✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dalilin da ya sa aka daina jin duriyata – Adamu Nagudu

Adamu Hassan Nagudu fitaccen mawaki ne a masana’antar fina-finan Hausa. A shekarun bayan nan an daina jin duriyarsa, inda har wadansu suka fara tambayar ko…

Adamu Hassan Nagudu fitaccen mawaki ne a masana’antar fina-finan Hausa. A shekarun bayan nan an daina jin duriyarsa, inda har wadansu suka fara tambayar ko ya daina harkar waka ce. A tattaunawarsa da Aminiya , mawakin ya bayyana dalilin da ya sa aka daina jin duriyarsa a harkar waka da dalilin da ya sa ya dawo harkar gadan-gadan yanzu da kuma shirinsa na ci gaba da fitowa a manyan fina-finai:

 

A ’yan shekarun da suka wuce an daina jin duriyarka, har wadansu sun fara tunanin ko ka daina harkar waka ce, yaya batun yake?

Nagudu: To, alhamdulillahi ka san ita harkar industiri da ma komai na duniya idan ka dauke shi a bisa sana’a, to, yana gaba ya kuma yi baya ne. Ko da kasuwanci ne samu yakan bambanta, za ka samu riba a wani lokaci, yayin da wani lokaci kuma faduwa ake kirgawa.

A harka ta industiri za ka ga yau wane a sama, ko wancan ne a sama, gobe kuma sai ka ga wance ko wane ne a kasa, haka abin yake juyawa. A da mawakan ma ba mu da yawa, amma yanzu ba zan ma iya kirga mawakan ba, mawaka a yanzu sun hada da yara da manya da ma sababbi.

Dalili na farko da ya sa aka daina jin duriyata shi ne, idan ka dubi yadda nake yin wakokina ba na sakin kundin wakoki na bidiyo ne ko na saurare a-kai-a-kai. Idan na yi albam nakan dauki shekara daya ko biyu kafin na sake sakin wani. A bana na kai shekara uku ko hudu ban saki wani kundin wakoki nawa ba, wannan dalili ne ya sa mutane suke tunanin na daina waka.

Dalili na biyu shi ne, yanayin kasuwa ta duniya ma komai a yanzu ya fadi, a shekarun bayan nan komai ya zama sai Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un. Kasuwancin ya taba ko’ina mu kanmu a yanzu ba za ka iya zuba kudinka, ka bata lokacinka ka yi waka ba, sannan ka kashe miliyoyin kudi wajen yin bidiyo ka sake a kasuwa amma ka fadi ba. Misali idan ka fitar da kwafi dubu 50, to kafin ka sayar da kwafi dubu biyar, to masu satar fasaha sun sayar da kwafi dubu 500, shi ya sa mutane suka ga a yanzu ba mu sake albam ba, yaya za mu sake bayan muna tsoron asara.

A yanzu zamani ya sauya inda yawancin mawaka suka koma kafar sadarwar intanet ta Youtube wajen sanya wakokinsu ko fina-finansu don a je a kalla, ko kai ma ka fara yunkurin haka?

A yanzu komai ya koma hanyar kafar sadarwar zamani, a yanzu maganar da nake da kai na saki wata sabuwar wakata wadda tun shekara uku zuwa hudu ban sake yin waka ba, sai wannan albam dina na yanzu, inda daya-bayan-daya zan rika sake su a Youtube mai suna Adamu Nagudu.

Ga wadanda ba sa shiga Youtube yaya za su yi su kalli wakokinka na yanzu ke nan?

Eh, sannu a hankali zan buga a faifan DBD don ya kai ga lungu da sako na kasar nan da wajenta.

Mene ne sunan albam din naka, sannan yana kunshe da wakoki kamar nawa?

Sunan albam din ‘Tauraro’, na kallo ne da na saurare, amma dai a Janairun sabuwar shekara zan fitar da shi a faifan DBD, wannan albam din zai fito da wakoki kamar shida.

