✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dalilin da ya sa ban yi bikin al’ada na ‘yan sanda a aurena  ba – Salihu Getso

Salihu Getso matashin dan sanda ne da a kwanakin baya ya angwance. Ya yi wani abu da ba kasafai aka saba gani a tsakanin matasa…

Salihu Getso matashin dan sanda ne da a kwanakin baya ya angwance. Ya yi wani abu da ba kasafai aka saba gani a tsakanin matasa masu aikin damara ba. A zantawar da Aminiya ta yi da shi, ya shaida cewa dalilin da ya sanya ya ki yin bukukuwan al’ada na ‘yan sanda, inda ya ce tubarraki ake nema lokacin aure ba a barnar kudi ba.

Aminiya: A kwanakin baya ka angwance sai dai ba kamar yadda aka saba ba, ba ka yi irin bikin nan da ‘yan sanda kan yi ba, ko meye dalili?

Salihu Getso: E, alal hakika ban yi irin bikin nan da jami’an ’yan sanda kan yi ba wanda ake shirya liyafa ta musamman cikin kayan sarki ban kuma yi ko wane irin bikin ba bayan aure da walimar aure nayi haka ne domin in tattala kudin da zan barnata a wadanccan ababe da basu da mahimmanci sai na dauki nauyin iyayena da Amaryata muka tafi kasa mai tsarki muka yi umara, kaga ni abin da naga yafi amfani ke nan a maimakon wadanccan domin shi aure albarka ake nema kuma ni a ganina ta yin hakan zan nemi albarkar na samu a maimakon yin almubazzaranci ko kashe kudi inda bai dace ba.

Aminiya: Ko akwai wani kalubale da ka fuskanta biyo bayan wannan mataki?

Salihu Getso: Tabbas na fuskanci kalubale da dama sakamakon matakin da na dauka abin da ba kasafai aka fiye gani ba, na yi gwagwarmaya da kawayen Amaryata sosai da kuma wasu daga cikin  ‘yan uwanta, akwai wani cikin abokan aikina har ya kama hayar dakin taro a Kabir Gymnasium a Kaduna bada sani na ba, daga wajen da amarya tayi walima suka zo da motoci suka dauki ‘yan matan Amarya da niyyar zasu wuce dasu kai tsaye an shirya za a yi bukukuwa ni  kuma nazo da mota na dauke Amarya na kaita gidan iyayenta, kaga babu yadda za ayi shagali ba Amarya ba Ango, Ina so na nuna ma duniya cewa yin almubazzaranci da lalata dukiya a wajen aure ba shine abin da addini ya koyar ba, albarka da dace wa ya kamata a nema ba ashara ranci ba, na shirya walima ta bayan daurin aure ‘yan uwa da abokan arziki sun halarta ina mika godiyata a gare su bayan wannan ne na dauki Amaryata da iyayena muka je muka yi umara domin neman tubaraki a wajen Allah, nayi haka ne domin neman albarka da yardar Allah tare da yiwa ‘yan uwa wa’azi a aikace ba a baki kawai ba.