✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dalilin da ya sa aka canja ni a wasa biyu – Ronaldo

Dan kwallon Fotugal da kulob din Jubentus na Italiya Cristiano Ronaldo a ranar Litinin da ta wuce ya bayyana dalilin da ya sa kocin Jubentus…

Dan kwallon Fotugal da kulob din Jubentus na Italiya Cristiano Ronaldo a ranar Litinin da ta wuce ya bayyana dalilin da ya sa kocin Jubentus Maurizio Sarri ya canja shi a wasa biyu da ya yi a makon jiya.

Kocin ya canja Ronaldo a wasan da kulob din ya yi da na AC Milan a gasar Serie A ta Iyaliya wanda hakan ya sa ya bar filin wasan cikin fushi kuma aka yi ta rade-radin zai iya fuskantar dagewar shekara biyu a gasar.  Sannan kocin ya canja shi a wasan da kulob din ya yi da na Lokomotib na Moscow a gasar Zakarun Turai da aka yi a kwanakin baya.

Ronaldo ya ce “Kocin ya canja ni ne a wadannan wasanni saboda ya lura ina dingishi a wani rauni da na samu.  Ka san ni da naci, ko ina tare da rauni nakan daure wajen yin kwallo don in taimaki kulob dina da kuma kasata Fotugal.  Babu dan kwallon da yake son a canja shi a yayin kwallo amma saboda na harzuka ne ya sa na dauki matakin fita daga filin wasan sai dai yanzu na gane manufar kocin da ya canja ni.”

Fotugal ta lallasa Ludemburg da ci 2-0 kuma Ronaldo ne ya zura daya daga cikin kwallayen a ranar Lahadin da ta wuce wanda hakan ya sa Fotugal ta haye gasar Euro 2020. Fotugal ce take rike da wannan kofi