✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dalilin da ya sa muka shiga yajin aiki – Shugaban kwadago

A jiya Alhamis kungiyoyin kwadagon suka fara yajin aiki na illa masha Allahu a fadin kasar nan, bayan tashi baram-baram daga tattaunawar da suka kai…

A jiya Alhamis kungiyoyin kwadagon suka fara yajin aiki na illa masha Allahu a fadin kasar nan, bayan tashi baram-baram daga tattaunawar da suka kai dare suna yi da Ministan kwadago, Chris Ngige a kan batun sabon albashi mafi karanci ga ma’aikatan Najeriya.

kungiyoyin da suka hada da NLC da ULC da TUC ne suka dauki matakin saboda abin da suka kira gazawar gwamnati wajen sauraron koke-kokensu.

Yunkurin da Gwamnatin Tarayyar ta yi don kauce wa yajin aikin ta wajen ganawa da shugabannin kungiyar ya ci tura saboda rashin amincewa da bayanan da Ministan kwadagon ya yi musu.

A  ganawar da Ministan kwadago, Chris Ngige ya yi da kungiyar kwadagon, ya yi alkawarin cewa kwamitin da aka dora wa alhakin warware takaddamar, zai sake zama a ranar 4 ga Oktoba, domin fayyace matakin karshe da ake ciki, dangane da cimma matsaya kan batun karin albashi daga Naira dubu 18 zuwa dubu 56 mafi karanci.

Alkawarin Ministan ya gaza yin tasiri wajen dakatar da yajin aikin, domin kungiyar ta ce ba za ta janye hukuncin da ta yanke ba, bayan karewar wa’adin mako biyu da ta bai wa Gwamnatin Tarayya.

Da yake ganawa da manema labarai jim kadan bayan tattaunawarsu da gwamnatin, Shugaban kungiyar kwadago ta kasa (NLC), Kwamared Ayuba Wabba, ya ce yajin aikin zai shafi ma’aikatan gwamnati da na kamfanoni, abin da zai sanya a rufe makarantu da bankuna da ma’aikatu da gidajen mai.

Sakataren Tsare-Tsare na Hadaddiyar kungiyar kwadago ta ULC, Kwamared Nasir Kabiru ya bayyana wa manema labarai dalilan da ya sa suka kasa cimma matsaya a tsakaninsu da gwamnati.

“Ba mu cimma daidaito ba, saboda mun dauki kiran da Ministan kwadago ya yi mana a matsayin yaudara ce kawai. Kuma wannan yaji da muka tsunduma cikinsa, za mu ci gaba a shi ne daga karfe 12 na daren Laraba har sai illa masha Allah.”

Ya ce da alama gwamnatin kasar nan ba ta damu da halin da talakan Najeriya ke ciki ba. “Wa’adin da muka ba gwamnati na kwana 14 na a tattauna batun ya zo har ya wuce, amma me ya sa bai tashi nemanmu ba sai ana gobe za a fara yajin aikin?” Ya tambaya.