320, wanda hakan ya nuna yawan sojan ya dauki kashi biyu bisa uku na jama’arsu a bisa kididdigar  Hukumar Kimiyya ta Amurka.

Kundin bayanai na  Wikipedia ya ce ’yan sandan kasar Masar sun kai dubu 500.

Ita kuwaAfirka ta Kudu tana da yawan jama’a miliyan 58 da dubu 558 da 270 a bayanan da Majalisar Duniya ta fitar amma tana da sojoji dubu 78 da 707 tun a shekarar 2014. Sannan tana da masu jiran-ko-ta-kwana dubu 15 da 107 a wancan shekarar.

Da aka tambaye shi dalilin dambarwar tsaron da take faruwa a kasar nan, tsohon jami’in sojan ya ce, “Babbar matsalar ita ce rashin gaskiya da son kai da kuma son a ci gaba da zama kan mukami da jami’an da ke kan shugabanci suke yi.”

Ya ci gaba da cewa “Shugabannin tsaro suna tsoron su fada wa ’yan siyasa gaskiya don gudun kada a tsige su. Kuma abin ban haushi shi ne duk kudin da ake ba su suna kashe su ne ba ta muhimman ayyukan da suka kamata ba. In ba haka ba, ta yaya ne ana yaki kuma har Rundunar Soja ta samu sukunin gina Jami’a a Biu, sannan kuma suke shirin kara gina wata a Bauchi? Mene ne aikin Kwalejin Kananan Hafsoshin Soja (NDA)?

“Kamata ya yi a ce sun ririta dan abin da aka ba su wajen sayen makamai da biyan hakkokin soja, ba wai gina asibitoci da jami’o’i ba, wadanda ake yi saboda biyan wata bukata ta siyasa a wuraren da ba su kamata ba.”

Ya kara da cewa “Kamata ya yi a ce soja sun sawo kayan yaki kamar na’urorin tone nakiya da MRAP, wadanda su ne ake bukata don cin galabar Boko Haram da sauran ’yan bindiga. Ya kamata a ce ana sayo wa soja makamai ne ba wai motoci kirar Hilud ba. Kuma a samar musu jirage masu kai hare-hare da dare amma ba a yin haka sai dai a yi ta bushasha da kudin da ake ba sojan.”

Ko binciken sanatoci zai haifar da da mai ido?

Zargin da Shugaban Majalisar Dattawa ya yi a baya-bayan nan ba shi ne farkon yunkurin majalisar na gano bakin zaren ci gaba da tabarbarewar tsaro ba. Ko a ranar 16 ga Yulin bana, sai da sanatoci suka amince da wani kuduri da ya bukaci a kira wani taro da zai kawo hanyoyin inganta tsaro a kasar nan.

Shugaban Majalsar Dattawa Ahmed Lawan shi ne ya bayyana haka yayin da yake jawabi kan wani kuduri da Sanata Ayo Akinlure na Jam’iyyar PDP mai wakiltar Ondo ya gabatar kan karuwar matsalar tsaro, bayan hallaka Misis Funke Olakunrin, ’yar Shugaban Kungiyar Afenifere, Reuben Fasoranti.

Lawan ya ce “Akwai abin takaici lura da yadda yanayin tsaro ke kara tabarbarewa a kasa. Kusan duk wani bangare na kasar nan yana da irin kalubalen tsaron da yake damunsa. Kuma hakki ne na sanatoci mu hada kan duk masu ruwa-da-tsaki a harkar tsaro don yin aiki tare domin ganin an kawar da wannan matsala ta tsaro.”

Da yake amsa tambaya ko rundunar soja za ta gabatar da kanta a gaban sanatocin don fayyace yadda take kashe kudin da take karba don gudanar da ayyukan tsaro, Kakakin Hedkwatar Tsaro, Kanar Onyema Nwachukwu cewa ya yi “Ina tabbatar maka in dai an bi hanyar da ta kamata a yi hakan zai yiwu.”

Ya kara da cewa “Na san akwai hanyoyin da muke yin bayanan yadda aka kashe kudaden da aka ba soja kuma su ma masu rike da mukaman siyasar sun sansu.”

Abubuwan da aka yi musu tanadi a baya

Bayanai sun ce a cikin shekara biyar da suka gabata, an kebe wa bangaren tsaro kudi a kasafin a 2016 sun kan Naira biliyan 429.12, a 2017 Naira biliyan 467.12. A 2018 kuma Naira biliyan 580.14. Sannan a bana Naira biliyan 158.11.

Wani tsohon Kanar mai ritaya da yake da ilimin harkokin kudi, ya ce: “Abu ne mai sauki ka san kasafin da ya shigo wa soja saboda yana nan a rubuce wanda aka amince da shi da wanda yake a ofishin Babban Akawu na Kasa. Amma ba su nuna wa kowa, za dai su fada maka cewa ai takardu ne masu muhimmanci.”

Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya