✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dalilin da ya sa ba na kallon kwallo a gida -Lionel Messi

Shahararren dan kwallon duniya da yanzu haka yake wasa a kulob din FC Barcelona da ke Sifen kuma dan asalin Ajantina Lionel Messi a shekaranjiya…

Shahararren dan kwallon duniya da yanzu haka yake wasa a kulob din FC Barcelona da ke Sifen kuma dan asalin Ajantina Lionel Messi a shekaranjiya Laraba ya bayyana wa duniya cewa matarsa Antonella ce take hana shi kallon kwallo a akwatin talabijin a gida saboda ba ta da sha’awar wasan kwallon kafa a rayuwarta.
Hasalima, Messi ya ce a lokuta da dama idan yana son kallon kwallo a gida matarsa kan umarce shi da ko dai ya rage sautin akwatin talabijin din ko kuma ya kashe  saboda yakan hana ta yin wasu al’amurra.
A lokacin da dan kwallon ke hira da jaridar Corrierre della Sera ta Sifen, ya ce “na sha komawa gida in tarar da mai dakina bayan na yi wasan kwallo na shaida mata yau na zura kwallaye biyu ko uku a raga don ta taya ni murna amma abin mamaki sai ta yi biris kamar ba ta ji abin da na fada ba”.
“Harkar wasan kwallon kafa ita ce hanyar neman abinci na amma abin mamaki mai dakina ba ta da sha’awar wasan kwallo”, inji shi.
Lionel Messi ne gwarzon dan kwallon duniya da ya taba lashe kyautar sau hudu a jere.  Ya taimaki kulob din FC Barcelona wajen lashe gasar rukuni-rukuni na Sifen karo na 22 bayan ya zura kwallaye 46 a yayin gasar a bara.  Kuma ya zura kwallaye 60 a duk wasannin da ya yi.
Kawo yanzu, Messi ne ya kafa tarihin dan kwallon da ya fi yin fice a harkar tamola da babu wanda ya kama kafarsa.