Wane jigo wannan albam din naka ya kunsa?

A yadda na dade ban fitar da albam din wakoki ba, to wannan kundin wakokin na shirya shi ne bayan na yi nazari a kan halayyar dan Adam da zamantakewa da kasuwanci da yadda kasar nan take ciki da ma yadda rayuwa take tafiya.

Haka akwai wata waka da na yi inda na yi magana a kan ita kanta daukaka, a lokacin da Ubangiji (SWT) zai ba ka ita da kuma lokacin da zai karba. Albam ne da ya shafi kowa da kowa, akwai wa’azantarwa a ciki.

Sannan albam din yana dauke da wakokin nishadantarwa, ka san fannina fannin soyayya ne, kowa ya san Adamu Hassan Nagudu gwanin wakokin soyayya ne, to wannan albam din ma yana dauke da wakokin soyayya.

Yawanci za ka ga mutane sun hada taura biyu a bakinsu, misali duk da harkar fim ko waka, za ka ga mutum yana taba wata sana’a ko kasuwanci, ko kai ma bayan harkar waka, kana wani kasuwanci?

Da ma na dade ina kasuwanci, kuma ba wai harkar fim da waka kawai nake yi ba, ina da wasu hanyoyi da nake buga-buga dina a gefe. A yanzu zan ce shi ne rufin asirin ma, ba wai kawai sana’a daya mutum ya kamata ya rika yi ba.

Kamar wacce sana’a kake yi ke nan?

Na farko idan ka dauke ni, to ni tela ne, a gaskiya dinki sana’a ce da ba zan yasar da ita ba, na ingantata a yanzu, na juya sana’ar ta koma ta zamani, yadda ni ma zan amfana. Haka wadanda suke karkashina su ma su amfana. Na biyu kuma ina harkar kasuwanci, inda nake sayar da atamfa da takalma, sannan na kware wajen hada lefen aure.

A kwanakin baya ka fara fitowa a fina-finai, yanzu kuma an ji shiru, yaya batun yake?

Har yanzu ni jarumi ne, kuma mawaki ne, shi fim ba a yi masa gaggawa, kuma komai yana da iyaka da kuma lokaci, duk abin da ka yi hakuri, inshaAllahu wata rana kana zaune ma abin zai zo maka. Harkar fim gida-gida ne, kowane jarumi ko jaruma da gidan da kowa yake, ba wai abu ne kawai da ake yin ta gaba daya ba. To, yanzu akwai abubuwan da nake shiri, kuma a yanzu ba kowane fim nake fitowa a ciki ba, idan ka kawo mini labarin fim sai na karanta, idan na ga ba zai amfanar da ni ba, to zan ba ka hakuri in ce ka nemi wani ya yi maka.

To, yawancin furodusoshi ba sa son irin haka, abin da suke so kawai idan an ba ka labarin fim, to sai ka karba kana rawar jiki, to ni ba haka nake ba, zan yi fim din da zai taimake ni ne. Amma duk da haka nan da wani lokaci za a rika ganina sosai a cikin fina-finai, mun tsaya mun kammala shiri, labaranmu na kasa, kudinmu na kasa, za mu kuma fara aiwatar da fina-finanmu a-kai-a-kai.

Masu karatu ma za su so su ji me ya ja hankalinka har ka fara fitowa a fina-finai, maimakon ka tsaya a bangaren waka da aka fi saninka da ita?

Idan ka koma baya wato kowa ya san ni tun daga lokacin da nake garin Jos kafin in dawo Kano, to gaskiya a jarumi ya san ni, ba mawaki ba. Na fara wasan dabe tun wasu shekaru da suka wuce, ina wasan dandali. Da na zo Kano na zama babban mawaki, saboda Allah Ya kaddara cewa waka ita ce abincina ba fitowa a fina-finai ba, amma tun can ina waka kuma ina fitowa a fim, na fi ba da karfi a kan waka ne tun da a nan Allah Ya kaddara zan samu abinci sosai.