Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Dalilin da ya sa Super Eagles ta samu nasara a 1994 – Oliseh

Sunday Oliseh

Tsohon Kyaftin din kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles kuma tsohon kocin kungiyar Sunday Oliseh ya bayyana dalilan da suka sanya ’yan wasan Super Eagles ta samu nasara a 1994.

Sunday Oliseh wanda yake jawabi a bikin karrama su da Hukumar Kwallon Kafa ta Najeriya (NFF) ta yi a karshen makon jiya a bikin karrama ’yan kwallo na shekara-shekara da aka yi a Abuja, ya yi jawabi ne a madadin sauran ’yan kwallon kungiyar.

ADVERTISEMENT

Oliseh ya ce kimanin shekara 25 ke nan da Super Eagles ta lashe Kofin Afirka da aka yi a Tunisiya, sannan bayan shekara biyu da faruwar hakan sai ’yan wasan suka samu nasarar lashe Lambar Zinare a gasar Olamfik da aka yi a Atlanta a 1996 wanda hakan ya girgiza duniya.

Ya ce babban abin da ya sa suka samu wannan nasara shi ne, daukacin ’yan wasan suna wasa ne kansu a hade, duk abin da ya shafi daya, tamkar ya shafi sauran ne.  Sannan sun yi wasa ne don kishin kasa, ba don kudi ba.

ADVERTISEMENT

Ya ce ya tuna yadda matar marigayi Stephen Keshi take dafa musu abinci daga gidansu na Amurka ta kai musu otel din da aka sauke su, inda suke haduwa su ci ba tare da nuna bambanci ba.  Ya ce hakan ya karfafa musu gwiwa wajen tunkarar kowane irin wasa da zuciya daya.

’Yan wasan Super Eagles a wancan lokaci sun hada da Jay-Jay Okocha da Kanu Nwankwo da Stephen Keshi da Uche Ikechukwu da Daniel Amokachi da Sunday Oliseh da Bictor Ikpeba da Mutiu Adepeju da Tijjani Babangida da sauransu.

NFF ta ce har yanzu ba a samu ayarin Super Eagles da ya samu nasara kamar yadda na 1994 suka samu ba, wanda hakan ya sa aka karrama su.